KA KUSACI ALLAH
Jehobah “Ba Mai-Tara Ba Ne”
Shin, an taɓa nuna maka wariya? An taɓa ƙin jin roƙonka ko ƙi ba ka wani abu ko kuma yi maka wulaƙanci don launin fatarka ko ƙabilarka ko kuma matsayinka? Idan haka ne, ba kai kaɗai ba ne ka taɓa fuskantar irin wannan yanayin. Amma ga albishiri: Ko da yake, irin wannan wulaƙanci ya zama ruwan dare a duniya, Allah ba ya nuna bambanci. Manzo Bitrus ya tabbatar da hakan kuma ya ce: “Allah ba mai-tara ba ne.”—Ka karanta Ayyukan Manzanni 10:34, 35.
Bitrus ya yi wannan furucin ne a wani yanayi mai ban mamaki, wato, a gidan wani mutumin Al’umma mai suna Karniliyus. Bitrus asalin Bayahude ne kuma a lokacin Yahudawa suna ganin cewa yin sha’ani da mutanen Al’ummai haramun ne. To, idan haka ne, me ya kai Bitrus gidan Karniliyus? A taƙaice, Allah ne ya umurce shi ya je. A wani wahayi da Bitrus ya gani, Allah ya gaya masa: “Abin da Allah ya tsarkake, kada kai ka maishe shi haram.” Bitrus bai san cewa kafin ranar, Allah ya umurci Karniliyus a cikin wani wahayi cewa ya aika a kira shi ba. (Ayyukan Manzanni 10:1-15) Sa’ad da Bitrus ya fahimci cewa abin da ke faruwa nufin Allah ne, sai ya yi furucin da ke gaba.
Bitrus ya ce: “Hakika na gane Allah ba mai-tara ba ne.” (Ayyukan Manzanni 10:34) Game da wannan kalmar Helenanci da aka fassara zuwa “tara,” wani masani ya ce: “Yana nuni ne ga alƙali da yake yanke hukunci bisa ga girman mutum, amma ba bisa ga laifin da ya yi ba.” Allah ba ya ɗaukan mutum da muhimmanci fiye da ɗan’uwansa saboda bambancin launin fata ko ƙasa ko matsayi ko kuma wani dalili dabam.
A maimakon haka, yana ganin abin da yake zuciyarmu. (1 Sama’ila 16:7; Misalai 21:2) Bitrus ya ci gaba da cewa: “A cikin kowace al’umma, wanda yake tsoronsa, yana aika adalci kuma, abin karɓa ne gare shi.” (Ayyukan Manzanni 10:35) Tsoron Allah yana nufin ba wa Allah girma da daraja, dogara da shi da kuma gudun aikata duk wani abin da zai ɓata masa rai. Aikata adalci yana nufin yin abin da ya dace a gaban Allah. Jehobah yana jin daɗin mutumin da yake yin abin da ya dace don yana tsoron Allah.—Kubawar Shari’a 10:12, 13.
Sa’ad da Jehobah ya kalli mutane daga sama, al’umma ɗaya kawai yake gani, wato, al’ummar ’yan Adam
Idan an taɓa nuna maka wariya da bambanci, za ka sami ƙarfafa daga abin da Bitrus ya faɗa game da Allah. Jehobah yana jan mutane daga dukan al’ummai zuwa cikin bauta ta gaskiya. (Yohanna 6:44; Ayyukan Manzanni 17:26, 27) Yana jin addu’o’in masu bauta masa, ko da farar fata ko baƙar fata ne, ko da daga wace ƙasa ce ya fito, ko da talaka ne ko mai kuɗi. (1 Sarakuna 8:41-43) Za mu iya kasancewa da tabbaci cewa sa’ad da Jehobah ya kalli mutane daga sama, al’umma ɗaya kawai yake gani, wato, al’ummar ’yan Adam. Babu shakka, za ka so ka kara koyo game da Jehobah, Allahn da ba ya tara, ko ba haka ba?
Karatun Littafi Mai Tsarki na watan Agusta: Romawa 1-16