Sanarwa
◼ Littafin da za a bayar a watan Fabrairu: Asirin Farinciki Na Iyali ko Ka Bauta wa Allah Makaɗaici na Gaskiya. Maris: Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa? Masu shela su ƙudurta soma nazarin Littafi Mai Tsarki a wurin da suka ba da wannan littafin ko kuma wurin da masu gida sun riga sun samu kofi ɗaya a gida. Afrilu da Mayu: Mujallun Hasumiyar Tsaro da Awake! Sa’ad da ake koma ziyara wurin masu marmari, har da waɗanda suka halarci Tuna Mutuwar Yesu ko kuma wasu tarurruka amma ba sa halartan taron ikilisiya kullum, a mai da hankali ga ba da littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa? Ƙudurin ya zama soma nazarin Littafi Mai Tsarki.
◼ Za a ba da jawabi na musamman na shekara ta 2010 a makon 12 ga Afrilu, 2010. Jigon shi ne “A Wane Lokaci Ne Za a Sami Salama da Kāriya ta Ainihi?” Ikilisiyoyi da suke da taro na musamman, taron da’ira ko ziyarar mai kula da da’ira a makon 12 ga Afrilu, 2010, za su iya ba da jawabin a makon 19 ga Afrilu, 2010.