Domin Matasanmu
Yesu ya Warkar da Mutane ta Hanyar Mu’ujiza
Umurni: Ka yi wannan aikin a inda za ka iya mai da hankalinka wuri ɗaya. Sa’ad da kake karanta nassosin, ka ji kamar kana wurin sa’ad da abin ke faruwa. Ka yi tunanin yanayin a zuciyarka. Ka ji muryoyin. Ka ji yadda ainihin mutanen da ke ciki suke ji.
KA YI TUNANI A KAN YANAYIN—KA KARANTA MATTA 15:21-28.
A ganinka, yaya uwar take ji?
․․․․․
Wace irin murya ce ka “ji” daga bakin Yesu a ayoyi na gaba?
24 ․․․․․ 26 ․․․․․ 28 ․․․․․
KA YI BINCIKE SOSAI.
Sau nawa ne Yesu ya nuna ta wajen kalamai ko kuma abin da ya yi, cewa ba zai warkar da ɗiyar matar ba?
․․․․․
Da farko, me ya sa Yesu ya ce ba zai warkar da ita ba?
․․․․․
Me ya sa Yesu ya warkar da yarinyar?
․․․․․
KA YI AMFANI DA ABIN DA KA KOYA. KA RUBUTA ABIN DA KA KOYA GAME DA . . .
Sanin ya kamata da Yesu ya nuna.
․․․․․
Yadda za ka yi koyi da wannan halin sa’ad da kake sha’ani da mutane.
․․․․․
KA YI TUNANI A KAN YANAYIN—KA KARANTA MARKUS 8:22-25.
Waɗanne abubuwa ne kake tunanin kana gani da kuma sauti da kake ji a ciki da wajen ƙauyen?
․․․․․
KA YI BINCIKE SOSAI.
A ganinka, me ya sa Yesu ya fitar da mutumin bayan ƙauyen kafin ya warkar da shi?
․․․․․
KA YI AMFANI DA ABIN DA KA KOYA. KA RUBUTA ABIN DA KA KOYA GAME DA . . .
Yadda Yesu ya ji game da naƙasassu, duk da cewa bai taɓa naƙasa ba.
․․․․․
WAƊANNE FASALOLI NA WAƊANNAN LABARAN BIYU NA LITTAFI MAI TSARKI NE YA TAƁA KA SOSAI, KUMA ME YA SA?
․․․․․