8-14 ga Fabrairu
NEHEMIYA 5-8
Waƙa ta 123 da Addu’a
Gabatarwar Taro (minti 3 ko ƙasa da hakan)
DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH
“Nehemiya Mai Kula Ne da Ya Ƙware”: (minti 10)
Ne 5:1-7—Nehemiya ya saurari mutanen kafin ya ɗauki mataki (w06 2/1 28 sakin layi na 2)
Ne 5:14-19—Nehemiya ya nuna tawali’u da rashin son kai da kuma hikima (w06 2/1 29 sakin layi na 4)
Ne 8:8-12—Nehemiya ya koyar da mutane su kasance da dangantaka mai kyau da Jehobah (w06 2/1 30 sakin layi na 4)
Neman Abubuwa Masu Tamani: (minti 8)
Ne 6:5—Me ya sa Sanballat ya aika wa Nehemiya “wasiƙa a buɗe”? (w06 2/1 28 sakin layi na 3)
Ne 6:10-13—Me ya sa Nehemiya bai yarda da shawarar Shemaiya ba? (w07 7/1 30 sakin layi na 15)
Mene ne karatun Littafi Mai Tsarki na wannan makon ya koya mini game da Jehobah?
Waɗanne darussa ne na koya a karatun Littafi Mai Tsarki na wannan makon da zan iya yin amfani da su a wa’azi?
Karatun Littafi Mai Tsarki: Ne 6:14–7:7a (minti 4 ko ƙasa da hakan)
KA YI WA’AZI DA ƘWAZO
Haɗuwa ta Fari: (minti 2 ko ƙasa da hakan) Ku ba da sabon Awake! ta wajen gabatar da jigon da ke bangon mujallar. Ka yi wata tambaya ko kuma ka ambaci wani batun da za ku tattauna idan ka dawo.
Koma Ziyara: (minti 4 ko ƙasa da hakan) A nuna yadda za a koma ziyara wurin wani da ya so bangon sabon Awake! Ka yi wata tambaya ko kuma ka ambaci wani batun da za ku tattauna idan ka dawo.
Nazarin Littafi Mai Tsarki: (minti 6 ko ƙasa da hakan) Ka sa a nuna yadda ake yin nazarin Littafi Mai Tsarki. (bh 28-29 sakin layi na 4-5)
RAYUWAR KIRISTA
Waƙa ta 62
Kana “Biɗan Aiki” Mai Kyau Kuwa?: (minti 15) Jawabin da dattijo zai yi daga Hasumiyar Tsaro ta 15 ga Satumba, 2014, shafuffuka na 3-6. Ka saka bidiyon nan ‘Yan’uwa Maza, Ku Yi Ƙoƙari don Samun Ƙarin Gata da ke JW Broadcasting na Disamba 2015. Ka ƙarfafa ‘yan’uwa su biɗi aiki mai kyau ta wurin ƙoƙartawa don su cancanci yin hidimar bayi masu hidima ko kuma dattawa.
Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya: ia babi na 8 sakin layi na 17-27, da tambayoyi don bimbini da ke shafi na 75 (minti 30)
Bita da Abin da Za A Tattauna Mako Mai Zuwa (minti 3)
Waƙa ta 125 da Addu’a