Gabatarwar Sashe na 3
Bayan Ambaliyar ruwan, Littafi Mai Tsarki ya faɗi sunayen wasu mutane da suke bauta wa Jehobah. Ɗaya daga cikinsu Ibrahim ne kuma ana kiransa abokin Jehobah. Amma me ya sa ake ce da shi abokin Jehobah? Idan kana da yara, ka taimaka musu su fahimci cewa Jehobah yana son su sosai kuma yana so ya taimaka musu. Za mu iya roƙan Jehobah ya taimaka mana kamar yadda Ibrahim da wasu amintattun maza kamar Lutu da kuma Yakubu suka yi. Za mu iya kasancewa da tabbaci cewa Jehobah zai cika dukan alkawuransa.