Sa’ad da Jehobah Ya Kwatanta Kansa
Fitowa 34:6, 7
YAYA za ka kwatanta Allah, mutumtakarsa da kuma hanyoyinsa? A ce za ka iya tambayar Allah game da kansa, sa’an nan ka saurari yadda ya kwatanta halayensa. Annabi Musa ya shaida hakan. Abin godiya, an hure shi ya rubuta abin da ya faru.
Sa’ad da yake kan Dutsen Sinai, Musa ya roƙi Jehobah: “Ka nuna mani darajarka.” (Fitowa 33:18) Washegari, annabin ya sami gatan hangen ɗaukakar Allah.a Musa bai ba da cikakken bayani game da abin da ya gani a wannan wahayin ba. Maimakon haka, ya rubuta abin da ya fi muhimmanci, wato, abin da Allah ya ce. Bari mu bincika abin da Jehobah ya ce, kamar yadda aka rubuta a Fitowa 34:6, 7.
Abu na farko da Jehobah ya bayyana game da kansa shi ne cewa, shi “Allah ne cike da juyayi, mai-alheri kuma.” (Aya ta 6) In ji wani masani, kalmar Ibrananci da aka fassara “juyayi” yana nuna “jin ƙai na Allah, irin na uba ga ’ya’yansa.” Kalmar kuma da aka fassara “mai-alheri” ta yi daidai da aikatau da “ya kwatanta mutumin da zuciyarsa ta motsa shi don ya taimaki wani mabukaci.” Babu shakka, Jehobah yana so mu fahimci cewa yana kula da dukan bayinsa kamar yadda iyaye ke kula da yaransu; cikin yawan ƙauna da kuma biyan bukatunsu sosai.—Zabura 103:8, 13.
Bayan haka, Jehobah ya ce shi “mai-Jinkirin fushi” ne. (Aya ta 6) Ba ya yawan fushi da bayinsa da ke duniya. Maimakon haka, yana haƙuri da su, yana jimrewa da kasawarsu kuma yana ba su zarafin su tuba daga halayensu marar kyau.—2 Bitrus 3:9.
Allah ya ci gaba da cewa, shi “mai-yalwar jinƙai da gaskiya” ne. (Aya ta 6) Yawan jin ƙai, ko ƙauna ta aminci, hali ne mai tamani da Jehobah yake amfani da shi ya kafa dangantaka mai jurewa da mutanensa. (Kubawar Shari’a 7:9) Jehobah ne tushen gaskiya. Ba zai taɓa yaudararmu ba kuma ba za mu iya yaudarar sa ba. Da yake shi “Allah na gaskiya” ne, za mu iya dogara ga dukan abin da ya faɗa, har da alkawarinsa game da nan gaba.—Zabura 31:5.
Wata gaskiya ta musamman da Jehobah yake so mu sani game da shi ita ce, yana “gafarta laifi da saɓo da zunubi.” (Aya ta 7) Yana “hanzarin gafartawa” masu zunubi da suka tuba. (Zabura 86:5) Duk da haka, Jehobah baya amincewa da zunubi. Ya bayyana cewa “ba shi kuɓutadda mai-laifi ko kaɗan.” (Aya ta 7) Allah mai tsarki kuma mai adalci zai yi wa waɗanda suke yin zunubi da gangan horo. Ko ba jima ko ba daɗe za su ga sakamakon zunubinsu.
Bayyana halayensa da Jehobah ya yi ya nuna dalla-dalla cewa yana son mu san shi kuma mu fahimci mutumtakarsa da kuma hanyoyinsa. Hakan bai motsa ka ba ka ƙara sanin halayensa masu kyau?
[Hasiya]
a Musa bai ga Jehobah da idanunsa ba, domin ba mutumin da zai ga Allah kuma ya rayu. (Fitowa 33:20) Hakika Jehobah ya nuna wa Musa wahayin ɗaukakarsa ta wajen wani mala’ika ne.