Za Ka So Ƙarin Bayani?
Wannan mujallar tana ɗauke ne da taƙaitaccen bayani mai ban al’ajabi game da saƙon da ke cikin Littafi Mai Tsarki. Amma wannan taƙaitawar ba wai za ta bayyana dalla-dalla dukan abubuwan da Littafi Mai Tsarki ya koyar a kan kowane batu ba.
Alal misali, a ce kana ɗokin sanin amsoshin da Littafi Mai Tsarki ya ba da game da irin waɗannan tambayoyin: Allah yana kula da kowannenmu kuwa da gaske? Me ke faruwa da mu sa’ad da muka mutu? Ta yaya zan samu farin ciki a rayuwa?
Za a iya samun amsoshin waɗannan da kuma wasu tambayoyin a cikin littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa? Shaidun Jehobah ne suka wallafa. An tsara wannan littafin ne don tattauna batu guda daga cikin Littafi Mai Tsarki a lokaci guda. Irin wannan nazarin yana taimaka wa mutum ya ga ayoyi dabam-dabam daga cikin Littafi Mai Tsarki da suka tattauna batu guda. Kana iya samun kofi guda na littafin nan ta wajen cika takardar da ke ƙasa kuma ka aika ta zuwa adireshin da ya dace a cikin waɗanda aka jera a ƙasa.
□ Ina bukatan kofi guda na littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa? Ka ambata yaren.
□ Don Allah ka tuntuɓe ni game da nazarin Littafi Mai Tsarki da ake yi kyauta.