Rahotannin Wa’azi
Fitaccen rahoto na watan Agusta 2012 ya nuna cewa ƙolin majagaba 34,383 ne suka ba da rahoto. Hakan ya sa an sami ƙarin majagaba 1,144 a kan na bara. Abin farin ciki kuma shi ne, mun sami ƙari a yawan littattafan da aka ba mutane da kuma nazarin Littafi Mai Tsarki da aka gudanar. Mun yi nazari da mutane 766,092 kuma hakan ya fi yawan mutane da muka yi nazari da su a watan Agusta bara da mutane 62,441. Muna godiya ga Jehobah don albarkar da yake mana a hidimarmu! Bari mu ci gaba da ‘duƙufa kan yin wa’azi’!—A. M. 18:5.