Sanarwa
◼ Littafin da za a ba da a watan Janairu: Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa? Ku yi ƙoƙarin soma nazarin Littafi Mai Tsarki a ziyara ta farko. Idan mai gidan yana da littafin kuma bai yarda a yi nazarin Littafi Mai Tsarki da shi ba, masu shela za su iya ba da tsofaffin mujallu ko jaridu da suka dace da mai gidan. Fabrairu: Asirin Farinciki Na Iyali da Ka Kusaci Jehovah. Maris: Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa? Ku yi ƙoƙarin soma nazarin Littafi Mai Tsarki a ziyara ta farko. Afrilu: Mujallun Hasumiyar Tsaro da Awake!
◼ Somawa daga watan Fabrairu, masu kula da da’ira za su gabatar da wannan jawabin mai jigo: “Kana Dogara ga Jehobah Kuwa?”
◼ Muna farin cikin sanar cewa za a yi taro na musamman da taron da’ira a Yaren Kurame na Amirka a shekara ta 2012 a waɗannan wuraren: Badagry a ranar 18 ga Fabrairu da 2-3 ga Yuni. Benin City a ranar 25-26 ga Fabrairu da 7 ga Yuli; Ibadan a ranar 14-15 ga Afrilu da 14 ga Yuli ; Kwali a ranar 10-11 ga Maris (taron da’ira kawai); Lekki a ranar 19-20 ga Mayu da 26 ga Agusta ; Uli a ranar 5-6 ga Mayu da 18 ga Agusta. Kuma za a yi taro na musamman da na da’ira a Faransanci a waɗannan wuraren: Badagry a ranar 1 ga Afrilu da 9-10 ga Yuni. Za a gabatar da wannan taron a Yaren Kurame na Amirka da Faransanci kaɗai. Muna gayyatar waɗanda suka iya waɗannan harsunan zuwa wannan taron.
◼ Somawa da fitowar Hasumiyar Tsaro ta wa’azi ta watan Afrilu-Yuni, 2012, za a riƙa wallafa wannan sabon talifi mai jigo, “Abin da Na Koya Daga Littafi Mai Tsarki.” An shirya wannan talifin ne don iyaye su tattauna shi da yaransu jarirai zuwa shekara uku. Zai sauya talifofin nan “Ku Koyar da Yaranku” da “Domin Matasa.”