Masu Karatu Sun Yi Tambaya
Me Ya Sa Shaidun Jehobah Ba Sa Zuwa Yaƙi?
A duk inda suke zaune, an san Shaidun Jehobah da guje wa saka hannu a yaƙi tsakanin ƙasashe ko kuwa tsakanin waɗanda suke zaune a ƙasa ɗaya. A shekaru hamsin da suka shige, littafin nan Australian Encyclopædia ya ce: “Shaidun Jehobah suna nuna tsaka-tsakanci sosai a lokacin yaƙi.”
Ainihin dalilin da ya sa Shaidu ba sa saka hannu a yaƙi shi ne, saka hannu a irin waɗannan yaƙe-yaƙen zai ɓata lamirinsu na Kirista. Sun koyar da lamirinsu da dokoki da kuma misalin Ubangiji Yesu Kristi. Ya umurci mabiyansa su ƙaunaci maƙwabtansu. Ya kuma umurce su: “Ku yi ƙaunar magabtanku, ku yi ma maƙiyanku nagarta.” (Luka 6:27; Matta 22:39) A lokacin da ɗaya daga cikin mabiyansa ya so ya kāre shi da takobi, Yesu ya ce masa: “Mai da takobinka kube. Duk wanda ya zari takobi, takobi ne ajalinsa.” (Matta 26:52, Littafi Mai Tsarki) Ta wajen magana da kuma misali, Yesu ya nuna dalla-dalla cewa mabiyansa ba za su yi amfani da makami ba.
Wani dalilin kuma da ya sa Shaidun Jehobah ba sa zuwa yaƙi shi ne cewa suna cikin rukunin addinin da mabiyansa ke ko’ina a duniya. Yaƙi zai sa ɗan’uwa ya yaƙi ɗan’uwansa, kuma hakan ba zai jitu da dokar Yesu da ta ce su nuna ‘ƙauna ga junansu’ ba.—Yohanna 13:35.
Ga Shaidun Jehobah, mizanan da aka ambata a baya game da ƙauna ba hasashe ba ne ba kawai. Ga misali, ka bincika matakan da suka ɗauka a lokacin Yaƙin Duniya na Biyu, a shekara ta 1939 zuwa 1945. A ƙasar Amirka, Shaidun Jehobah fiye da 4,300 ne aka jefa a gidajen kurkuku domin sun ƙi su shiga aikin soja. A ƙasar Britaniya, maza 1,500 tare da mata fiye da 300 ne aka jefa kurkuku don sun ƙi yin aikin soja. A Nazi da ke ƙasar Jamus, gwamnati ta ba da umurni a kashe Shaidu fiye da 270 don sun ƙi ɗaukan makamai. A ƙarƙashin mulkin Nazi, Shaidu fiye da 10,000 ne aka jefa kurkuku. Shaidun da ke ƙasar Japan sun sha wahala sosai. Duk mutanen da waɗanda suke ƙauna suka mutu a filin dāga na Yaƙin Duniya na Biyu, ko yaƙin da ya faru bayan hakan, su san cewa babu wani cikin Shaidun Jehobah da ke da alhakin kashe wani a cikinsu.
Ra’ayin Shaidun Jehobah game da yaƙi ya fita sarai a kalaman ƙarshe na Wolfgang Kusserow. A shekara ta 1942 Nazi ta yanke kan wannan ɗan Jamus ɗin ɗan shekara 20 domin ya ƙi zuwa yaƙi. (Ishaya 2:4) Ya faɗi kalaman da ke gaba a gaban kotun sojoji: “An yi reno na a matsayin Mashaidin Jehobah, bisa ga Kalmar Allah da ke cikin Nassosi Masu Tsarki. Doka mafi girma kuma mafi tsarki da ya ba mutane ita ce: ‘Ka ƙaunaci Allahnka fiye da komi kuma ka ƙaunaci maƙwabcinka kamar kanka.’ Sauran dokokin sun ce: ‘Kada ka yi kisan kai.’ Itatuwa ne Mahaliccinmu ya rubuta wa waɗannan abubuwan?”—Markus 12:29-31; Fitowa 20:13.
Shaidun Jehobah sun gaskata cewa Jehobah, Allah Maɗaukaki, ne kaɗai zai kawo salama na dindindin a duniya. Suna jiran lokacin da Allah zai cika alkawarin da ya yi na “sa yaƙoƙi su ƙare har iyakar duniya.”—Zabura 46:9.