Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • lfb darasi na 2 p. 10-p. 11 par. 1
  • Allah Ya Yi Mace da Miji na Farko

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Allah Ya Yi Mace da Miji na Farko
  • Darussa daga Littafi Mai Tsarki
  • Makamantan Littattafai
  • Namiji Da Ta Mace Na Farko
    Littafina na Labarun Littafi Mai Tsarki
  • Me Ya Sa Mutane Suke Tsufa da Mutuwa?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Wa’azi)—2019
  • An Kawar da Mutuwa, Maƙiya ta Ƙarshe
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2014
  • Mutuwar Yesu da Kuma Tashinsa Daga Mutuwa​—⁠Yadda Za Su Iya Amfanar Ka
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2015
Dubi Ƙari
Darussa daga Littafi Mai Tsarki
lfb darasi na 2 p. 10-p. 11 par. 1
Adamu da Hauwa’u a lambun Adnin

DARASI NA 2

Allah Ya Yi Mata da Miji na Farko

Jehobah ya yi lambu a wani wuri da ake kira Adnin. Akwai fulawoyi da itatuwa da kuma dabbobi dabam-dabam a lambun. Bayan haka, sai Allah ya halicci mutum na farko mai suna Adamu da ƙasa. Sai ya hura iska a hancinsa. Ka san abin da ya faru bayan haka? Mutumin ya soma numfashi! Sai Jehobah ya gaya wa Adamu cewa ya kula da lambun kuma ya ba dukan dabbobin da ke wurin suna.

Allah ya ba Adamu wata doka. Ya ce: ‘Za ka iya ci daga dukan itatuwan da ke lambun amma ban da guda ɗaya. A ranar da ka ci ’ya’yan itacen nan, za ka mutu.’

Bayan haka, sai Jehobah ya ce: ‘Zan yi ma Adamu macen da za ta riƙa taimaka masa.’ Allah ya sa Adamu ya yi barci sosai, sai ya cire ƙashin da ke ƙirjinsa ya yi macen da shi. Sunanta Hauwa’u. Adamu da Hauwa’u su ne iyali na farko a duniya. Yaya Adamu ya ji sa’ad da Allah ya ba shi mata? Ya yi farin ciki sosai kuma ya ce: ‘Duba abin da Jehobah ya yi da ƙashin ƙirjina! Abin mamaki! An yi wata kamar ni.’

Sai Jehobah ya gaya wa Adamu da Hauwa’u cewa su haifi yara kuma su cika duniya. Yana so su yi aiki tare don su mai da duniya Aljanna, wato wuri mai kyau kamar lambun Adnin kuma yana so su ji daɗin aikin da ya ba su. Amma hakan bai faru ba. Me ya sa? Za mu san dalilin a babi na gaba.

‘Shi wanda ya yi su tun farko, namiji da mace ya yi su.ʼ​—Matta 19:4

Tambayoyi: Wane aiki ne Jehobah ya ba Adamu? Me zai faru da Adamu da Hauwa’u idan suka ci ’ya’yan itacen da Allah ya ce kada su ci?

Farawa 1:​27-31; 2:​7-9, 15-23; Zabura 115:16; Matta 19:​4-6

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba