DAGA TARIHINMU
Sarkin Ya Yi Farin Ciki Sosai!
WANNAN labarin ya faru a fādar Sarkin Suwazilan, a watan Agusta na shekara ta 1936. ’Yan’uwa Robert da George Nisbet sun saka waƙa da kuma jawabin Ɗan’uwa Joseph Rutherford a mota mai lasifika. Bayan Sarki Sobhuza na biyu ya gama saurarawa, sai ya yi farin ciki sosai. Ɗan’uwa George ya ce: “Abin taƙaici, sarkin ya ce yana son ya sayi na’urar da fayafayan da kuma lasifika da muke amfani da su don yaɗa bishara.”
Sai ɗan’uwa Robert ya roƙe shi kuma ya gaya masa cewa waɗannan abubuwan ba na sayarwa ba ne, domin na wani mutum ne. Sarkin ya so ya san wannan mutumin.
Ɗan’uwa Robert ya ce masa: “Dukan na’urorin na wani Sarki ne.” Sai Sobhuza ya yi tambaya ko wane ne wannan Sarkin, kuma Robert ya ce masa: “Yesu Kristi ne kuma shi ne Sarkin Mulkin Allah.”
Sarki Sobhuza ya amsa cewa: “Ah, shi babban Sarki ne. Ba na son in karɓi duk abin da ke nasa.”
Robert ya ce: ‘Halin Babban Sarki Sobhuza ya burge ni sosai. Ya iya Turanci sosai, amma ba ya fahariya. Yana da kirki da fara’a, kuma yana faɗin gaskiya.’ Na yi minti 45 a ofishinsa, yayin da George ya saka waƙoƙin ƙungiyar Jehobah a waje.
Robert ya ci gaba da cewa: ‘Da yamma, sai muka ziyarci makarantar da ake kira Swazi National School. Abubuwa masu kayatarwa sun faru a nan. Mun yi wa shugaban makarantar wa’azi, kuma ya saurara sosai. Ya yi farin ciki sosai sa’ad da muka gaya masa cewa mun kawo wata na’urar sauti da muke so mu saka, kuma ya sa ɗaliban suka zauna a ciyawa don su saurara. An gaya mana cewa a makarantar, maza suna koyon noma da kafinta da gini da Turanci da kuma lissafi. Mata kuma suna koyon aikin nas da aikace-aikacen gida da kuma wasu sana’o’i masu amfani.’ Kakar Sarkin ne ta gina makarantar.
A shekara ta 1933, Sarki Sobhuza ya saurari majagaba da suka kai masa ziyara a fādarsa. A wani lokaci ma, ya tattara matsaransa guda ɗari don su saurari saƙon Mulki da aka saka a sauti. Yakan yi odar mujallunmu, kuma yakan karɓi littattafanmu. Kafin a ce kwabo, Sarkin ya buɗe laburare na littattafanmu. Duk da cewa gwamnatin Turai ta hana rarraba littattafanmu a lokacin yaƙin duniya na biyu, Sarkin ya adana littattafan da suke cikin laburaren.
Sarki Sobhuza na biyu ya ci gaba da karɓar Shaidu a fādarsa da ke garin Lobamba, kuma yakan gayyaci limamai su zo su saurari jawabai daga Littafi Mai Tsarki. Sa’ad da ɗan’uwa Helvie Mashazi yake tattauna littafin Matta sura 23, sai rukunin limamai suka fusata kuma suka tilasta masa ya zauna. Amma, Sarkin bai yarda ba, kuma ya ce wa ɗan’uwa Mashazi ya ci gaba. Ban da haka ma, sarkin ya umurci masu sauraro su rubuta dukan nassosin da aka ambata a jawabin.
Bayan wani jawabin da wani majagaba ya ba da, sai wasu limamai huɗu da suke wurin suka ce: “Daga yanzu, mu ba limamai ba ne, amma mu Shaidun Jehobah ne.” Suka tambayi majagaban ko yana da irin littattafan da aka ba Babban Sarkin.
Daga tsakanin shekara ta 1930 zuwa sa’ad da ya mutu a shekara ta 1982, wannan babban sarkin ya ci gaba da daraja Shaidun Jehobah kuma bai ƙyale a tsananta musu don sun ƙi yin bukukuwan ƙasar da suka saɓa wa ƙa’idodin Allah ba. Saboda haka, Shaidu sun yi farin ciki sosai don abubuwan da ya yi, kuma sun yi baƙin ciki ainun sa’ad da ya rasu.
A farkon shekara ta 2013, akwai masu shela fiye da 3,000 a ƙasar Suwazilan. Akwai mutane fiye da miliyan ɗaya a ƙasar, kuma kowane mai shela yana da mutane 384 da zai yi wa wa’azi. Majagaba fiye da 260 a ikilisiyoyi 90 suna yin wa’azi da ƙwazo kuma mutane 7,496 sun halarci taron Tunawa da Mutuwar Yesu a shekara ta 2012. Babu shakka, za a samu ƙaruwa a nan gaba. Hakika, an dasa iri mai kyau a lokacin da masu shela suka je ƙasar Suwazilan a tsakanin shekara ta 1930 zuwa 1939.—Daga tarihinmu a Afrika ta Kudu.