Sanarwa
◼ Littattafan da za mu ba mutane a watannin Satumba da Oktoba: Mujallun Hasumiyar Tsaro da Awake! Nuwamba da Disamba: Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa? ko kuma Za Ka So Ka San Amsoshin Waɗannan Tambayoyin?
◼ A shekara ta 2015, za a ba da jawabi na musamman na lokacin Tuna Mutuwar Yesu a makon 6 ga Afrilu. Za a sanar da jigon jawabin a nan gaba. Ikilisiyoyin da mai kula da da’ira zai ziyarce su ko waɗanda suke da taron da’ira a wannan makon za su iya ba da jawabin a mako na gaba. Kada ikilisiyoyi su ba da jawabin kafin ranar 6 ga Afrilu.
◼ Daga watan Satumba, jigon jawabi ga jama’a da masu kula da da’ira za su riƙa bayarwa shi ne, “Yadda Hikima Daga Allah Take Amfanar Mu.”