ABIN DA KE SHAFIN FARKO | WANE SAƘO NE KE LITTAFI MAI TSARKI?
“Mun Sami Almasihu”!
Shekaru wajen ɗari huɗu bayan da aka rubuta littafi na ƙarshe a cikin Nassosin Ibrananci, annabcin da Mikah ya yi game da Almasihu ya cika kuma aka haifi Yesu a Bai’talami. Wajen shekaru 30 bayan haka, wato a shekara ta 29 a zamaninmu, sashe na farko a cikin annabcin Daniyel game da zuwan Almasihun ya cika. An yi wa Yesu baftisma kuma Allah ya shafe shi da ruhu mai tsarki. Almasihun da aka daɗe ana jiransa, wanda shi ne Zuriyar ya iso a daidai lokacin da aka ce zai zo!
Nan da nan, Yesu ya soma yin wa’azi, yana “kawo bishara ta mulkin Allah.” (Luka 8:1) Yesu ya kasance mai alheri kuma ya damu da mutane sosai, daidai kamar yadda aka annabta. Ya koyar da mutane cikin ƙauna kuma a hanyar da za su gane, kuma ya warkar da mutane daga “kowane irin rashin lafiya.” Hakan ya nuna cewa Allah yana tare da shi. (Matta 4:23) Mutane manya da ƙanana da suka je wurin Yesu sun ga tabbaci cewa shi ne “Almasihu.”—Yohanna 1:41.
Yesu ya annabta cewa gab da lokacin da Mulkinsa zai mallaki duniyar nan gaba ɗaya, za a yi yaƙe-yaƙe da girgizar ƙasa kuma mutane za su sha wahala sosai. Ya umurce mu duka mu “yi tsaro.”—Markus 13:37.
Yesu kamiltaccen mutum ne da ya yi biyayya da Allah sa’ad da yake duniya, amma a ƙarshe magabtansa suka kashe shi. Mutuwarsa ta buɗe mana hanyar samun abin da Adamu da Hawwa’u suka rasa, wato begen yin rayuwa har abada a cikin Aljanna.
Mutuwar Yesu da kuma tashinsa daga matattu a matsayin mala’ika mai iko, kwana uku bayan ya mutu cikar annabci ne. Bayan haka, Yesu ya bayyana ga almajiransa sama da 500 a lokaci ɗaya. Kafin ya haura sama, Yesu ya umurci mabiyansa su yi shelar bishara game da shi da kuma Mulkinsa ga “dukan al’ummai.” (Matta 28:19) Sun yi wannan aikin iyakacin gwargwadonsu kuwa?
—Bisa ga abin da ke littafin Matta, Markus, Luka, Yohanna, 1 Korintiyawa.