ABIN DA KE SHAFIN FARKO | ALHERIN DA ALLAH YA YI MAKA
Taron da Bai Kamata A Ba Ka Labari Ba
A dare na ƙarshe da ya yi kafin ya mutu, Yesu ya umurci mabiyansa su riƙa tuna da hadayar fansa da zai yi. Ta wajen yin amfani da gurasa marar yisti da kuma ruwan inabi, ya kafa abin da ake kira Jibin Maraice na Ubangiji kuma ya ce: “Ku yi wannan abin tunawa da ni.”—Luka 22:19.
Kowace shekara, Shaidun Jehobah a dukan duniya suna yin taro don su tuna da mutuwar Yesu a duk lokacin da ranar ta zagayo. A shekara ta 2014, za a yi taron Tunawa da Mutuwar Yesu a ranar Litinin 14 ga Afrilu, bayan faɗuwar rana.
Muna gayyatar ka zuwa wannan taron, kuma a wurin za a ƙara tattauna dalilin da ya sa mutuwar fansa da Yesu ya yi take da muhimmanci sosai. Ba a karɓan ko sisi a wurin. Wanda ya ba ka wannan mujallar zai iya gaya maka lokaci da kuma wurin da za a yi taron a yankinku, ko kuma za ka iya bincika hakan a dandalin www.pr418.com/ha. Don Allah, ka rubuta wannan kwanan watan a wani wuri don kada ka manta. Muna fatan za ka halarci taron.