Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w08 10/15 p. 16
  • “Hakika Wannan Sunan Allah Ne Mafi Tsarki Mai Girma”

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • “Hakika Wannan Sunan Allah Ne Mafi Tsarki Mai Girma”
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
w08 10/15 p. 16

“Hakika Wannan Sunan Allah Ne Mafi Tsarki Mai Girma”

Nicholas ɗan birnin Cusa ne ya yi wannan kalamin a jawabin da ya yi a shekara ta 1430.a Shi mutumi ne mai son koyan abubuwa da yawa, alal misali ya koyi Helenanci, Ibrananci, falsafa, ilimin sanin Allah, lissafi, da kuma ilimin sanin taurari. Sa’ad da yake shekara 22, ya zama Dakta na dokar Cocin Katolika. A shekara ta 1448 an naɗa shi ya zama Kardinal.

Kusan shekaru 550 da suka shige, Nicholas ɗan birnin Cusa ce ya kafa gidan da ake kula da tsofaffi a Kues, yanzu ana kiran wurin Bernkastel-Kues, wani gari da ke mil 80 a kudancin Bonn a Jamus. A yanzu wannan ginin ya zama wajen aje littattafan Cusa da ke ɗauke da fiye da littatafai na dā guda 310. Ɗaya daga cikinsu shi ne littafin Codex Cusanus guda 220 inda aka rubuta jawabin da Cusa ya yi a shekara ta 1430. A wannan jawabin, mai jigo, “A Cikin Farko Akwai Kalma”, Nicholas ɗan birnin Cusa ya rubuta Iehoua da harshen Latin, wato Jehovah kenan a Turanci.b Shafi na 56 yana ɗauke da wannan kalamin game da sunan Allah: “Daga wajen Allah ne. Suna ne mai baƙaƙe huɗu. . . . Hakika wannan sunan Allah ne mafi tsarki mai girma.” Furcin da Nicholas ɗan birnin Cusa ya yi ya nuna cewa sunan Allah yana cikin Nassi na Ibrananci na asali.—Fit. 6:3.

Daga ƙarni na 15 wannan littafin shi ne litafin da ya fi daɗewa da aka rubuta “Iehoua” da baƙaƙe. Wannan tabbacin ya sake nuna cewa yadda aka rubuta sunan Allah da ya yi kusa da “Jehobah” shi ne ainihin fassarar sunan Allah a ƙarnuka da suka wuce.

[Hasiya]

a Ana kuma kiran Nicholas ɗan birnin Cusa da waɗannan sunayen, Nikolaus Cryfts (wato, Krebs), Nicolaus Cusanus, da Nikolaus von Kues. Kues shi ne sunan wani gari a Jamus inda aka haife shi.

b Manufar wannan jawabin shi ne don ya goyi bayan koyarwar Allah uku cikin ɗaya.

[Hoto a shafi na 16]

Wajen aje littattafai a Cusa

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba