Mene ne Zai Faru A Nan Gaba?
© 2018 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
Wannan mujallar ba ta sayarwa ba ce. Sashe ce ta aikin ilimantarwa na Littafi Mai Tsarki a dukan duniya wadda ake tallafa wa da gudummawar da aka ba da da son rai. Don ba da gudummawa, ka shiga jw.org/ha. An ɗauko nassosin da aka yi amfani da su a nan ne daga Littafi Mai Tsarki: Juyi Mai Fitar da Ma’ana. A duk inda kuka ga an rubuta LMT, ana nufin an yi ƙaulin wata fassarar Littafi Mai Tsarki ne. Idan kuma kuka ga NW, ana nufin an yi ƙaulin fassarar New World Translation.
WANNAN MUJALLAR, Hasumiyar Tsaro, ana buga ta ne don girmama Jehobah Allah, Mamallakin sama da ƙasa. Tana ƙarfafa mutane cewa Mulkin Allah zai kawar da dukan mugunta kuma ya mai da duniya aljanna ba da daɗewa ba. Tana sa a ba da gaskiya ga Yesu Kristi, wanda ya mutu domin mu sami rai madawwami kuma wanda a yanzu shi ne Sarkin Mulkin Allah. An soma buga wannan mujallar babu fashi tun daga shekara ta 1879. Wannan mujallar ba ta siyasa ba ce. Littafi Mai Tsarki ne madogaranta.