Shaidun Jehobah Suna Raba Aure Ne?
“IDAN wata mai aure ta canja addininta, hakan zai raba aure.” Abin da mutane da yawa suke da’awa ke nan. A wani lokaci ana yi wa wata mai aure da take so ta zama Mashaidiyar Jehobah. Amma wannan abin da ake faɗa gaskiya ne?
Hakika, idan abokiyar aure ta ta fara sha’awar wani addini ko kuma ta fara canja ra’ayinta game da abin da ta yi imani da shi dā, zai iya kasancewa abin mamaki ga abokin aurenta. Zai iya kawo damuwa, rashin jin daɗi, har ma da ƙiyayya.
Sau da yawa mace ce take ganin ya kamata ta canja addininta. Idan matarka tana nazari da Shaidun Jehobah yaya hakan zai shafi aurenka? Idan ke mace ce da kike nazari da Shaidun Jehobah, menene za ki iya yi domin ki rage damuwar da maigidanki zai yi?
Ra’ayin Masu Gida
Mark, wanda yake da zama a Austireliya, aurensa yana da shekara 12 sa’ad da matarsa ta fara nazarin Littafi Mai Tsarki da Shaidun Jehobah. “Muna farin ciki a aurenmu kuma ina aiki mai gamsarwa,” in ji Mark. “Rayuwa tana da daɗi. Sai matata ta yanke shawara za ta yi nazari da Shaidun Jehobah. Farat ɗaya sai na ji ana yi wa salon rayuwata barazana. Da farko, ban ji daɗin irin sabuwar sha’awa da matata take da shi ga Littafi Mai Tsarki ba, amma da ta gaya mini cewa ta yanke shawara za ta yi baftisma ta zama Mashaidiyar Jehobah abin ya dame ni ƙwarai.”
Mark ya fara tunani ko sabon addinin matarsa zai rabu su. Ya yi tunanin ya hana ta nazarin Littafi Mai Tsarki kuma ya haramta mata duk wani hulɗa da Shaidun Jehobah. Amma maimakon ya yanke irin wannan shawarar, Mark ya ɗan ƙyale lokaci ya shige. Menene ya faru da aurensa?
“Abin farin ciki,” in ji Mark, “aurenmu ya fi ma dā ƙarfi. Ya ci gaba da kyautata tun da matata ta zama Mashaidiyar Jehobah shekaru 15 da suka wuce.” Menene ya taimaki auren ya yi nasara? “Da ya tuna baya, Mark ya ce, “domin matata ta yi amfani da shawara mai kyau da ke cikin Littafi Mai Tsarki. Ta yi ƙoƙari ta girmama ni a dukan lokaci.”
Shawara Daga Mata da Suka Yi Nasara
Idan ke mace ce da kike cuɗanya da Shaidun Jehobah, menene za ki yi kuma ki faɗa da zai taimaka wajen rage damuwar mijinki? Ki yi la’akari da kalaman waɗannan mata daga ɓangarori dabam dabam na duniya.
Sakiko, daga Japan: “Na yi shekara 31 ina da aure kuma ina da yara uku. Shekaru na 22 ke nan ina Mashaidiyar Jehobah. Zama tare da maigidan da bai yi imani da abin da na yi ba wani lokaci ƙalubale ne ƙwarai. Amma in ƙoƙari ƙwarai na yi amfani da shawarar Littafi Mai Tsarki, ‘yi hanzarin ji, yi jinkirin yin magana, yi jinkirin yin fushi.’ (Yaƙ. 1:19) Na yi ƙoƙari na kasance mai kirki ga maigidana kuma na yarda da abin da yake bukata idan hakan bai saɓa wa mizanan Littafi Mai Tsarki ba. Wannan ya taimaka wa aurenmu ya yi nasara.”
Nadezhda, daga Rasha: “Shekaru na 28 ke nan da aure kuma yanzu shekarata 16 da yin baftisma. Kafin na yi nazarin Littafi Mai Tsarki, ban yarda mijina ya kasance shi ne shugaban iyali ba. Na fi so na yanke nawa shawara da kaina. Amma, a hankali na fahimci cewa bin mizanan Littafi Mai Tsarki ya kowa kwanciyar hankali da farin cikin a iyalinmu. (1 Korinthiyawa 11:3) A hankali ya kasance mini da sauƙi in miƙa kai, kuma maigidana ya lura da waɗannan canje-canje da ya yi.”
Marli, Brazil: “Ina da ’ya’ya biyu kuma shekaru na 22 ke nan da aure. Na zama Mashaidiyar Jehobah shekaru 16 da suka shige. Na koyi cewa Jehobah Allah yana son masu aure su zauna tare, kada su rabu. Saboda haka, na yi ƙoƙari na zama matar kirki, na yi magana kuma na yi abubuwa a hanyar da za ta sa Jehobah da kuma maigidana farin ciki.”
Larisa, Rasha: “Sa’ad da na zama Mashaidiyar Jehobah shekaru 19 da suka shige, na fahimci cewa abu mafi muhimmanci shi ne na yi canje-canje a rayuwata. Maigidana ya ga yadda Littafi Mai Tsarki ya kyautata rayuwata, hakan ya sa na ƙaunace shi ƙwarai. Da farko, mun sami rashin jituwa game da renon yara amma mun magance dukan waɗannan matsalolin. Maigidana ya ƙyale yaranmu su bi ni su halarci taron addini da nake halarta domin ya san ana koya musu abin da zai amfani su ne.”
Valquiria, daga Brazil: “Ina da shekara 19 da aure kuma ina da yaro ɗaya. Na zama Mashaidiyar Jehobah shekaru 13 da suka shige. Da farko, mijina ba ya su na fita hidimar fage. Amma na koyi na kwantar masa da hankali cikin sauƙin hali kuma na sa ya ga cewa Littafi Mai Tsarki ya sa na canja halina. A hankali maigidana ya fahimci cewa yana da muhimmancin in fita wa’azi. Yanzu, yana tallafa mini ƙwarai wajen ayyukana na ruhaniya. Sa’ad da na je nazari Littafi Mai Tsarki da mutane a ƙauyuka, yana ma kai ni a motarsa kuma ya jira ni cikin haƙuri har sai na gama.”
Rinjayar Aure a Hanya Mai Kyau
Idan matarka tana hulɗa da Shaidun Jehobah, kada ka ji tsoro cewa hakan zai kashe maka aure. Kamar yadda maza da mata da yawa a dukan ɓangarorin duniya suka fahimta, Littafi Mai Tsarki yana rinjayar aure a hanya mai kyau.
Wani Maigida da ba Mashaidin Jehobah ba ne ya ce: “Da farko na damu sa’ad da matata ta karɓi imanin Shaidun Jehobah, amma yanzu na sani cewa riba da na samu ya fi damuwa da na yi.” Wani kuma ya faɗa haka game da matarsa: “Amincin matata, ƙudurinta, sun sa ina sha’awar Shaidun Jehobah. Aurenmu ya amfana ƙwarai daga abin da ta yi imani da shi. Muna yin la’akari da juna kuma muna zaman aure yadda ya kamata.”
[Akwati/Hotunan da ke shafi na 13]
Yaya Shaidun Jehobah Suke Ɗaukan Aure?
Littafi Mai Tsarki Kalmar Allah ne ga Shaidun Jehobah. Saboda haka suna ɗaukan abin da ya ce game da aure da muhimmanci. Ka lura da amsoshi da Littafi Mai Tsarki ya bayar ga waɗannan tambayoyi:
▪ Shin Shaidun Jehobah suna ƙarfafa ’yan’uwansu ne su rabu da abokan aurensu da ba Shaidun Jehobah ba? A’a. Manzo Bulus ya rubuta: “Idan kowane ɗan’uwa yana da matatasa mara-bangaskiya, tana kuwa yarda ta zauna tare da shi, kada ya rabu da ita. Mace kuwa wadda ta ke da miji mara-bangaskiya, yana kuwa yarda ya zauna tare da ita, kada ta rabu da mijinta.” (1 Korinthiyawa 7:12, 13) Shaidun Jehobah suna bin wannan umurnin.
▪ Ana ƙarfafa mace wadda Mashaidiyar Jehobah ce ta yi banza da bukatun mijinta idan bai yi imani da abin da ta gaskata ba? A’a. Manzo Bitrus ya rubuta: “Hakanan, ku mata kuma, ku yi zaman biyayya ga mazaje naku; domin ko da akwai waɗansu da ba su yin biyayya da magana, su rinjayu banda magana saboda halayen matansu; suna lura da halayenku masu-tsabta tare da tsoro.”—1 Bitrus 3:1, 2.
▪ Shin Shaidun Jehobah suna koyarwa ne cewa namiji yana da iko marar iyaka? A’a. Manzo Bulus ya ce: “Amma ina so ku sani, kan kowane namiji Kristi ne; kan mace kuma namiji ne; kan Kristi kuma Allah ne.” (1 Korinthiyawa 11:3) Mace Kirista za ta daraja mijinta domin shi ne shugaban iyali. Amma, ikonsa yana da iyaka. Zai amsa wa Allah da kuma Kristi. Saboda haka, idan namiji ya umurci matarsa ta yi abin da zai saɓa wa dokar Allah, mace Kirista za ta “fi biyayya ga Allah da mutane.”—Ayukan Manzanni 5:29.
▪ Shaidun Jehobah suna koyarwa ne cewa an haramta kisan aure? A’a. Yesu ya ce: ‘Ni ma na ce muku, Dukan wanda ya saki matatasa, in ba domin fasikanci ba, ya kuwa auri wata, zina ya ke yi.’ (Matta 19:9) Saboda haka, Shaidun Jehobah sun yi imani da abin da Yesu ya ce, zina tana iya sa a kashe aure. Sun kuma yi imani cewa aure ba abin da za a kashe ba ne kawai domin wasu dalilai. Suna ƙarfafa ’yan’uwansu su bi abin da Yesu ya ce: “Saboda wannan namiji za ya bar ubansa da uwatasa shi manne ma matatasa; su biyu kuwa za su zama nama ɗaya . . . Abin da Allah ya gama fa, kada mutum shi raba.”—Matta 19:5, 6.