Ka Koya Daga Kalmar Allah
Littafi Mai Tsarki Ya Annabta Abubuwan da Za Su Faru a Nan Gaba Ne?
Wannan talifin ya tattauna tambayoyin da wataƙila ka taɓa yin tunani a kansu kuma ya nuna inda za ka iya samun amsoshinsu a cikin naka Littafi Mai Tsarki. Shaidun Jehobah za su yi farin cikin tattauna waɗannan amsoshin da kai.
1. Annabcin da ke Littafi Mai Tsarki takamaimai ne?
Allah Mai Iko Duka ne kaɗai zai iya sanin ainihin abin da zai faru a gaba. (Amos 3:7) Alal misali, tun da daɗewa ya annabta zuwan wanda ake kira Almasihu, ko Kristi. Almasihu zai fito ne daga zuriyar mutumin nan mai aminci Ibrahim. Zai zama sarkin da zai sa ’yan Adam masu biyayya su sake samun kamiltacciyar rayuwa kuma rashin lafiya za ta zama labari. (Farawa 22:18; Ishaya 53:4, 5) Wannan Wanda aka yi alkawarinsa zai fito ne daga Bai’talami.—Karanta Mikah 5:2.
Yesu ne wannan Almasihun. Fiye da shekara ɗari bakwai kafin haihuwarsa, Littafi Mai Tsarki ya annabta cewa budurwa ce za ta haifi Almasihu kuma za a wulaƙanta shi. Zai ba da ransa domin zunuban jama’a, kuma za a binne shi tare da mawadata. (Ishaya 7:14; 53:3, 9, 12) Fiye da ƙarnuka biyar kafin lokacin, Littafi Mai Tsarki ya ƙara annabta cewa zai shiga cikin Urushalima a kan jaki kuma za a ci amanarsa a kan azurfa 30. Kuma dukan abubuwan nan sun faru dalla-dalla kamar yadda aka annabta.—Karanta Zakariya 9:9; 11:12.
2. Allah yana annabta daidai lokacin da wani abu zai faru ne?
Fiye da ƙarnuka biyar kafin lokacin, Littafi Mai Tsarki ya annabta ainihin shekarar da Almasihu zai bayyana. An lissafa tsawon lokacin da zai shige kafin bayyanuwarsa a makonni na alama da suke nufin “makonnin shekaru” inda kwana ɗaya take wakiltar shekara ɗaya. Saboda haka, kowane “mako” yana nufin shekara bakwai. Wato, makonni 7 a tara da makonni 62, waɗanda za su ba da makonni 69 na shekaru. Adadin gaba ɗaya zai ba ka shekara 483. Daga wane lokaci aka soma ƙirga waɗannan shekarun? In ji Littafi Mai Tsarki, lokacin ya soma ne sa’ad da bawan Allah Nehemiya ya je Urushalima kuma ya soma sake gina birnin. Tarihin Farisa ya nuna cewa hakan ya faru a shekara ta 455 K.Z. (Nehemiya 2:1-5) Yesu ya yi baftisma a matsayin Almasihu shekaru 483 bayan haka, a shekara ta 29 A.Z., a kan kari.—Karanta Daniyel 9:25.
3. Annabcin da ke cikin Littafi Mai Tsarki suna cika kuwa a yau?
Yesu ya annabta abubuwa masu muhimmanci da za su faru a zamaninmu. A annabcinsa, ya ambata bisharar Mulkin Allah, wadda za ta kawo sauƙi ga dukan mutanen da suke ƙaunar Allah a faɗin duniya. Mulkin zai kawo ƙarshen mugun yanayin da duniya take ciki a yau.—Karanta Matta 24:14, 21, 22.
Annabcin da ke cikin Littafi Mai Tsarki sun kwatanta abubuwan da ke nuna cewa ƙarshen yanayin da duniya take ciki a yau ya kusa. Akasin abubuwa da mutane suke tsammanin za su faru a wannan zamani da aka sami ci gaba, Littafi Mai Tsarki ya bayyana cewa mutane za su riƙa ɓata duniya. Matsalolin da yaƙe-yaƙe, ƙarancin abinci, girgizar ƙasa da kuma annoba suke jawowa za su zama aukuwa na yau da kullum. (Luka 21:11; Ru’ya ta Yohanna 11:18) Mutane ba za su riƙa rayuwa bisa ɗabi’u masu kyau ba. A wannan lokaci mai wuya, mabiyan Yesu za su yi wa’azin bisharar Mulkin Allah ga dukan al’ummai.—Karanta Matta 24:3, 7, 8; 2 Timotawus 3:1-5.
4. Yaya rayuwar ’yan Adam za ta kasance a nan gaba?
Akwai abubuwa masu kyau da Allah Mai Iko Duka ya riga ya shirya domin mutane masu aminci. Yesu Kristi, Almasihu, tare da mutane 144,000 da aka zaɓo daga duniya, za su yi sarauta daga sama bisa duniya. Wannan Mulkin zai yi sarauta na shekara dubu ɗaya. Za a ta da matattu kuma za a ba su zarafi su nuna ko sun cancanci yin rayuwa har abada. Bugu da ƙari, Mulkin zai warkar da duk waɗanda suke raye a lokacin. Rashin lafiya da mutuwa ba za su ƙara kasancewa ba.—Karanta Ru’ya ta Yohanna 5:10; 20:6, 12; 21:4, 5.
Don ƙarin bayani, ka duba shafuffuka na 23-25 da 197-201 a littafin da aka nuna hotonsa a nan, Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?