Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • hf sashe na 5 pp. 15-17
  • Yadda Za Ku Zauna Lafiya da Danginku

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Yadda Za Ku Zauna Lafiya da Danginku
  • Yadda Iyalinku Za Ta Zauna Lafiya
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • 1 KU KASANCE DA RA’AYIN DA YA DACE GAME DA SURUKANKU
  • 2 KU TASHI TSAYE IDAN DA BUKATA
  • Kada Ku Ci Amanar Juna
    Yadda Iyalinku Za Ta Zauna Lafiya
  • Ku Nemi Taimakon Allah don Ku Ji Daɗin Aurenku
    Yadda Iyalinku Za Ta Zauna Lafiya
  • Yadda Za Ka Daraja Matarka
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
  • Zaman Aure
    Ku Ci Gaba da Kaunar Allah
Dubi Ƙari
Yadda Iyalinku Za Ta Zauna Lafiya
hf sashe na 5 pp. 15-17
Wata surukuwa ba ta so yadda matar danta ke dahuwa ba

SASHE NA 5

Yadda Za Ku Zauna Lafiya da Danginku

“Ku ɗau halin . . . kirki, da tawali’u, da salihanci, da haƙuri.”​—Kolosiyawa 3:12, Littafi Mai Tsarki

Aure yana haifar da sabon iyali. Ko da yake kana bukatar ka ci gaba da yi wa iyayenka ladabi kuma ka ƙaunace su, amma bayan ka yi aure, matarka ta fi kowa a nan duniyar muhimmanci a gare ka. Wasu iyayen ba za su fahimci hakan ba. Duk da haka, ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki za su iya taimaka maka ka san yadda za ka zauna lafiya da iyayenka da kuma surukanka yayin da kake ƙoƙarin ƙarfafa sabon iyalinka. Za a iya yin amfani da dukan ƙa’idodin da aka ambata a wannan talifin sa’ad da ake sha’ani da ’yan’uwa, surukai, kawunai, gwaggo, kakanni da sauran dangi.

1 KU KASANCE DA RA’AYIN DA YA DACE GAME DA SURUKANKU

Auraru suna liyafa tare da iyayensu

ABIN DA LITTAFI MAI TSARKI YA CE: “Ka girmama ubanka da uwarka.” (Afisawa 6:2) Kome yawan shekarunka, wajibi ne ka riƙa girmama iyayenka. Ka tuna cewa matarka ma tana da iyaye kuma tana bukatar ta kula da su. Kada dangantakar da ke tsakanin matarka da iyayenta ta sa ka yin kishi, domin “ƙauna ba ta jin kishi.”​—1 Korintiyawa 13:4; Galatiyawa 5:26.

SHAWARA:

  • Ka guji yin furuci kamar su “Iyalinki sun cika raina ni” ko kuma “Babu abin da na taɓa yi da ya gamshi mahaifiyarki”

  • Ka yi ƙoƙari ka fahimci matarka

2 KU TASHI TSAYE IDAN DA BUKATA

ABIN DA LITTAFI MAI TSARKI YA CE: ‘Mutum za ya rabu da ubansa da uwarsa, ya manne wa matarsa: za su zama nama ɗaya kuma.’ (Farawa 2:24) Bayan ka yi aure, iyayenka suna iya yin tunanin cewa har yanzu kana ƙarƙashinsu, kuma hakan zai sa su so su riƙa yawan sa baki a aurenku.

Kai da matarka ne za ku kafa musu iyaka domin kada su wuce gona da iri, sa’an nan ku bayyana musu hakan da ladabi. Za ku iya gaya musu abin da ke zuciyarku ba tare da raini ba. (Misalai 15:1) Idan kuna da haƙuri da kuma sauƙin kai, za ku ji daɗin dangantakarku da surukanku kuma za ku ci gaba da yin “haƙuri da junanku cikin ƙauna.”​—Afisawa 4:2.

Mata da miji suna tattaunawa; mata da miji suna ba wa iyayensu wata kyauta

SHAWARA:

  • Idan kun damu sosai da yadda surukanku suke yawan sa baki a sha’aninku, ku tattauna hakan da matarku bayan kome ya lafa

  • Ku bari bakinku ya zo ɗaya a kan yadda za ku riƙa bi da irin wannan batu

KU YI ƘOƘARI KU FAHIMCE SU

Yana da muhimmanci ku fahimci ra’ayin iyayenku. Sun damu ne da ku sosai, ba wai suna da wani mugun nufi ba. Zai yi wa iyayenku wuya su ɗauke ku a matsayin wani iyali dabam. Suna ma iya ji kamar kun yi watsi da su. Amma idan kuna bin ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki kuma kuna tattaunawa da juna da kuma iyayenku, za ku ci gaba da girmama iyayenku kuma aurenku ba zai dagule ba.

KA TAMBAYI KANKA . . .

  • Me ya sa ba laifi ba ne idan iyayena ko na matata suka damu da sha’aninmu?

  • Ta yaya zan ba matata ko mijina fifiko ba tare da na raina iyayena ba?

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba