Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w11 1/1 pp. 15-17
  • “A Gare Ni, Gata ne Mai Girma”

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • “A Gare Ni, Gata ne Mai Girma”
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
  • Makamantan Littattafai
  • Mun Koyi Darussa da Dama Daga Malamin da Babu Kamar Sa
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2025
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
w11 1/1 pp. 15-17

Wasiƙa Daga Ƙasar Haiti

“A Gare Ni, Gata ne Mai Girma”

BAYAN girgizar ƙasar da aka yi a ƙasar Haiti a ranar 12 ga Janairu, 2010, kallon irin ɓarnar da ya faru a cikin labarai ya yi mini wuya. A ranar 20 ga watan, ƙawata Carmen ta kira ni kuma ta ba ni shawarar mu je ƙasar Haiti a matsayin masu aikin agaji. Na haɗu da Carmen wasu shekaru ne da suka shige sa’ad da muka yi aikin nas da suka ba da kansu da son rai a wani wurin da ake gina Majami’ar Mulki. Tun daga lokacin, mun je inda aka yi ayyuka dabam-dabam kuma mun zama abokai na kud da kud.

Na gaya wa Carmen cewa ba ni da kuzari da ƙarfin zuciyar taimakawa a ƙasar Haiti. Ta tuna mini cewa mun yi aiki sosai tare kuma za mu iya taimaka wa juna. Saboda ƙarfafawar da na samu daga kalamanta, na kira Hedkwatan Shaidun Jehobah a Brooklyn, New York, kuma na tattauna da mutumin da ke tsara aikin agajin daga Amirka. Na ba shi sunana don ya daɗa shi ga jerin sunayen ’yan agajin. Na ambata sunan Carmen kuma na ce zan so mu yi aiki tare. Ya gaya mini cewa babu wani tabbaci cewa za a kira ni ko ita ko mu yi aiki tare.

Na ci gaba da yin ayyukana na yau da kullum, ina zaton cewa ba za a gayyace ni ba. Bayan kwana huɗu, a ranar Litinin 25 ga watan, na samu kira daga Brooklyn kuma suka tambaye ni ko zan iya zuwa ƙasar Haiti, idan zai yiwu wan shekare! Na ɗauka mafarki nake yi. Na yarda cewa zan yi iya ƙoƙarina. Da farko, ina bukatar ɗaukan hutu daga aikina. Bayan haka, na tuntuɓi Carmen, sai kwaram ta gaya mini cewa ba a gayyace ta ba domin ba ta iya yaren Faransanci ba. Na cika da ɗoki har da tsoro. A ranar 28 ga Janairu, bayan na samu takardar shiga jirgin sama, na tashi daga New York zuwa Santo Domingo, a Jamhuriyar Dominican, wadda ke da iyaka da ƙasar Haiti.

Wani Mashaidi matashi ya same ni a filin jirgin sama kuma ya ja ni a mota zuwa ofishin reshe na Shaidun Jehobah da ke Jamhuriyar Dominican. A wannan ranar, wasu nas guda biyu mata sun iso daga ƙasar Amirka, kuma muka kwana a ɗaki ɗaya a wannan daren. Washegari da safe, an ɗauke mu da mota zuwa ofishin reshen Haiti a Port-au-Prince, wadda tafiya ce ta awa bakwai da rabi.

Bayan da muka tsalleke iyakar ƙasar zuwa Haiti, mun ga irin ɓarnar da ya faru. Ba ƙaramin mamaki muka yi ba sa’ad da muka ga abin da girgizar ƙasa na daƙiƙa 35 ta yi wa wannan ƙasa mai kyau. Kallon ɓarnar a cikin talabijin ya yi mini wuya; ba zan iya kwatanta yadda na ji ba sa’ad da na ga ɓarnar ido da ido. Gidaje masu yawa, har da fadar shugaban ƙasa duk sun lalace, yayin da sauran suka zama kango. Yawancin gidajen nan na mutane ne da suka yi aiki tuƙuru a dukan rayuwarsu don su gina su, amma duk sun rushe a cikin ’yan daƙiƙa kaɗan. Hakan ya sa na ci gaba da yin tunani a kan cewa ba dukiya ba ce abubuwa mafi muhimmanci a rayuwa ba.

Sa’ad da muka isa ofishin reshen, mai karɓan baƙi ta hango mu muna tafe sai ta rugo daga inda take zaune muka haɗu a bakin ƙofa, ta rungume mu tana cike da murmushi. Ta yi godiya saboda ƙyale ayyukanmu da muka yi kuma muka zo wurinsu. Bayan mun ci abincin rana, sai muka tafi Majami’ar Taro da ke kusa, wanda aka mai da asibiti. A nan ne na haɗu da Shaidu da suka ba da kansu da son rai don su zo ƙasar, har da wasu ma’aurata daga Jamus waɗanda likitoci ne, tare da mataimakinsu, da kuma wata ungozoma daga ƙasar Switzerland.

Na soma aiki ne a daren ranar. Akwai majiyyata 18, Shaidu da waɗanda ba Shaidu ba, suna kwance a kan katifu a ƙasan Majami’ar Taron. Kowanne majiyyaci ya samu kulawa daidai kamar sauran kuma kyauta daga Shaidu waɗanda ma’aikatan asibiti ne.

A wannan daren, wani majiyyaci ɗan shekara 80 ya rasu. Matarsa tana gefensa, tare da ni da abokiyar ɗakina. Bayan haka, wata mata matashiya mai suna Ketly ta soma kuka saboda raɗaɗi. An yanke kafaɗarta na dama saboda raunukan da ta samu daga girgizar ƙasar. A gefenta akwai wata Mashaidiya wadda ke koya wa Ketly Littafi Mai Tsarki. Tana kwanciya a gefen gadon Ketly a Majami’ar Taro a kusan kowane dare.

Na je wajen Ketly, da fatan cewa zan rage raɗaɗin da take ji, amma zafin ba na zahiri ba ne ba kawai. Ta gaya mini cewa tana gidan ƙawarta ne sa’ad da girgizar ƙasar ta auku. Duk sun ruɗe ba su san abin da ke faruwa ba. Sun soma gudu ke nan kafaɗa da kafaɗa zuwa barandā, sa’ad da wani bango ya faɗa kansu kuma ya danne su. Ta kira ƙawarta, amma ba ta amsa ba. Ta ce nan da nan ta san cewa ƙawarta ta mutu. Jikin ƙawarta yana kwance a kan Ketly har sa’ad da masu aikin ceto suka zo bayan awa huɗu. Ketly ta rasa hannunta na dama har zuwa kafaɗa.

A dare na na farko a wajen, Ketly tana ta ambata abin da ya faru a duk lokacin da ta yi ƙoƙarin yin barci. Cike da kuka da shassheƙa, ta gaya mini: “Na san abin da Nassosi suka ce game da ranaku na ƙarshe da kuma girgizar ƙasa. Na san cewa muna da bege mai kyau a nan gaba. Na san cewa ya kamata in gode wa Allah cewa ina da rai. Amma ki yi tunanin irin yanayin da nake ciki yanzu. A ce komi yana tafiya daidai a rayuwarki, sai ba zato ba tsammani kika samu kanki a cikin wannan yanayin.” Na rasa abin da zan ce, na riƙe ta, sai muka soma kuka tare. Mun ci gaba da kukan har sai da barci ya ɗauke ta.

A kullum, ana aika likita guda da nas guda biyu su taimaka wa waɗanda suke bukatar jinya. An tura ni Petit Goave, wadda tafiya ce ta kusan awa biyu daga Port-au-Prince. Na tafi tare da masu aikin agaji guda biyu da suka ba da kansu da son rai, wata nas daga ƙasar Florida da kuma wani likita daga ƙasar Faransa. Mun isa ƙarfe 9:30 na safe, muka sauƙe kayanmu, kuma muka shigar da su cikin Majami’ar Mulkin yankin. An gaya wa mutane cewa muna tafe, saboda haka duk suna zaune suna jiran isowarmu.

Nan da nan muka kama aiki. Akwai zafi, kuma layin masu bukatar jinya sai ƙara tsawo yake yi. Sai wajen ƙarfe uku na rana ne muka tafi shan iska. Mu ukun mun yi wa mutane 114 rigakafi kuma mun duba mutane 105. Duk na bi na gaji amma ina farin cikin cewa mun kula da lafiyar mabukata.

Gabaki ɗaya na yi fiye da sati biyu a wannan aikin agajin a ƙasar Haiti. Kusan kowane dare, ina yin aikin awa 12 a Majami’ar Taron. Aiki ne mai girma, wanda ban taɓa yin irin sa ba a dā. Duk da haka, kasancewa ta a wajen gata ne a gare ni da kuma albarka. Na yi farin ciki sosai cewa na ɗan ƙarfafa mutanen ƙasar Haiti kuma na kawo musu sauƙi, domin sun sha wahala sosai.

Akwai abubuwa da yawa da za mu iya koya a wajen su. Alal misali, ɗaya daga cikin masu jinya da na kula da shi mai suna Eliser, ɗan shekara 15, an yanke ɗaya daga cikin ƙafafunsa. Na lura cewa yana adana abincinsa don shi da Jimmy da ke kwanciya a wajen sa su ci abincin tare. Ya bayyana mini cewa Jimmy ba ya yawan samun abinci kafin ya zo da yamma. Misalin Eliser ya koya mini cewa ba sai muna da arziki ko lafiya ba, kafin mu raba abin da muke da shi da wasu.

Irin wannan halin ya bayyana a tsakanin masu aikin agajin da muke aiki tare. Akwai wata ’yar aikin agajin da ba ta jin daɗi; wata kuma tana da ciwon baya. Duk da haka, mun saka bukatun majiyyatan a gaban na mu jin daɗin. Hakan ya ba ni ƙarfafawar da nake bukata don ci gaba da aikin. Duk muna gajiya a zahiri, a tunaninmu, da kuma motsin zuciyarmu daga loto-loto, amma mun taimaka wa juna kuma mun ci gaba da aikin. Wannan wani abu ne da ba zan taɓa mancewa ba! Ina godiya sosai don kasancewa cikin ƙungiyar Kiristoci masu kula, masu nuna ƙauna, da sadaukar da kai.

Kafin na bar ƙasar Haiti, biyu daga cikin masu jinyar da aka yanke hannuwansu na dama sun lallaɓa sun rubuta mini wasiƙun godiya kuma sun nace cewa kada in karanta har sai na shiga jirgin sama. Abin da na yi ke nan. Wasiƙun sun taɓa zuciyata, har na kasa daina yin kuka.

Tun da na dawo gida, ina tuntuɓar wasu daga cikin sababbin abokan da na haɗu da su a ƙasar Haiti. Ana kafa da kuma gwada abota mai ƙarfi ne a lokutan wahala da bala’i. Ina da tabbacin cewa abotan da muka ƙulla, za ta jimre duk wata irin wahala a nan gaba. A gare ni, gata ne mai girma.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba