Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • lr babi na 48 pp. 250-256
  • Sabuwar Duniya Mai Salama Ta Allah—Za Ka Iya Zama Ciki

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Sabuwar Duniya Mai Salama Ta Allah—Za Ka Iya Zama Ciki
  • Ka Koya Daga Wurin Babban Malami
  • Makamantan Littattafai
  • Rayuwa Cikin Sabuwar Duniya ta Salama
    Rayuwa Cikin Sabuwar Duniya ta Salama
  • Aljannar da Ta Kusan Zuwa!
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Wa’azi)—2021
  • Minene Nufin Allah ga Duniya?
    Menene Allah Yake Bukata a Garemu?
  • Me Ya Sa Allah Ya Halicci Mutane?
    Me Za Mu Koya Daga Littafi Mai Tsarki?
Dubi Ƙari
Ka Koya Daga Wurin Babban Malami
lr babi na 48 pp. 250-256

BABI NA 48

Sabuwar Duniya Mai Salama Ta Allah​—Za Ka Iya Zama Ciki

ALLAH ya saka Adamu da Hauwa’u a cikin lambun Adnin. Ko da yake sun yi rashin biyayya kuma sun mutu, Allah ya sa ya yiwu ’ya’yansu, haɗe da mu a yau mu zauna har abada cikin Aljanna. Littafi Mai Tsarki ya yi alkawari: “Masu-adalci za su gāji ƙasan, su zauna a cikinta har abada.”—Zabura 37:29.

Littafi Mai Tsarki ya yi magana game da “sababbin sammai” da “sabuwar duniya.” (Ishaya 65:17; 2 Bitrus 3:13) Wannan “sama” ta yanzu ta ƙunshi gwamnatocin mutane, amma Yesu Kristi da kuma waɗanda za su yi sarauta tare da shi a sama, su za su zama “sababbin sammai.” Kai, zai kasance da ban sha’awa sa’ad da waɗannan sababbin sammai, da gwamnati ce mai adalci ta salama, ta mallaki dukan duniya!

To, mecece ‘sabuwar duniyar’?— “Sabuwar duniya” mutane ne masu kirki da suke ƙaunar Jehovah. Ya kamata ka fahimci cewa, sa’ad da Littafi Mai Tsarki ya yi maganar “duniya” yana nufin mutane ne da suke rayuwa a duniya, ba ƙasar ba ce. (Farawa 11:1; Zabura 66:4; 96:1) Saboda haka, mutane da za su zama sabuwar duniya za su rayu a nan duniya.

Wannan duniya ta miyagun mutane a lokacin za ta shuɗe. Ka tuna, Ambaliyar zamanin Nuhu ta halaka duniyar miyagun mutane ne. Kuma kamar yadda muka koya, wannan duniya ta miyagu za ta halaka a Armageddon. Bari yanzu mu ga yadda rayuwa za ta zama a sabuwar duniya ta Allah bayan Armageddon.

Kana so ka rayu har abada a cikin Aljanna a sabuwar duniya mai salama ta Allah?— Babu likitan da zai iya sa mu rayu har abada. Babu magani da zai iya yin maganin mutuwa. Hanyar da kawai za mu iya rayuwa har abada ita ce ta wajen kusantar Allah. Kuma Babban Malami ya gaya mana yadda za mu yi haka.

Bari mu buɗe Littafi Mai Tsarki zuwa Yohanna sura 17, aya ta 3. A nan mun sami waɗannan kalmomi na Babban Malami: “Rai na har abada ke nan, su san ka, Allah makaɗaici mai-gaskiya, da shi kuma wanda ka aiko, Yesu Kristi.”

To, menene Yesu ya ce muke bukatar mu yi domin mu rayu har abada?— Da farko, dole ne mu koyi game da Ubanmu na samaniya, Jehovah, da kuma Ɗansa, wanda ya ba da ransa dominmu. Wannan yana nufin cewa muna bukatar mu yi nazarin Littafi Mai Tsarki. Wannan littafin na Ka Koya Daga Wurin Babban Malami, yana taimakonmu mu yi haka.

Amma ta yaya koyo game da Jehovah zai taimake mu mu rayu har abada?— Kamar yadda muke bukatar abinci kowacce rana, muna bukatar mu koyi game da Jehovah kowacce rana. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ba da abinci kaɗai ba mutum za ya rayu, amma da kowacce magana da ke fitowa daga bakin Allah.”—Matta 4:4.

Muna kuma bukatar mu koyi game da Yesu Kristi domin Allah ya aiko Ɗansa ya kawar da zunubinmu. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Babu ceto ga waninsa.” Kuma Littafi Mai Tsarki ya ƙara cewa: “Wanda yana bada gaskiya ga Ɗan yana da rai na har abada.” (Ayukan Manzanni 4:12; Yohanna 3:36) To, me yake nufi a ‘ba da gaskiya’ ga Yesu?— Yana nufi ne mu yarda da Yesu ƙwarai kuma mu sani cewa ba za mu rayu har abada ba ba tare da shi ba. Mun gaskata da haka?— Idan mun gaskata da haka, za mu ci gaba da koyo game da Babban Malami kowacce rana, kuma za mu yi abin da ya ce.

Hanya ɗaya mai kyau da za mu koya daga Babban Malami ita ce ta karanta wannan littafi a kai a kai mu kalli dukan hotunan kuma mu yi tunani a kansu. Ka yi ƙoƙari ka amsa tambayar da suke kan waɗannan hotunan. Ka kuma karanta wannan littafin da mamarka da babanka. Idan iyayenka ba sa tare da kai, ka karanta shi da wasu manyan mutane da kuma wasu yara. Ba abin farin ciki ba ne idan ka taimaki wasu suka koyi daga Babban Malami abin da ya kamata su yi domin su rayu har abada a sabuwar duniya ta Allah?—

Littafi Mai Tsarki ya gaya mana: “Duniya ma tana wucewa.” Amma kuma Littafi Mai Tsarki ya yi bayani game da abin da za mu yi mu rayu har abada a sabuwar duniya ta Allah. Ya ce: “Wanda ya aika nufin Allah ya zauna har abada.” (1 Yohanna 2:17) To, ta yaya za mu zauna a cikin sabuwar duniya ta Allah har abada?— Za mu iya yin haka, ta wajen koyo game da Jehovah da kuma Ɗansa wanda yake ƙauna, Yesu. Amma kuma muna bukatar mu yi abin da muka koya. Muna fata nazarinka na wannan littafin zai taimake ka ka yi waɗannan abubuwa.

Yara da manya suna wasa da dabbobi a aljanna

Sa’ad da kake karanta Ishaya 11:6-9 da kuma Ishaya 65:25, kana koyo game da dabbobi da suke zaune cikin salama. Ka duba wannan hoton. Ka lura da ɗan rago, ɗan akuya, damisa, ɗan maraƙi, babban zaki, da kuma yara da suke tare. Za ka iya faɗin sunayen wasu dabbobin da Littafi Mai Tsarki ya yi magana game da su?— Ga yaron nan yana wasa da kumurci! Babu wanda yake zaune a sabuwar duniya da zai bukaci ya ji tsoro. (Hosea 2:18) Me ka ce game da wannan?—

Mutane daga kabilu dabam-dabam suna zaman lafiya tare a sabuwar duniya

Ka lura da salama da take tsakanin dukan iren-iren mutane. Duka suna ƙaunar juna, kamar yadda Yesu ya ce mabiyansa za su yi. (Yohanna 13:34, 35) Makaman yaƙi za a mai da su kayayyakin noma. Littafi Mai Tsarki ya faɗi game da salama mai ban sha’awa da mutane za su more a sabuwar duniya. Za mu iya karanta wannan a nassosi kamar su Zabura 72:7; Ishaya 2:4; 32:16-18; da kuma Ezekiel 34:25.

Mutane a aljanna suna gini, suna datsa itatuwa, kuma suna more ’ya’yan itatuwan

Dubi mutane da suke wannan shafi. Suna kula da duniya, suna mai da ta kyakkyawa. Ka ga wannan gida mai kyau da kuma dukan gidaje da dukan ’ya’yan itatuwa da ganyaye masu kyau. Mutane suna zaman lafiya da duniya, to, ya zama aljanna kamar lambun Adnin. Za mu iya karanta game da waɗannan abubuwa masu ban sha’awa a Zabura 67:6; 72:16; Ishaya 25:6; 65:21-24; da kuma Ezekiel 36:35.

Mutane suna da koshin lafiya kuma suna farin ciki a aljanna

Kamar yadda kake gani a nan, kowa yana da lafiya kuma yana farin ciki. Mutane za su iya tsalle kamar barewa. Babu gurgu, makaho, ko marar lafiya. Kuma duba waɗancan mutanen da aka ta da su daga matattu! Littafi Mai Tsarki ya yi magana game da waɗannan abubuwa a Ishaya 25:8; 33:24; 35:5, 6; Ayukan Manzanni 24:15; da kuma Ru’ya ta Yohanna 21:3, 4.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba