Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w08 1/1 pp. 22-24
  • Abin Da Jehobah Ya Annabta Yana Faruwa

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Abin Da Jehobah Ya Annabta Yana Faruwa
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Ƙasashen Zamanin Dā
  • Bayani Mai Ban Al’ajabi
  • Littafi Mai Tsarki—Littafi Ne Daga Allah
    Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?
  • Ka Koyi Darussa Daga Annabcin Littafi Mai Tsarki
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2023
  • Yesu Kristi Ya Soma Mulki!
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2022
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
w08 1/1 pp. 22-24

Abin Da Jehobah Ya Annabta Yana Faruwa

“NI NE Allah, babu wanina; ni Allah ne, kuma babu wani mai-kama da ni; mai-bayana ƙarshe tun daga mafarin, tun zamanin dā kuma al’amuran da ba a rigaya a aika ba tukuna.” (Ishaya 46:9, 10) Jehobah ne, wanda zai iya annabta abin da zai faru a nan gaba ba tare da kuskure ba ya faɗi haka.

A dukan duniya an san cewa ’yan adam ba za su iya annabta abin da zai faru a nan gaba daidai ba. Da yake Littafi Mai Tsarki littafi ne na annabci wannan ya kamata ya motsa dukan masu son gaskiya su bincika ko daga Allah ne da gaske. Bari mu bincika wasu annabce-annabcen Littafi Mai Tsarki da sun riga sun cika.

Ƙasashen Zamanin Dā

Allah ya annabta cewa za a halaka Babila, Edom, Mowab, Ammon, da Taya har abada. (Irmiya 48:42; 49:17, 18; 51:24-26; Obadiah 8, 18; Zephaniah 2:8, 9) Da yake waɗannan al’umman ba sa wanzuwa a yanzu ya nuna cewa Kalmar Allah ta annabcin daidai ne.

Hakika, mutum yana iya cewa, ai, kowa yana iya annabta cewa al’umma za ta shuɗe da shigewar lokaci, ko yaya ƙarfinta. Amma irin wannan musū bai yi la’akari da cewa Littafi Mai Tsarki ya ba da bayanin dalla-dalla ba. Alal misali, ya ba da bayani dalla-dalla a kan yadda za a hamɓare Babila. Littafi Mai Tsarki ya annabta cewa mutanen Mediya ne za su ci birnin, ya faɗi cewa sojojin za su kasance ƙarƙashin shugabancin Cyrus, kuma koguna da ke kare birnin za su bushe.—Ishaya 13:17-19; 44:27–45:1.

Ba dukan annabcin Littafi Mai Tsarki ba ne ya annabta za a ci wata al’umma ko kuma mutane, kuma mutanen su daina wanzuwa har abada. Akasin haka, sa’ad da yake annabta cewa Babiloniyawa za su mallaki Urushalima, Allah ya ce birnin zai sake farfaɗowa ko da yake Babila ba ta sake waɗanda ta kama bauta. (Irmiya 24:4-7; 29:10; 30:18, 19) Hakan ya faru, kuma zuriyar Yahudawa sun ci gaba da wanzuwa har a yau.

Bugu da ƙari, Jehobah ya annabta cewa za a ci ƙasar Masar a yaƙi, amma “daga baya kuwa za a zauna cikinta, kamar cikin kwanakin dā.” Da shigewar lokaci, wannan ƙasar mai iko a dā za ta “zama mulki ƙanƙan.” (Irmiya 46:25, 26; Ezekiel 29:14, 15) Haka kuma ya faru kamar yadda aka annabta. Bugu da ƙari, Jehobah ya annabta cewa za a ci mulki Hellas, amma bai ce wannan al’ummar ba za ta sake wanzuwa ba. Menene muka koya daga ɓacewar mutane da Jehobah ya annabta za su halaka da kuma waɗanda bai yi musu irin wannan annabci ba? Hakan yana nuna cewa Kalmar Allah tana ɗauke da tabbataccen annabci.

Bayani Mai Ban Al’ajabi

Kamar yadda aka faɗa a baya, Jehobah ya ba da cikakken bayani game da yadda za a halaka Babila. Hakazalika, game da yadda za a halaka Taya, littafin Ezekiel ya ce za a kai duwatsunta, katakonta, da kuma turɓayanta “a tsakiyar ruwa.” (Ezekiel 26:4, 5, 12) Wannan annabcin ya cika a shekara ta 332 K.Z. sa’ad da Iskandari Mai Girma da sojojinsa suka yi amfani da kayayyaki daga ɓangaren birnin da aka halaka suka gina gada zuwa ɓangaren Taya da tsibiri ne, hakan ya sa suka ci ta a yaƙi.

Annabcin da aka rubuta a cikin Daniel 8:5-8, 21, 22 da 11:3,4 sun ba da cikakken bayani game da wani “Sarki Hellas” mai girma. Wannan sarki zai mutu a lokacin da yake cin nasara sosai a sarautarsa, kuma za a raɓa mulkinsa kashi huɗu amma ba a tsakanin zuriyarsa ba. Fiye da shekaru 200 bayan da aka rubuta wannan annabci, Iskandari Mai Girma ya zama wannan sarki. Tarihi ya gaya mana cewa ya mutu yana da ƙarfinsa kuma janar janar ɗinsa guda huɗu da ba zuriyarsa ba ne suka raɓa mulkinsa a tsakaninsu.

’Yan sūka suka ce an rubuta wannan annabcin bayan da abin ya faru ne. Ka sake duba labarin da ke cikin littafin Daniel da aka ambata a baya. Idan aka ɗauke shi a matsayin annabci, bayaninsa suna da ban al’ajabi. Amma idan tarihi ne aka ɗauke shi a matsayin annabci, zai kasance da rashin cikakken bayani. Idan wani mai-ruɗi da ya rayu bayan Iskandari yana son ya burge masu karatun annabci, me ya sa bai ambata cewa bayan mutuwar Iskandari, ’ya’yansa biyu za su yi ƙoƙari su ƙafa na su mulkin amma za a kashe su ba? Me ya sa bai faɗi cewa shekaru masu dama za su wuce kafin dukan janar janar ɗin su kafa sarautarsu bisa ɓangarori dabam na mulkin Iskandari ba? Hakika, me ya sa bai faɗi sunan sarki mai girma ba da kuma janar janar ɗinsa huɗun?

Da’awar da aka yi cewa an rubuta annabcin Littafi Mai Tsarki bayan abubuwan sun faru, ra’ayi ne na waɗanda kafin su bincika tabbacin, sun riga sun yi imani cewa ba zai yiwu ba a faɗi abin da zai faru nan gaba ba. Domin sun ƙi su amince cewa Littafi Mai Tsarki Kalmar Allah ce, dole ne su bayyana kome bisa ra’ayin ’yan adam. Duk da haka, Allah ya ba da isashen bayani game da annabce-annabcen don ya nuna cewa shi ne tushensu.a

Annabcin Littafi Mai Tsarki zai ƙarfafa bangaskiyarka idan ka ba da lokaci ka yi bimbini a kan annabce-annabcen da ka ke karantawa da kuma cikarsu. Me ya sa ba za ka yi nazarin annabcin Littafi Mai Tsarki ba? Taswira da ke shafofi 343 zuwa 346 na littafin nan “All Scripture Is Inspired of God and Beneficial” zai taimake ka.b Idan ka bi wannan shawara, ka yi nazarin da nufin ƙarfafa bangaskiyarka. Kada ka yi hanzari, don ka yi karutun kawai. Maimakon haka, ka yi bimbini a kan tabbacin cewa kome da Jehobah ya annabta zai faru.

[Hasiya]

a Domin ƙarin bayani na ƙaryata da’awar cewa an rubuta Littafi Mai Tsarki bayan abubuwan sun faru, ka dubi shafofi na 106-111 na littafin nan Is There a Creator Who Cares About You? da Shaidun Jehobah suka wallafa.

b Shaidun Jehobah ne suka wallafa.

[Box/Hoto a shafi na 24]

ƘA’IDODIN RAYUWA

Ga wani abu da za a yi bimbini a kai. Allah wanda ya annabta tasowa da faɗuwar masu iko na duniya shi ne Tushen ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki don zaman rayuwa. Wasu cikinsu shi ne:

Za ka girbe abin da ka shuka.—Galatiyawa 6:7.

Bayarwa ta fi karɓa albarka.—Ayukan Manzanni 20:35.

Masu-albarka ne masu-ladabi a ruhu.—Matta 5:3.

Idan ka yi amfani da waɗannan ƙa’idodin a rayuwarka, ka kasance da tabbaci cewa za su kasance gaskiya a gare ka.

[Hotuna a shafuffuka na 22, 23]

Kalmar Allah ta annabta cewa za a halaka waɗannan ƙasashe har abada . . .

EDOM

BABILA

. . . amma ba na waɗannan ba

HELLAS

MASAR

[Inda aka Daukos]

Pictorial Archive (Near Eastern History) Est.

WHO photo by Edouard Boubat

[Hoto a shafi na 23]

Iskandari mai Girma

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba