Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w01 5/1 p. 31
  • “Jehovah Ya Yi Mini Alheri Ƙwarai!”

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • “Jehovah Ya Yi Mini Alheri Ƙwarai!”
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2001
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2001
w01 5/1 p. 31

“Jehovah Ya Yi Mini Alheri Ƙwarai!”

A WANI maraice a Maris shekara ta 1985, mata da maza da suke Sashen Rubuce-Rubuce a hedkwatar Shaidun Jehovah da ke New York, U.S.A., suka lura da wata aukuwa ta musamman. Karl F. Klein ya yi shekara 60 ke nan a hidima ta cikakken lokaci. Da ƙwazo, Ɗan’uwa Klein ya ce: “Jehovah ya yi mini alheri ƙwarai!” Ya lura cewa Zabura 37:4 aya ce ta Littafi Mai Tsarki da yake so sosai. Bayan haka, ya kaɗa molonsa da ya sa kowa farin ciki.

Shekara 15 da suka biyo bayan, Ɗan’uwa Klein ya ci gaba da aiki a sashen rubuce-rubuce kuma yana ɗaya daga cikin Hukumar Mulki na Shaidun Jehovah. Sai, a ranar 3 ga Janairu, 2001, a ɗan shekara 95, Karl Klein ya gama hidimarsa a duniya da aminci.

An haife Karl a Jamus. Iyalinsa suka ƙaura zuwa Amirka, kuma Karl ya yi girma a gefen Chicago, a Illinois. Yayin da suke yara, Karl da ƙaninsa Ted suka nuna suna son Littafi Mai Tsarki sosai. An yi wa Karl baftisma a shekara ta 1918, kuma abubuwan da ya ji a taron gunduma na Ɗaliban Littafi Mai Tsarki a shekara ta 1922 ya tartsatsa ƙaunar hidimar fage na dukan rayuwarsa. Ba ya son mako guda ya wuce ba tare da ya yi wa’azi ba, har a makonnin ƙarshe na rayuwarsa.

Karl ya zama ɗaya cikin waɗanda suke aiki a hedkwata a shekara ta 1925, da farko ya yi aiki a maɗaba’ar littattafai. Mai sha’awar kaɗe-kaɗe ne ƙwarai, ya kaɗa molo na wasu shekaru tsakanin makaɗa a wata tashar rediyo na Kirista. Bayan haka, ya yi aiki a Sashen Hidima, ya ji daɗin tarayyarsa da shugaban aikinsa T. J. Sullivan. Yayin nan, Ted ya yi aure, shi da matarsa, Doris, suka fara aikin wa’azi a ƙasar waje a Puerto Rico.

Karl Klein ya yi aiki a Sashen Rubuce-Rubuce, rabin ƙarni, inda ya ba da nasa gudummawa domin yana son yin bincike kuma yana da sanin Littafi Mai Tsarki ƙwarai. A shekara ta 1963 Karl ya auri Margareta, Ba’jamusiya, mai wa’azi a ƙasar waje da take hidima a Bolivia. Tare da taimakonta na ƙauna, musamman lokacin da yake ciwo, ya iya yin aiki sosai bayan shekaru da yawanci mutane suke yin murabus. Yadda yake son gaskiya haɗe da halinsa na son kaɗe-kaɗe, ya yi ƙari ga jawabai da ba za a manta da su ba a ikilisiyoyi da kuma a taron gunduma. Ba da daɗewa ba kafin ya mutu, ya shugabanci tattaunawa ta kowace safiya wa babban iyalin Bethel na New York, da ta amfani kuma ta sa duka suka yi murna.

Masu karanta Hasumiyar Tsaro kullum za su tuna da labarin rayuwar Ɗan’uwa Klein, a wani talifi mai kyau da aka buga cikin fitar 1 ga Oktoba, 1984 (Turanci). Za ka ji daɗin karantawa ko kuma sake karanta wannan labarin, da tuna cewa wanda ya rubuta shi ya daɗa yin kusan shekara goma sha biyar yana Kirista da ya ba da kai, mai aminci.

Tun da yana cikin waɗanda Ubangiji ya shafa, Ɗan’uwa Klein ya yi sha’awa da dukan zuciyarsa ya yi sarauta da Kristi a sama. Muna da cikakken dalilin gaskata cewa yanzu Jehovah ya cika wannan sha’awar.—Luka 22:28-30.

[Hoto a shafi na 31]

Karl a shekara ta 1943 tare da T. J. Sullivan da Ted da kuma Doris

[Hoto a shafi na 31]

Karl da Margareta, a Oktoba 2000

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba