Tsarin Ayyuka na Makon 20 ga Mayu
MAKON 20 GA MAYU
Waƙa ta 70 da Addu’a
□ Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya:
wt babi na 6, sakin layi na 1-10 (minti 30)
□ Makarantar Hidima ta Allah:
Karatun Littafi Mai Tsarki: Yohanna 8-11 (minti 10)
Na 1: Yohanna 8:12-30 (minti 4 ko ƙasa da hakan)
Na 2: Mene Ne Ya Kamata Mu Yi don Mu Kāre Kanmu Daga Malaman Ƙarya?—Rom. 16:17; 2 Yoh. 9-11 (minti 5)
Na 3: Abin da Ya Sa Allah Ya Ƙyale Mugunta—td 32B (minti 5)
□ Taron Hidima:
Waƙa ta 96
Minti 10: Hanyoyin da Za Ku Iya Faɗaɗa Hidimarku—Sashe na 3. Ka tattauna bayanin da ke littafin Organized to Do Jehovah’s Will, shafi na 116, sakin layi na 1 zuwa shafi na 117, sakin layi na 1. Ka gana da mai shela ɗaya ko biyu da suka taimaka wajen gina Majami’un Mulki da Majami’un Taro. A waɗanne hanyoyi ne suka ji daɗin wannan hidimar?
Minti 10: Jehobah Yana Taimaka Mana Mu Cika Hidimarmu. (Fit. 4:10-12; Filib. 4:13) Ka tattauna bayanin da ke w10 9/15 shafi na 10, sakin layi na 13-14. Ka gaya wa masu sauraro su faɗi darussan da suka koya.
Minti 10: “Wa Zai Fi Son Wannan Talifin?” Tambayoyi ana ba da amsoshi. Ka gaya wa masu sauraro su ambaci wasu ofisoshin ƙananan hukumomi da na cinikayya da ke yankinku da za su so su sami bayani game da wani batu da ya fito a mujallunmu.
Waƙa ta 92 da Addu’a