Don Matasa
Ka Kiyayi Yin Hulɗa da Aljanu!
Umurni: Ka yi wannan aikin a inda babu surutu. Sa’ad da kake karanta nassin, ka sa kanka cikin yanayin. Ka yi tunanin yanayin a zuciyarka. Ka ji muryoyin mutanen. Ka ji yadda ainihin mutanen da ke ciki suka ji. Ka sa labarin ya kasance kamar yanzu yake faruwa.
1 KA YI TUNANI A KAN YANAYIN NAN.—KARANTA FARAWA 6:1-6 DA AYYUKAN MANZANNI 19:11-20.
Ka kwatanta kamannin mutanen nan, Nephilim.
․․․․․
Kamar yadda aka kwatanta a Ayyukan Manzanni 19:13-16, yaya kake ganin waɗannan mutanen suka ji bayan sun gamu da aljani?
․․․․․
2 KA BINCIKA SOSAI.
Ka yi amfani da littattafan bincike da kake da su don samun ƙarin bayani game da Nephilim. A ganin ka, me ya sa suke da rashin imani?
․․․․․
Ta yaya aljanu “suka rabu da nasu wurin zama”? (Karanta Yahuda 6.) Me ya sa auren mata da aljanun suka yi mugun abu ne?
․․․․․
Mene ne labaran nan biyu suka nuna maka game da jarabar da aljanu suke da ita na yin jima’ai da kuma mugunta?
․․․․․
3 KA YI AMFANI DA ABIN DA KA KOYA. KA RUBUTA ABIN DA KA KOYA GAME DA . . .
Yadda aljanu suke nuna mugunta da son kai.
․․․․․
DON ƘARIN AMFANI.
Tun da aljanu ba za su sake iya zama mutane ba, ta yaya za su iya rinjayar ka a hanyar da ba za ka gane da sauri ba?
․․․․․
Waɗanne irin wasanni ne a yau suke ɗaukaka sha’awoyin aljanu?
․․․․․
Ta yaya za ka nuna cewa ba za ka yarda aljanu su yi tasiri a kanka ba? (Sake karanta Ayyukan Manzanni 19:18, 19.)
․․․․․
4 WANE ƁANGAREN WAƊANNAN LABARAN NE YA FI MA’ANA A GARE KA, KUMA ME YA SA?
․․․․․
Ka ƙara koya game da Littafi Mai Tsarki, a duniyar gizon www.watchtower.org da www.pr418.com