Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w12 5/15 pp. 31-32
  • “Ina Daɗa Sha’awar Hidimar Majagaba Kowace Rana”

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • “Ina Daɗa Sha’awar Hidimar Majagaba Kowace Rana”
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
w12 5/15 pp. 31-32

Daga Tarihinmu

“Ina Daɗa Sha’awar Hidimar Majagaba Kowace Rana”

A SHEKARA ta 1886, mun tura kofi ɗari na littafin nan Millennial Dawn, Littafi na 1, daga Bible House da ke garin Allegheny, Pennsylvania, Amirka, zuwa birnin Chicago a Illinois. Charles Taze Russell yana son a rarraba wannan sabon littafin wa shagunan sayar da littattafai. Wani kamfani mafi girma a Amirka da ke rarraba littattafan addinai ya amince ya riƙa karɓa odar wannan littafin Millennial Dawn. Amma makonni biyu bayan wannan ranar, kamfanin ya mayar da littattafan zuwa Bible House.

Me ya sa aka mayar da wannan littattafan? Wani sanannen limami ya yi fushi don za a rarraba wannan littafin Millennial Dawn tare da littattafansa. Ya ce idan ba a mayar da littafin ba, shi da sauran limaman za su kwashe littattafansu, kuma su kai su wani wuri. Shi ya sa mai kamfanin ya mayar da littafin Millennial Dawn. Ƙari ga haka, an yi tallar wannan littafin a jaridu. Amma waɗannan maƙiya sun sa kamfanin jaridar ta daina yin wannan tallar. Ta yaya mutane masu son gaskiya za su samu wannan littafin?

Colporteurs sun yi aiki tuƙuru.a A shekara ta 1881, Zion’s Watch Tower [Hasumiyar Tsaro ta Sihiyona] ta yi kira ga masu wa’azi dubu ɗaya da za su iya hidima ta cikakken lokaci don su rarraba littafin. Ko da yake akwai majagaba wajen ɗari uku kawai a lokacin, amma sun rarraba wannan littafin a wurare da yawa. A shekara ta 1897, majagaban sun rarraba kusan kofi miliyan ɗaya na wannan littafin Millennial Dawn. Yawancinsu suna kula da kansu da ɗan tallafin kuɗin da suke samu daga kowanne Hasumiyar Tsaro da littafin da suka rarraba.

Su wane ne waɗannan majagaba masu gaba gaɗi? Wasu sun soma wannan hidimar sa’ad da ba su kai shekara ashirin ba, wasu kuma sa’ad da suka manyanta. Da yawa a cikinsu marasa aure ne ko kuma ma’aurata da ba su da yara, iyalai da dama sun soma hidimar majagaba. Majagaba na kullum suna yini a hidima kuma majagaba na ɗan lokaci suna ba da sa’a ɗaya ko sa’o’i biyu a yini. Ba kowa ba ne yake da koshin lafiyar yin aikin majagaba ba. Amma, a taron gunduma da aka yi a shekara ta 1906, an gaya wa maniyyata cewa ba sa bukata su zama “masu ilimi sosai, ko kuma masu baiwa.”

A kusan kowane nahiya, mutane marasa ilimi ne suka cim ma abubuwa da suka wuce misali a aikin majagaba. Wani ɗan’uwa ya ce ya rarraba kimanin littattafai guda 15,000. “Ban shiga aikin majagaba don in zama mai sayar da littattafai ba, amma don in yi wa Jehobah da kuma gaskiya shaida,” in ji ɗan’uwan. A duk inda majagaba suka je, gaskiya tana yaɗuwa kuma ɗaliban Littafi Mai Tsarki suna ƙaruwa.

Limaman Kiristendam suna yi wa majagaba ba’a, suna kiransu masu sayar da littattafai. Hasumiyar Tsaro ta shekara ta 1892 ta ce: “Mutanen kalilan ne suka san su a matsayin wakilan Ubangiji ko kuma suka daraja su kamar yadda Ubangiji yake yi don tawali’u da kuma sadaukarwar da suka yi.” Hakika rayuwar majagaba ba cin tuwo ba ce, kamar yadda ɗaya daga cikinsu ya faɗa. Takalma masu ƙwari da kekuna su ne abokan tafiyarsu na musamman. Inda babu kuɗi, sai majagaban su yi musanyar littattafai da abinci. Bayan sun yini suna wa’azi, suna gajiya amma da farin ciki sai su koma tanti da ɗakunan haya da suke kwana a ciki. Kuma suna da ɗaki mai taya da ya rage musu kashe kuɗi sosai.b

Somawa daga Taron gundumar da aka yi a birnin Chicago a shekara ta 1893, aka fara wani sashen taro na musamman da majagaba. A wannan sashen, ana ba da labaran wa’azi masu daɗi, yadda za a yi wa’azi da kuma shawarwari masu amfani. Ɗan’uwa Russell ya taɓa ba waɗannan majagaba masu ƙwazo shawara cewa su riƙa cin abinci mai kyau da safe, madara da hantsi, kuma ƙanƙarar soda da rana.

Majagaban da suke neman abokan wa’azi sukan sanya igiya mai ruwan ɗorawa. Ana haɗa sabon majagaba da wanda ya ƙware. Yin wa’azi bibbiyu abu ne da ake bukata, domin wani sabon majagaban ya taɓa cewa, “ba ka son waɗannan littattafan ko?” Sa’ad da yake gabatar da littattafai. Abin farin ciki shi ne matar ta karɓi littattafan kuma daga baya ta zama Mashaidiya.

Wani ɗan’uwa ya taɓa yin wannan tunanin: ‘Shin in ci gaba da sana’ata mai kawo kuɗi, kuma in ba da gudummawar dala 1,000 don aikin wa’azi ne, ko kuma in zama majagaba?’ Ubangiji zai yi farin ciki idan ya cim ma ɗaya daga cikin maƙasudan nan, amma idan ya ba da lokacinsa don aikin wa’azi Ubangiji zai yi masa albarka sosai. Mary Hinds ta ɗauki wannan aikin majagaba a matsayin “hanya mafi inganci ta yi wa mutane da yawa alheri sosai.” Wata mai suna Alberta Crosby ta ce, “Ina daɗa sha’awar hidimar majagaba kowace rana.”

A yau, zuriyar waɗannan majagaban da kuma wasu ’yan’uwa masu ƙwazo suna bin misalin waɗannan majagaban na dā. Idan babu majagaba a cikin zuriyarku, zai dace ka yi ƙoƙarin kafa wannan al’ada. Idan ka yi hakan, sha’awar da kake da shi na aikin majagaba zai riƙa ƙaruwa kowace rana.

[Hasiya]

a An canja sunan nan “colporteur” zuwa “majagaba” a shekara ta 1931.

b Ƙarin bayani game da ɗakuna masu taya zai fito a wani talifi a nan gaba.

[Bayanin da ke shafi na 32]

Ba sa bukata su zama “masu ilimi sosai, ko kuma masu baiwa”

[Hoto a shafi na 31]

Majagaba Alfred Winfred Osei a ƙasar Gana, a misalin shekara ta 1930

[Hotona a shafi na 32]

Sama: Majagaba Edith Keen da Gertrude Morris a ƙasar Ingila, a misalin shekara ta 1918; ƙasa: Stanley Cossaboom da Henry Nonkes a Amurka, da fankon kwalaye na littattafan da suka rarraba

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba