Ka Yi Koyi Da Imaninsu
Ta Yi Amfani da Hankalinta
ABIGAIL ta ga tsoron da ke idanun saurayin. Hankalinsa ya tashi ne saboda wani dalili mai muhimmanci. Wani mugun haɗari na tafe. A daidai wannan lokacin, mayaƙa ɗari huɗu suna kan hanya, sun ƙudurta cewa za su kashe duka mazan da ke gidan Nabal, mijin Abigail. Me ya sa?
Nabal ne ya jawo hakan. Ya yi wulaƙanci da rashin kunya, kamar yadda ya saba yi. Amma, a wannan lokacin, ya wulaƙanta wanda ya fi ƙarfinsa, wato, shugaban wasu mayaƙa ƙwararru kuma masu aminci. Sai wani matashi da ke yi wa Nabal aiki, wataƙila makiyayi ne, ya je wajen Abigail, da tabbaci cewa za ta nemi yadda za ta kāre su. Amma menene mace gudu za ta iya yi wa rundunar soja?
Da farko, bari mu samu ƙarin bayani game da wannan matar da ta yi fice. Wacece Abigail? Ta yaya wannan bala’in ya taso? Kuma menene za mu iya koya daga misalinta mai kyau na bangaskiya?
‘Mai-Fahimi Kuma Kyakkyawa’
Abigail da Nabal ba su dace da juna ba. Nabal ya yi dacen mata, amma ita Abigail ba ta yi dacen miji ba. Hakika, mutumin yana da kuɗi. Saboda haka, ya ɗauki kansa da muhimmanci sosai, amma yaya wasu suka ɗauke shi? Da wuya ka ga wani a Littafi Mai Tsarki da aka bayyana da irin waɗannan kalamai masu muni. Sunansa yana nufin “Mara hankali” ko “Wawa.” Iyayensa ne suka ba shi wannan sunan ko kuwa sunan da ya samu ne saboda ayyukansa? Ko ta yaya, ya aikata ma’anar sunansa. Nabal “mai-tankiya ne mai-munanan ayuka.” Azzalumi da mashayi, mutane suna jin tsoronsa kuma sun ƙi jininsa.—1 Samuila 25:2, 3, 17, 21, 25.
Abigail kuwa ta bambanta. Sunanta na nufin “Mahaifina Ya Faranta Zuciyarsa.” Iyaye maza da yawa suna alfahari idan suna da kyakkyawar ’ya, amma uba mai hikima ya fi farin ciki idan ’yarsa tana da hali mai kyau. Sau da yawa, mutumin da ke da kyaun sura ba ya tunanin muhimmancin kasancewa da halayen nan kamar yin amfani da hankali, hikima, gaba gaɗi, ko bangaskiya. Amma Abigail ba ta yi hakan ba. Littafi Mai Tsarki ya ce ita “mai-fahimi ce, kyakkyawa” kuma.—1 Samuila 25:3.
Wasu a yau za su yi mamakin abin da ya sa irin wannan kyakkyawar mace mai hankali ta auri wannan mutumin marar hankali. Ka tuna cewa iyaye ne suke haɗa yawancin auren da ake yi a zamanin dā. Ko da ba a yi hakan ba, amincewar iyaye yana da muhimmanci sosai. Iyayen Abigail sun goyi bayan wannan aure ne, ko kuma sun shirya shi, domin suna son wadata da kuma arzikin Nabal? Sun yarda ne saboda talauci yana damun su? Ko yaya dai, wadatar Nabal ba ta sa shi ya zama miji mai hankali ba.
Iyaye masu hikima suna koya wa yaransu yadda za su ɗauki aure da daraja. Ba sa gaya wa yaransu su auri wani saboda wadata ko kuwa su matsa masu su fara yin soyayya da wani sa’ad da ba su isa yin hakan ba. (1 Korinthiyawa 7:36) Amma dai, lokaci ya riga ya ƙure da Abigail za ta yi irin waɗannan tunanin. Ko menene dalili dai, ta auri Nabal, kuma ta ƙudurta ta kasance da hikima a yanayi mai tsanani.
Ya “Yi Masu Furji”
Nabal ya daɗa tsananta yanayin Abigail fiye da dā. Dauda ne mutumin da ya zaga. Wannan bawan Jehobah ne amintacce wanda annabi Sama’ila ya shafa, don nuna cewa Allah ya zaɓe shi ya gaji kujeran Saul a matsayin sarki. (1 Samuila 16:1, 2, 11-13) Sa’ad da ya gudu daga Sarki Saul mai kishi da kisa, Dauda yana zaune a cikin jeji tare da rundunarsa ɗari shida masu aminci.
Nabal yana da zama a ƙasar Maon amma wataƙila yana aiki kuma yana da fili a kusa da Karmel.a Waɗannan garurrukan masu tsauni suna da ciyayi da suka dace da yin kiwon tumaki, kuma Nabal yana da tumaki dubu uku. Kurmi ya zagaye garin. Jejin Paran yana kudancin ƙasar. Hayar zuwa Tekun Gishiri kuma tana daga gabas cikin hamada cike da kwazazzabai da koguna. A waɗannan wuraren ne Dauda da mutanensa suke fama don su rayu, suna farautar abin da za su ci da kuma jimre wahaloli da yawa. Suna yawan haɗuwa da matasan da ke kiwon tumakin Nabal mai arziki.
Yaya waɗannan rundunar sojojin da suke shan wahala don su rayu suka bi da waɗannan makiyayan? Suna iya satar tunkiya a kai a kai idan suka ga damar yin hakan, amma ba su yi hakan ba. Akasin hakan, sun zama kamar ganuwar tsaro ga tumakin Nabal da bayinsa. (1 Samuila 25:15, 16) Tumaki da makiyaya suna fuskantar haɗarurruka da yawa. A lokacin akwai masu kwace da kisa da yawa. Iyakar kudancin ƙasar Isra’ila ta yi kusa da wurin, saboda haka, a yawancin lokaci ɓarayi daga ƙasashen wajen suna shiga su yi sata.b
Ba ƙaramin aiki ba ne ciyar da dukan waɗannan mutanen a cikin jeji. Saboda haka, wata rana Dauda ya aika mutane goma zuwa wurin Nabal don neman taimako. Dauda ya zaɓi lokaci mafi kyau. Lokacin biki ne na rarraba tumaki, sa’ad da ake ba da kyauta da yin biki. Dauda ya yi amfani da kalamai masu kyau, kuma masu daɗin ji. Ya ma kira kansa “ɗanka Dauda,” wataƙila saboda shekarun Nabal. Menene Nabal ya ce?—1 Samuila 25:5-8.
Sai ya yi fushi! “Ya kuwa yi masu furji” in ji matashin da aka ambata da farko sa’ad da yake bayyana wa Abigail abin da ya faru. Nabal marowaci ya yi gunaguni game da abincinsa, ruwa, da kuma naman da ya yanka. Ya yi wa Dauda ba’a kuma ya ɗauke shi mutumi marar muhimmanci kuma ya kwatanta shi da bawan da ya gudu daga maigidansa. Wataƙila ra’ayin Nabal ya yi daidai da na Saul, wanda ya ƙi jinin Dauda. Su biyun ba su da ra’ayin Jehobah. Jehobah ya ƙaunace Dauda kuma ya gan shi a matsayin sarkin Isra’ila mai jiran gado, ba bawa mai tawaye ba.—1 Samuila 25:10, 11, 14.
Sa’ad da ’yan aiken Dauda suka gaya masa abin da ya faru, sai ya yi fushi. Ya ce wa mutanensa, “kowane mutum shi rataye takobinsa.” Riƙe da na sa makamin, Dauda ya tafi da mutanensa ɗari huɗu don su kai hari. Ya yi alkawarin kashe duka mazan da ke gidan Nabal. (1 Samuila 25:12, 13, 21, 22) Ya kamata Dauda ya yi fushi, amma yadda yake son ya nuna fushinsa ne bai dace ba. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Fushin mutum ba ya aikata adalcin Allah.” (Yaƙub 1:20) Ta yaya, Abigail za ta ceci mutanen gidanta?
“Mai-Albarka Ce Hikimarki”
Mun riga mun ga yadda Abigail ta ɗauki mataki na farko don daidaita abin da ya riga ya faru. Akasin mijinta, Nabal, ta saurara sosai. Bawan ya ce game da Nabal: “Shi shaƙiyin mutum ne, har ba shi yiwuwa a yi magana da shi.”c (1 Samuila 25:17) Abin baƙin ciki, Nabal bai saurara ba saboda ya ɗauki kansa da muhimmanci. Irin wannan girman kan ya zama ruwan dare a yau. Amma wannan bawan ya san cewa ba haka Abigail take ba, shi ya sa ya gaya mata wannan matsalar.
Abigail ta yi tunani kuma ta ɗauki mataki nan da nan. Mun karanta cewa, “Abigail ta yi sauri.” Sau huɗu a wannan labarin mun ga wannan aikatau, “sauri,” da aka yi amfani da shi game da wannan matar. Ta shirya kyauta mai kyau ga Dauda da mutanensa. Ya haɗa da gurasa, ruwan anab, raguna, soyayyen hatsi, wainar ’ya’yan inabi, da wainar ɓaure. Babu shakka, Abigail ta san abubuwan da take da shi kuma takan aikata ayyukanta na gida, kamar mace mai tsarkin rai da aka kwatanta a littafin Misalai. (Misalai 31:10-31) Ta sa wasu cikin bayinta su yi gaba da tanadodin, sai ta biyo bayansu ita kaɗai. Mun karanta cewa “amma ba ta faɗa wa Nabal, mijinta ba.”—1 Samuila 25:18, 19, Littafi Mai Tsarki.
Hakan ya nuna cewa Abigail ba ta daraja matsayin mijinta ne? A’a. Nabal ya riga ya aikata abin da bai da kyau ga shafaffen bawan Jehobah, kuma wannan wataƙila zai kai ga mutuwar mutanen da ba su yi laifi ba a gidan Nabal. Da a ce Abigail ba ta yi wani abu ba, da wataƙila ta saka hannu a laifin da mijinta ya yi? Ko yaya dai, ya kamata ta yi biyayya ga Allahnta fiye da mijinta.
Ba da daɗewa ba, Abigail ta haɗu da Dauda da mutanensa. Kuma ta yi sauri, ta sauko daga jakinta kuma ta durƙusa a gaban Dauda. (1 Samuila 25:20, 23) Sai ta gaya wa Dauda yadda ta ji, kuma ta roƙe shi a madadin maigidanta da mutanen gidanta. Menene ya sa maganar ta ya shiga kunnen Dauda?
Ta ɗauki nauyin laifin da mijinta ya yi kuma ta ce wa Dauda ya yafe mata. Ta yarda cewa mijinta marar hankali ne kamar yadda sunansa yake nufi, wataƙila hakan yana nufin cewa Dauda zai ɓata lokacinsa ne kawai idan ya ce zai yi wa irin wannan mutumin horo. Ta nuna dogarar ta ga Dauda a matsayin wakilin Jehobah, da sanin cewa “yana yaƙin jihadin Ubangiji.” Ta kuma nuna cewa ta san alkawarin da Jehobah ya yi wa Dauda game da sarauta, domin ta ce ‘Ubangiji zai sanya ka sarki bisa ga Isra’ila.’ Bugu da ƙari, ta gaya wa Dauda kada ya ɗauki matakin da zai sa ya ɗauki alhakin jini ko kuma zai zama “abin ladama,” wato, lamirinsa ya dame shi. (1 Samuila 25:24-31) Waɗannan kalamai ne masu ban sha’awa!
Menene Dauda ya yi? Ya karɓi abubuwan da Abigail ta kawo kuma ya ce: “Mai-albarka ne Ubangiji Allah na Isra’ila, wanda ya aiko ki yau garin ki tarbe ni: mai-albarka ce hikimarki, mai-albarka ce ke kuma da kin hana ni yau daga alhakin jini.” Dauda ya yaba mata don hanzarin da ta yi don ta same shi, kuma ya faɗi cewa ta hana shi ɗaukan alhakin jini. Ya ce mata: “Ki isa gidanki lafiya,” kuma ya daɗa cewa: “Ga shi, na saurari muryarki.”—1 Samuila 25:32-35.
“Ga Baiwarka”
Bayan dukansu sun tafi gidajensu, Abigail ta ci gaba da yin tunani game da wannan haɗuwar, kuma ta ga bambancin da ke tsakanin amintaccen sarki Dauda da mijinta marar hankali. Amma ba ta ci gaba da yin wannan tunanin ba. Mun karanta: “Sai Abigail ta zo wurin Nabal.” Hakika, ta koma wurin mijinta, kuma ta ci gaba da yin aikace-aikacenta na gida a matsayin matarsa. Tana bukatan ta gaya masa game da kyautar da ta yi wa Dauda da mutanensa. Domin ya kamata ya sani. Kuma tana bukatan ta gaya masa game da haɗarin da ta kawar, domin kunyar za ta yi masa yawa idan ya ji hakan a wani wurin dabam. Amma ba za ta iya gaya masa ba yanzu. Yana yin biki kamar sarki kuma ya riga ya bugu sosai.—1 Samuila 25:36.
Kuma don nuna ƙarfin zuciya da hankali, ta dakata har sai gari ya waye, lokacin da giyan ya riga ya sake shi. Zai kasance cikin hankalinsa sosai kuma zai fahimci abin da ta faɗa, amma hakan yana da lahani sosai saboda fushinsa. Duk da haka, ta gaya masa dukan abin da ya faru. Babu shakka, ta yi tsammanin cewa zai yi fushi sosai kuma ya hau ta da faɗa. Maimakon haka, ya zauna shiru, ya kasa yin motsi.—1 Samuila 25:37.
Menene ya same shi? “Zuciyassa kuwa ta mutu a cikinsa, ya zama kamar dutse.” Wataƙila ya samu wani irin ciwon gazawar jiki. Amma dai, bayan kwanaki goma, sai ya mutu, ba saboda cuta ba. “Ubangiji ya buga Nabal har ya mutu.” (1 Samuila 25:38) Da wannan hukunci na adalci, Abigail ta huta da matsalar da take samu a aurenta. Ko da yake Jehobah ba ya yin hukunci cikin mu’ujiza a yau, amma wannan labarin ya tuna mana cewa babu zaluncin da ba ya gani. A daidai lokacinsa, zai yi hukunci.
Ban da samun tsira daga aure marar kyau, Abigail za ta sami wata albarkar. Sa’ad da Dauda ya samu labari cewa Nabal ya mutu, sai ya aika saƙo wajen Abigail cewa yana son ya aure ta. Sai ta ce: “Ga baiwarka kuyanga ce ta wanki ƙafafun bayin ubangijina.” Hakika, ba ta canja halayen ta masu kyau ba duk da cewa tana son ta auri Dauda; har ma ta ce za ta zama baiwa ga bayinsa! Kuma mun sake karanta cewa ta yi hanzari don ta tafi wajen Dauda.—1 Samuila 25:39-42.
Hakan baya nufin cewa ta daina samun matsala, zaman Abigail tare da Dauda ba zai kasance mai sauƙi a kowane lokaci ba. Dauda ya riga ya auri Ahinoam, kuma auren mata da yawa yakan kawo ƙalubale na musamman ga mata amintattu a dā. Kuma Dauda bai zama sarki ba tukun; matsaloli da wahaloli za su ɓullo kafin ya soma bauta wa Jehobah a wannan matsayin. Amma yayin da Abigail ta taimaka wa Dauda a rayuwarsa, har ta haifar masa ɗa, ta ga cewa ta samu mijin da ya daraja ta kuma yana kāre ta. Akwai lokacin da ya cece ta daga hannun masu sace mutane! (1 Samuila 30:1-19) Da haka, Dauda ya yi koyi da Jehobah Allah, wanda yake ƙauna da kuma daraja irin waɗannan mata masu gaba gaɗi, da aminci.
[Hasiya]
a Wannan ba sanannen Dutsen Karmel ɗin da ke arewancin ƙasar ba ne amma wanda ke gefen jejin da ke kudu ne.
b Wataƙila Dauda yana ganin cewa tsare ’yan garin tare da garkensu hidima ce ga Jehobah Allah. A wannan zamanin, nufin Jehobah ne zuriyar Ibrahim, Ishaku da Yakubu su zauna a ƙasar. Saboda haka, kāre ta daga ɓarayin da suke shigowa daga ƙasashen waje, hidima ce mai tsarki.
c Furcin da wannan bawan ya yi amfani da shi yana nufin “ɗan belial (marar amfani).” Wasu Littafi Mai Tsarki sun bayyana Nabal kamar “mutumin da ba ya saurarar kowa,” kuma a ƙarshe, “yi masa magana bai da amfani.”
[Hotunan da ke shafi na 23]
Akasin mijinta, Abigail tana saurarawa sosai
[Hotunan da ke shafi na 24]
Abigail ta nuna tawali’u, gaba gaɗi, da hankali sa’ad da take magana da Dauda