LABARI
Yadda Na Mai da Hidimar Jehobah Aikina a Rayuwa
Bayan na sauke karatu daga makarantar sakandare a watan Janairu na shekara ta 1937, na shiga jami’ar Iowa State a yammacin Amirka, wato inda muke zama. Zuwa makaranta da kuma yin aiki don biyan kuɗin makarantata sun sa ban sami lokacin yin wani abu ban da waɗannan abubuwa biyu ba. Burina a rayuwa shi ne yin nazari a kan gine-gine masu tsawo da kuma gadajen sama.
Na riga na yi shekaru biyar a makarantar jami’a a lokacin da Amirka ta sa kai a Yaƙin Duniya na Biyu, wato a farkon shekara ta 1942. A lokacin, ’yan watanni ne kawai suka rage mini in sami digiri a matsayin injiniyan gine-gine. Ina zama da ’yan makaranta biyu a ɗakina. Ɗayansu ya shawarce ni in yi magana da wani mutum da yakan “ziyarci ’yan makaranta a ɗakuna da ke ƙasa da mu.” Da na je sai na haɗu da wani Mashaidin Jehobah mai suna John (Johnny) Brehmer. Na yi mamaki sosai da yadda yake amfani da Littafi Mai Tsarki don ya amsa duk wata tambaya da aka yi masa. Hakan ya sa na soma nazarin Littafi Mai Tsarki da Johnny a kai a kai kuma daga baya na soma fita wa’azi da shi a duk lokacin da na sami zarafi.
Mahaifin Johnny mai suna Otto ya zama Mashaidi a lokacin da shi ne shugaban bankin da ke birnin Walnut a Iowa. Otto ya yi murabus kuma ya soma hidima ta cikakken lokaci. Da shigewar lokaci, misalinsa da na iyalinsa ya ƙarfafa ni in tsai da wata shawara mai muhimmanci.
LOKACIN ƊAUKAN MATAKI
Wata rana, shugaban makarantar jami’armu ya gaya mini cewa ba za a bar ni in sauke karatu ba idan ban daɗa ƙoƙari ba. Hakan ya sa na roƙi Jehobah Allah da dukan zuciyata don ya ja-gorance ni a wannan batun. Bayan haka, wata rana wani farfesan injiniya da ya koyar da ni ya ce in zo in gan shi. Sai ya gaya mini cewa ana neman wani da ya ƙware a aikin injiniya kuma ya riga ya ce musu zan karɓi aikin ko da yake bai gaya mini ba. Na gode wa farfesan, amma na bayyana masa cewa ba zan karɓi aikin ba domin na ƙudura niyyar yi wa Jehobah hidima duk rayuwata. Na yi baftisma a ranar 17 ga Yuni a shekara ta 1942, kuma ba da daɗewa ba bayan haka, na soma hidimar majagaba, wato hidima ta cikakken lokaci da Shaidun Jehobah suke yi.
Kusan ƙarshen wannan shekarar, na sami wata wasiƙa kuma a cikin wasiƙar an bukaci in shiga soja. Sai na je gaban waɗanda suke ɗaukan mutane a soja kuma na bayyana musu dalilin da ya sa ba zan yi yaƙi ba. Na kuma ba su takardun shaida daga farfesa dabam-dabam da suka nuna cewa ina da halin kirki kuma na ƙware sosai a matsayin injiniyan gine-gine. Duk da wannan shaida mai kyau, an ci mini tarar kuɗi fiye da naira miliyan ɗaya da dubu ɗari biyar kuma aka tura ni kurkuku na shekara biyar a birnin Leavenworth, Kansas da ke Amirka.
RAYUWATA A KURKUKU
An tsare Shaidu matasa fiye da 230 a kurkukun noma wanda ke ƙarƙashin kurkuku ta ƙasa a Leavenworth. A wannan kurkukun, gandirobobi da dama suna tura mu aiki. Wasu cikinsu sun san cewa ba ruwanmu da yaƙi kuma suna daraja matsayinmu.
Wasu cikin gandirobobin sun yarda mu ci gaba da yin taro, inda muke tattauna Littafi Mai Tsarki. Sun kuma taimaka mana mu samu littattafai da suke bayyana Littafi Mai Tsarki a cikin kurkuku. Shugaban kurkukun ma ya aika a riƙa kawo masa mujallar da yanzu ake kira Awake!
YIN AIKIN MISHAN BAYAN AN SAKE NI
Bayan na yi shekara uku a kurkuku, an sake ni a ranar 16 ga Fabrairu, a shekara ta 1946, ’yan watanni kawai bayan an daina Yaƙin Duniya na Biyu. Nan da nan na sake soma hidima ta cikakken lokaci a matsayin majagaba. An tura ni hidima a wannan birnin Leavenworth da ke Kansas. Hakan ya tsoratar da ni sosai domin an tsani Shaidun Jehobah a wannan birnin. Samun aikin yi da kuma masauki ya yi mini wuya sosai.
Akwai ranar da nake wa’azi gida-gida, sai na tarar da wani gandiroba kuma ya ce mini, “Maza ka bar gidana!” Sa’ad da na ga sandan buga ƙwallon baseball da ke hannunsa, na tsorata kuma kafin a ce kwabo na bar wurin. A wani gida kuma, wata mata ta ce in ɗan jira ta tana zuwa, sai ta rufe kofar. Sa’ad da nake jira, sai kawai na ji an yi mini wanka da ruwan wanke-wanke daga tagar benen. Duk da haka, Allah ya albarkaci hidimata. Na sami labari daga baya cewa wasu cikin mutanen da suka karɓi littattafai da suke bayyana Littafi Mai Tsarki a hannuna sun zama Shaidun Jehobah.
A shekara ta 1943, an buɗe wata sabuwar makaranta da ake horar da ’yan mishan da ake kira Makarantar Littafi Mai Tsarki ta Gilead, a ƙasar New York. An gayyace ni zuwa aji na goma na makarantar kuma na sauke karatu a ranar 8 ga Fabrairu, 1948. Bayan haka, an tura ni hidima a ƙasar Gana.
A ƙasar Gana, aikina shi ne yin wa’azi ga ma’aikatan gwamnati da kuma Turawa. Sa’an nan a ƙarshen mako, nakan yi hidima tare da wata ikilisiyar Shaidun Jehobah kuma ina horar da ’yan’uwa a ikilisiyar a yin wa’azi gida-gida. Ƙari ga haka, nakan ziyarci Shaidun da ke wuraren da ba ikilisiyoyi don in horar da su a aikin wa’azi. Na kuma yi hidimar mai kula mai ziyara a ƙasar Kwaddebuwa da ke kusa.
Sa’ad da nake hidima a waɗannan yankunan, na koyi rayuwar mutanen Afirka. Alal misali na kwana a gidan laka, na ci abinci da hannu kuma na yi bayan gida a daji kamar yadda Isra’ilawa ke yi a dā. (Kubawar Shari’a 23:12-14) Yin waɗannan abubuwan ya sa ni da kuma ’yan’uwana ’yan mishan muka kasance da farin jini a gaban mutanen. Har ma muka soma nazarin Littafi Mai Tsarki da wasu cikin matan jami’an gwamnati. Saboda haka a lokacin da wasu ’yan hamayya suka karɓi izinin janye takardun bizanmu, wasu cikin waɗannan matan suka matsa wa mazajensu har sai da aka bar mana bizanmu.
Da sannu-sannu, na kamu da zazzabin cizon sauro, kamar yadda yake faruwa da yawancin ’yan mishan da suka zo Afirka. Hakan ya sa ni jiri sosai kuma jikina ya riƙa kakkaɗawa saboda sanyi. A wasu lokatai nakan riƙe bakina don ya daina kakkaɗawa. Duk da haka, na ci gaba da yin farin ciki da kuma samun gamsuwa a hidimata.
Na riƙa rubuta wasiƙu zuwa ga wata ’yar’uwa mai suna Eva Hallquist na tsawon shekaru huɗun da nake hidima a Afirka. Na haɗu da ita kafin in bar Amirka. Na sami labari cewa tana aji na 21 a Makarantar Littafi Mai Tsarki na Gilead kuma za ta sauke karatu a ranar 19 ga Yuli 1953, a taro na ƙasashe da Shaidun Jehobah za su yi a filin wasa da ke Yankee a Amirka. Na shirya da kyaftin na wani jirgin ruwa da zai je Amirka cewa zan bi shi kuma zan yi masa aiki a cikin jirgin a matsayin kuɗin tafiyata.
Bayan tafiyar kwana 22, wasu lokatai ma cikin guguwa, na isa Amirka kuma na wuce wurin Eva a hedkwatar Shaidun Jehobah a Brooklyn. Wata rana sa’ad da ni da Eva muke saman wani bene, sai muka yi alkawarin aure. Daga baya muka yi aure, sai Eva ta bi ni Gana kuma muka ci gaba da yin hidima tare.
KULA DA IYALINMU
Bayan da muka yi hidima na wasu shekaru tare da Eva a Afirka, sai na sami wasiƙa daga mahaifiyata. A cikin wasiƙar, ta gaya mini cewa mahaifina yana da ciwon Kansa kuma ciwon ya yi tsanani. Hakan ya sa aka ba mu hutu kuma muka koma Amirka. Rashin lafiyar ta yi tsanani, kuma ba da daɗewa ba mahaifina ya rasu.
Shekaru huɗu bayan dawowarmu Gana, muka sami labari cewa mahaifiyata tana rashin lafiya. Wasu abokanmu suka shawarta cewa mu koma gida don mu kula da ita. Ɗaukan wannan matakin bai kasance mana da sauƙi ba. Bayan na yi shekaru 15 a hidimar mishan, sai muka kwashi kayanmu, muka koma Amirka. A hakan, ni da matata mun yi shekaru 11 muna hidimar mishan tare.
Mun kula da mahaifiyata tare, kuma muka taimaka mata ta halarci taro a duk lokacin da hakan ya yiwu. A ranar 17 ga Janairu 1976 sa’ad da take ’yar shekara 86, sai ta rasu. Amma wani abin baƙin ciki sosai ya faru shekaru tara bayan haka. Matata Eva ta kamu da ciwon Kansa. Mun yi ta fama da cutar har ta rasu a ranar 4 ga Yuni 1985. A lokacin, shekarunta 70 ne.
CANJE-CANJE DA NA SHAIDA A HIDIMATA
A shekara ta 1988, a lokacin da za a keɓe sababbin gine-gine na ofishin reshe da ke Gana ga Jehobah, an gayyace ni, kuma na halarta. A wannan taron, na shaida abin da ba zan taɓa mantawa ba! Shaidu wajen 735 ne kawai suke Gana a lokacin da na zo wurin bayan na sauke karatu daga Gilead, wato shekaru 40 da suka gabata ke nan. Sun wuce 34,000 a shekara ta 1988, amma yanzu sun kusan 114,000!
Shekaru biyu bayan na ziyarci Gana, a ranar 6 ga Agusta 1990, na auri Betty Miller wata kawar matata Eva. Mun ci gaba da yi wa Jehobah hidima tare. Muna ɗokin ganin kakanninmu da iyayenmu da kuma Eva wata rana a cikin Aljanna bayan an ta da matattu.—Ayyukan Manzanni 24:15.
Nakan yi farin ciki sosai a duk lokacin da na yi tunanin yadda Jehobah ya yi amfani da ni a hidimarsa har tsawon shekaru fiye da 70 yanzu. Hakan babban gata ne a gare ni. Ina masa godiya a kowane lokaci don yadda ya taimaka mini in mai da hidimarsa aikina a rayuwa. Ko da yake yanzu na riga na ba shekaru 90 baya sosai, Jehobah wanda shi ne babban injiniya a duk sararin samaniya ya ci gaba da ƙarfafa ni in ci gaba da yi masa hidima.