Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • lff darasi na 20
  • Yadda Aka Tsara Ikilisiya

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Yadda Aka Tsara Ikilisiya
  • Ka Ji Dadin Rayuwa Har Abada!​—Don Nazarin Littafi Mai Tsarki
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • KA YI BINCIKE SOSAI
  • TAƘAITAWA
  • KA BINCIKA
  • Yaya Dattawa Suke Hidima a Ikilisiya?
    Su Wane Ne Suke yin Nufin Jehobah A Yau?
  • “Ku Girmama Waɗanda Suke Aiki Tuƙuru A Cikinku”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
  • Ka ‘Kira Dattawa’
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2025
  • “Ku Yi Kiwon Garken Allah Wanda Ke Wurinku”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
Dubi Ƙari
Ka Ji Dadin Rayuwa Har Abada!​—Don Nazarin Littafi Mai Tsarki
lff darasi na 20
Darasi na 20. A taron Shaidun Jehobah, wani dan’uwa ya yi tambaya kuma mutane dabam-dabam sun daga hannu don su ba da amsa.

DARASI NA 20

Yadda Aka Tsara Ikilisiya

Hoto
Hoto
Hoto

Jehobah Allah ne mai tsara abubuwa da kyau. (1 Korintiyawa 14:​33, 40) Saboda haka, ya kamata masu bauta masa ma su riƙa tsara abubuwa da kyau. Yaya ake gudanar da ayyuka a ikilisiya? Me za mu yi don a riƙa yin kome yadda ya kamata?

1. Wane ne shugaban ikilisiya?

“Almasihu [ne] shugaban ikilisiya.” (Afisawa 5:​23, Littafi Mai Tsarki) Daga sama ne yake ja-gorancin ayyukan Shaidun Jehobah a faɗin duniya. Yesu ne ya naɗa “bawan nan mai aminci, mai hikima” wato, Hukumar da Ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah. (Karanta Matiyu 24:​45-47.) Kamar manzanni da kuma dattawan da ke ƙarni na farko a Urushalima, Hukumar da Ke Kula da Ayyukanmu ne suke ja-goranci a dukan ikilisiyoyi a duniya. (Ayyukan Manzanni 15:2) Amma su ba shugabanni ba ne a ƙungiyar Jehobah. Suna karanta Littafi Mai Tsarki don su fahimci abin da Jehobah yake so su yi, kuma suna bin umurnin Yesu.

2. Su waye ne dattawa kuma wane aiki ne suke yi?

Dattawa maza ne da suka ƙware kuma suna koya wa mutanen Jehobah Littafi Mai Tsarki da taimaka musu da kuma ƙarfafa su. Ba a biyan su kuɗi don aikin da suke yi. A maimakon haka, suna ‘yin shi da yardar ransu yadda Allah yake so,’ ba don suna neman ribar banza ba, amma don suna da niyyar yin hidima. (1 Bitrus 5:​1, 2) Bayi masu hidima maza ne da suke taimaka wa dattawa a ikilisiya. Da shigewar lokaci, su ma za su zama dattawa idan suka cancanci hakan.

Hukumar da Ke Kula da Ayyukanmu ne suke zaɓan wasu dattawa don su zama masu kula da da’ira. Suna ziyartar ikilisiyoyi dabam-dabam don su ja-goranci ’yan’uwa da kuma ƙarfafa su. Masu kula da da’ira suna bin ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki don su ga ko wani ɗan’uwa ya cancanci zama bawa mai hidima ko dattijo.​—1 Timoti 3:​1-10, 12; Titus 1:​5-9.

3. Mene ne aikin kowannenmu a ikilisiya?

Dukan ’yan’uwa a ikilisiya suna yabon “sunan Yahweh” ta yin kalami da jawabai, da rera waƙa da kuma yin wa’azi daidai gwargwadon ƙarfinsu.​—Karanta Zabura 148:​12, 13.

KA YI BINCIKE SOSAI

Za mu san ko wane irin shugaba ne Yesu, da yadda dattawa suke bin misalinsa, da kuma yadda za mu bi umurnin Yesu kuma mu goyi bayan dattawa.

4. Yesu shugaban kirki ne

Yesu ya ƙarfafa mu mu nemi taimakonsa. Ku karanta Matiyu 11:​28-30, sai ku tattauna tambayar nan:

  • Yaya Yesu yake so mu ji game da shugabancinsa?

Ta yaya dattawa suke yin koyi da misalin Yesu? Ku kalli BIDIYON nan.

BIDIYO: Dattawa Sun Taimaka da Aka Yi Girgizar Ƙasa a Nepal (4:56)

Littafi Mai Tsarki ya nuna yadda ya kamata dattawa su yi aikinsu.

Ku karanta Ishaya 32:2 da 1 Bitrus 5:​1-3, sai ku tattauna tambayoyin nan:

  • Yaya kake ji don yadda dattawa suke bin misalin Yesu wajen ƙarfafa mutane?

  • A waɗanne hanyoyi ne kuma dattawa suke bin misalin Yesu?

5. Dattawa suna koyar da mu ta wurin halayensu masu kyau

Yaya Yesu yake so dattawa su riƙa ɗaukan aikinsu? Ku kalli BIDIYON nan.

BIDIYO: Dattawa Ne Suke Yin Ja-goranci! (7:39)

Yesu ne ya kafa ƙa’idodin da masu ja-goranci a ikilisiya suke bi. Ku karanta Matiyu 23:​8-12, sai ku tattauna tambayoyin nan:

  • Waɗanne ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki ne dattawa suke bi? Kana ganin malaman addinai suna bin abin da Littafi Mai Tsarki ya ce kuwa?

A. Hotuna: Wani dattijo yana yin abubuwan da za su karfafa dangantakarsa da Jehobah da kuma na iyalinsa. 1. Yana addu’a kafin ya soma nazarin Littafi Mai Tsarki. 2. Shi da matarsa suna koya wa ’yarsu karama abin da ke Littafi Mai Tsarki. B. Dattijon da matarsa sun ziyarci wata ’yar’uwa a ikilisiyarsu da aka kwantar a asibiti. C. Dattijon ya je kofar gidan wani mutum yana masa wa’azi. D. Hotuna: 1. Dattijon yana ba da jawabi a ikilisiya. 2. Yana tsabtace wata Majami’ar Mulki.
  1. Dattawa suna ƙarfafa dangantakarsu da Jehobah kuma suna taimaka wa iyalansu su yi hakan

  2. Dattawa suna kula da ’yan’uwan da ke ikilisiyarsu

  3. Dattawa suna wa’azi kowane lokaci

  4. Dattawa suna koyar da ’yan’uwa a ikilisiya. Suna yin shara da kuma wasu ayyuka

6. Za mu iya bin ja-gorancin dattawa

A cikin Littafi Mai Tsarki an ambata dalili mai muhimmanci da zai sa mu bi abin da dattawa suka ce. Ku karanta Ibraniyawa 13:​17, sai ku tattauna tambayoyin nan:

  • Me ya sa Littafi Mai Tsarki ya ce mu riƙa biyayya ga ­waɗanda suke mana ja-goranci? Yaya kake ji game da hakan?

Ku karanta Luka 16:10, sai ku tattauna tambayar nan:

  • Me ya sa za mu yi abin da dattawa suka ce har a abubuwan da muke ganin ba su da muhimmanci sosai?

WASU SUN CE: “Za mu iya bauta wa Allah yadda muka ga dama.”

  • Me ya sa kake ganin ya dace mutum ya riƙa bauta wa Allah tare da ’yan’uwa a ikilisiya?

TAƘAITAWA

Yesu ne shugaban ikilisiya. Muna jin daɗin yin biyayya ga dattawa don Yesu ne shugabansu, suna ƙarfafa mu kuma za mu iya yin koyi da halayensu masu kyau.

Bita

  • Wane ne shugaban ikilisiya?

  • Ta yaya dattawa suke taimakawa a ikilisiya?

  • Mene ne aikin kowanne bawan Jehobah a ikilisiya?

Maƙasudi

KA BINCIKA

Ku kalli bidiyon nan don ku ga yadda Hukumar da Ke Kula da Ayyukanmu da dattawa suka damu da ’yan’uwa a yau.

An Ƙarfafa ’Yan’uwa Lokacin da Aka Hana Aikinmu (4:22)

Ku kalli bidiyon nan don ku ga irin hidimar da masu kula da da’ira suke yi.

Rayuwar Masu Kula da Da’ira da Suke Hidima a Karkara (4:51)

Ku karanta talifin nan don ku koyi game da hidimar da mata suke yi a ikilisiya.

“Shaidun Jehobah Suna Barin Mata Su Koyar da Mutane Ne?” (Hasumiyar Tsaro, 1 ga ­Oktoba, 2012)

Ku karanta talifin nan don ku ga yadda dattawa suke aiki tuƙuru don su ƙarfafa ­’yan’uwansu.

“Dattawa Kirista Suna Aiki Don Mu Yi ‘Farin Ciki’” (Hasumiyar Tsaro, 15 ga Janairu, 2013)

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba