Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w11 4/1 pp. 8-9
  • Mene Ne “Ƙarshen”?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Mene Ne “Ƙarshen”?
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
  • Makamantan Littattafai
  • Za A Hallaka Duniyar Nan Ne?
    Amsoshin Tambayoyi Daga Littafi Mai Tsarki
  • Ya Kamata Ka Ji Tsoron Ƙarshen Duniya?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2013
  • Shin Wannan Duniyar Za Ta Kare?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Wa’azi)—2021
  • Mene ne Ra’ayinka Game da “Karshen” Duniya?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2015
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
w11 4/1 pp. 8-9

Mene Ne “Ƙarshen”?

“. . . sa’an nan kuma sai ƙarshen ya zo.”—MATTA 24:14, Littafi Mai Tsarki.

A KWANAN nan, yin magana game da ƙarshen duniya ya zama ruwan dare. Littattafai, siliman, da jaridu na ban dariya da kuma na kimiya, suna nuna yadda ƙarshen duniya za ta zo a fasaloli dabam-dabam. Hakan ya haɗa da yin yaƙi da makaman nukuliya, da kuma karon da duwatsun da suke kewaye rana za su yi kuma su faɗo duniya, ƙwayoyin muguwar cuta, har da canjin yanayi da aka kasa sarrafawa.

Ra’ayoyin addinai ma sun bambanta; addinai da yawa suna koyar da cewa “ƙarshen” zai halaka dukan wani abu mai rai a duniya. Sa’ad da yake furuci game da Matta 24:14, wani ɗan tauhidi ya rubuta waɗannan kalmomi masu ban tsoro: “Wannan ayar tana ɗaya daga cikin ayoyi mafi muhimmanci a cikin dukan Kalmar Allah . . . Tsaranmu yana fuskantar halaka mai girma kuma mutane da yawa sun kasa hangar wannan mummunar halakar da ke tafe.”

Irin waɗannan ra’ayoyin sun yi watsi da wata gaskiya mai muhimmanci: Jehobah Allah ya “kafa” duniya; ya “halicce ta ba wofi ba, [amma] ya kamanta ta domin wurin zama.” (Ishaya 45:18) Saboda haka, sa’ad da Yesu ya yi maganar “ƙarshen,” ba ya nufin cewa za a halaka duniya, ko kuma za a share ’yan Adam gabaki ɗaya daga doron duniya ba. Abin da yake nufi shi ne, za a halaka miyagu, waɗanda suka ƙi yin rayuwar da ta jitu da ja-gora mai kyau na Jehobah.

Ka yi la’akari da wannan misalin. A ce kana da gida mai kyau kuma ka yarda mutane su zauna a cikinsa kyauta. Wasu daga cikin mazauna gidan suna zaune lafiya da juna kuma suna kula da gidanka sosai. Amma, sauran fitinannu ne, suna faɗa da juna, kuma suna zagin sauran mazauna gidan da suke da hali mai kyau. Sun lalata dukiyarka kuma sun yi kunnen uwar shegu ga duk ƙoƙarce-ƙoƙarcen da ka yi na hana su yin hakan.

Mene ne za ka yi don ka magance wannan matsalar? Za ka rushe gidanka ne? Da ƙyar. Wataƙila abin da za ka yi shi ne, za ka kori fitinannun da ke zaune a gidanka kuma ka gyara ɓarnar da suka yi.

Abin da Jehobah zai yi ke nan. Ya hure mai zabura ya rubuta: “Za a datse masu-aika mugunta: amma waɗanda ke sauraro ga Ubangiji, su ne za su gāji duniya. Gama in an jima kaɗan, sa’annan mai-mugunta ba shi: Hakika, da anniya za ka duba wurin zamansa, ba kuwa za ya kasance ba. Amma masu-tawali’u za su gāji ƙasan; za su faranta zuciyarsu kuma cikin yalwar salama.”—Zabura 37:9-11.

Manzo Bulus ma ya yi magana game da wannan batun. An hure shi ya rubuta: “Akwai sammai tun dā, da duniya kuma a tattare daga bisa ruwa, cikin tsakiyar ruwa kuma, bisa ga maganar Allah; bisa ga wannan fa duniya wanda take a sa’an nan, yayin da ruwa ya sha kanta, ta halaka.” (2 Bitrus 3:5, 6) A nan manzon yana magana ne game da Rigyawar zamanin Nuhu. Miyagun mutane ne aka halaka, amma ba a halaka duniya ba. Wannan Rigyawar da ta faru a dukan duniya “ishara [ce] ga marasa bin Allah.”—2 Bitrus 2:6, LMT.

Sai Bitrus ya daɗa cewa: ‘Sama da ƙasa da ke nan yanzu, an tanada su ga wuta.’ Idan muka tsaya a nan, muna iya kasancewa da masaniyar da ba daidai ba. Za ka lura cewa ayar ta ci gaba da cewa: “Za a yi wa marasa bin Allah . . . hallaka.” Halakar ba ta duniya ba ce amma ta marasa bin Allah. Me zai bi bayan haka? Bitrus ya rubuta: “Amma bisa ga alkawarinsa muna jiran sababbin sammai [Mulkin Allah ta hanyar Almasihu] da sabuwar ƙasa [al’ummar ’yan Adam masu aminci], inda adalci zai yi zamansa.”—2 Bitrus 3:7, 13, LMT.

Annabcin da ke cikin Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa lokacin “ƙarshen” ya kusa. Ka karanta Matta 24:3-14 da 2 Timotawus 3:1-5 domin ka ga abubuwan da suka tabbatar da hakan.a

Kana tunanin cewa bahagon abu ne a ce akwai rashin fahimta sosai game da Matta 24:14, ayar da ko yaro ma zai iya ganewa? Akwai dalilan da suka jawo hakan. Shaiɗan ya makantar da mutane don kada su ga gaskiya masu tamani da ke cikin Kalmar Allah. (2 Korintiyawa 4:4) Allah ya ɓoye nufe-nufensa daga mutane masu girman kai kuma ya bayyana su ga masu tawali’u. Game da wannan batun, Yesu ya ce: “Ina yabonka, ya Uba, Ubangijin sama da ƙasa, da ka ɓoye ma masu-hikima da masu-fahimi waɗannan al’amura, ka bayyana su ga jarirai.” (Matta 11:25) Gata ne mai girma mu kasance cikin masu tawali’un da suka fahimci ainihin ko mene ne Mulkin Allah, waɗanda suke ɗokin samun albarkar da Mulkin zai kawo ga dukan waɗanda suke goyon bayansa!

[Hasiya]

a Domin cikakken bayani, ka duba babi na 9 na littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa? Shaidun Jehobah ne suka wallafa shi.

[Hoton da ke shafi na 9]

Mulkin zai kawo “ƙarshen” dukan mugunta a duniya

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba