Littattafan da Aka Ɗauko Bayanai Daga Cikinsu a Littafin Taro don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu
4-10 GA NUWAMBA
DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH | 1 YOHANNA 1-5
“Kada Ku Ƙaunaci Duniya Ko Abubuwan da Suke Cikinta”
(1 Yohanna 2:15, 16) Kada ku ƙaunaci duniya, ko abubuwan da suke cikinta. Duk wanda yake ƙaunar duniya, to, babu ƙaunar Uban a cikinsa. 16 Gama dukan abubuwan da suke a duniya, kamar neman biyan sha’awa ta jiki, da kwaɗayin ido, da kuma taƙama da abubuwan rayuwa. Waɗannan dai ba daga wurin Uba suka fito ba, amma daga duniya ne suka fito.
(1 Yohanna 2:17) Duniya da dukan muguwar sha’awarta tana wucewa, amma wanda ya aikata nufin Allah zai rayu har abada.
(1 Yohanna 2:7, 8) Ya ku waɗanda nake ƙauna, ba domin in ba ku sabon umarni nake rubuta muku ba. Ai, umarni na dā ne wanda kuke da shi tun daga farko. Umarnin nan na dā kuwa shi ne saƙon da kun riga kun ji. 8 Amma duk da haka, ina rubuta muku sabon umarni, wanda yake tabbatacce ga Almasihu, haka ma a gare ku. Ai, duhu yana ƙārewa, hasken gaskiya kuwa ya riga ya fara haskakawa.
(1 Yohanna 5:16, 17) Idan wani ya ga ɗan’uwansa yana yin zunubi wanda bai kai ga mutuwa ba, sai ya yi masa addu’a. Saboda mai addu’ar nan kuwa Allah zai ba mai zunubin nan rai. Ko da yake akwai zunubin da yake kai ga mutuwa, amma ban ce a yi addu’a game da wannan ba. 17 Duk rashin adalci zunubi ne, amma ba kowane zunubi yana kai ga mutuwa ba.
it-1-E 862 sakin layi na 5
Gafartawa
Yana da kyau mu yi addu’a a madadin mutane ko kuma ’yan’uwa a ikilisiya don gafarar zunubai. Musa ya yi addu’a a madadin al’umar Isra’ila don gafara, ya gaya wa Allah zunubansu kuma Allah ya amsa addu’arsa. (L.Ƙi 14:19, 20) Ban da haka ma, a lokacin da ake keɓe haikali, Sulemanu ya yi addu’a a madadin mutanensa don Allah ya gafarta musu idan suka yi zunubi kuma su daina yin zunubin. (1Sar 8:30, 33-40, 46-52) Ezra ma ya yi addu’a a madadin Yahudawa da suka dawo ƙasarsu don Allah ya gafarta musu zunubansu. Addu’arsa da kashedin da ya yi musu ya sa mutanen sun ɗauki matakin da ya dace don Jehobah ya gafarta musu zunubansu. (Ezr 9:13–10:4, 10-19, 44) Manzo Yaƙub ya ƙarfafa wanda ya yi zunubi ya kira dattawan ikilisiya don su yi masa addu’a kuma idan ya yi hakan, “za a gafarta masa.” (Yaƙ 5:14-16) Amma akwai “zunubin da yake kai ga mutuwa,” irin wannan zunubin shi ne yin saɓo ga ruhu mai tsarki, wato yin zunubi da gangan. Allah ba ya gafarta irin wannan zunubin. Bai kamata Kirista ya yi addu’a a madadin irin waɗannan mutanen ba.—1Yo 5:16; Mt 12:31; Ibr 10:26, 27.
Karatun Littafi Mai Tsarki
(1 Yohanna 1:1–2:6) Muna yi muku shela game da wanda tun farko yana nan, wanda muka ji, muka gani da idanunmu, muka duba, muka kuma taɓa da hannuwanmu, wato game da Kalma mai ba da Rai. 2 Wannan rai kuwa an bayyana mana shi, mun kuma gan shi. A kansa ne muke ba da shaida muna kuma sanar muku cewa shi ne Mai Rai nan na har abada, wanda tun dā yake tare da Uba, aka kuwa bayyana mana shi. 3 Muna yi muku shelar abin da muka ji, muka kuma gani ne, domin ku ma ku yi zumunta tare da mu. Zumuntarmu kuwa tana tare da Allah Uba, da kuma Ɗansa Yesu Almasihu. 4 Muna kuma rubuta muku wannan ne domin farin cikinmu ya zama cikakke. 5 Wannan shi ne saƙon da muka ji daga wurin Ɗansa cewa, Allah haske ne, kuma a cikinsa babu duhu ko kaɗan. 6 Saboda haka in mun ce muna zumunci da Allah, amma kuma muna ci gaba da tafiya cikin duhu, to, muna ƙarya ke nan, kuma ba ma bin gaskiya. 7 Amma in muna tafiya cikin haske kamar yadda Allah yake cikin haske, muna zumunta da juna ke nan, jinin Yesu Ɗansa kuma yana tsabtace mu daga dukan zunubi. 8 Idan mun ce ba mu da zunubi, ruɗin kanmu muke yi, gaskiya kuwa ba ta cikinmu. 9 Amma idan mun faɗa wa Allah zunubanmu, ai, shi mai aminci ne, mai gaskiya kuma, zai kuma gafarta mana zunubanmu, ya kuma tsabtace mu daga dukan rashin adalcinmu. 10 In mun ce ba mu yi zunubi ba, mun mai da Allah mai ƙarya ke nan, kuma kalmarsa ba ta cikin zuciyarmu. 2 Ya ku ’ya’yana waɗanda nake ƙauna, ina rubuta muku wannan ne domin kada ku yi zunubi. Amma in har wani ya yi zunubi, to, muna da mai tsaya mana a gaban Uba, wato Yesu Almasihu mai adalci. 2 Shi ne hadaya ta ɗaukar alhakin zunubanmu, ba tamu kaɗai ba amma har da ta dukan duniya. 3 In mun yi biyayya da umarnin Allah, to, wannan zai tabbatar mana cewa mun san shi. 4 Duk wanda ya ce, “Ai, na san Allah,” amma bai yi biyayya da umarnin Allah ba, to, wannan mutumin mai ƙarya ne, kuma gaskiya ba ta cikinsa. 5 Amma wanda ya yi biyayya da kalmar Allah, to, ai, ƙaunar Allah ta zama cikakkiya ke nan a cikinsa. Ta haka ne za mu tabbatar cewa muna cikinsa. 6 Duk wanda ya ce yana rayuwa cikin Allah, dole ne ya yi tafiyarsa kamar yadda Yesu Almasihu ya yi.
11-17 GA NUWAMBA
DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH | 2 YOHANNA 1–YAHUDA
“Dole Mu Dāge Sosai Mu Kiyaye Bangaskiyarmu”
(Yahuda 3) Ya ku waɗanda nake ƙauna, dā ma na yi marmarin rubuta muku game da ceton nan namu duka. Amma daga baya na ga ya zama dole ne in rubuta muku in gargaɗe ku ku dāge sosai ku kiyaye bangaskiyarku wadda Allah ya danƙa wa tsarkakansa, sau ɗaya tak, ba ƙari.
Neman Abubuwa Masu Tamani
(Yahuda 20, 21) Amma ya ku waɗanda nake ƙauna, ku yi ta gina kanku a kan bangaskiyarku nan mafi tsarki. Ku kuma yi addu’a ta wurin ikon Ruhu Mai Tsarki. 21 Ku kiyaye kanku cikin ƙaunar Allah, kuna jiran Ubangijinmu Yesu almasihu wanda cikin jiƙansa zai kai ku ga rai na har abada.
(Yahuda 14, 15) Enok ma, wanda yake na tsara ta bakwai daga Adam, shi ma ya yi annabci a kan waɗannan mutane cewa, “Duba dai, Ubangiji yana zuwa da mala’ikunsa masu tsarki, 15 domin ya aikata hukuncinsa a kan kowa. Zai nuna wa marasa hali iri na Allah dukan aikinsu na rashin halin Allah. Zai tone dukan mugayen maganganun da masu zunubi marasa hali iri na Allah suka faɗa game da shi.”
Karatun Littafi Mai Tsarki
(2 Yohanna 1-13) Daga dattijon nan zuwa uwargida wadda Allah ya zaɓa da kuma ’ya’yanta, waɗanda nake ƙauna ƙwarai da gaske. Ba ni kaɗai nake ƙaunarku ba, har ma da dukan mutanen da suka san gaskiyar nan ta Allah. 2 Wato, muna ƙaunarku saboda gaskiyar nan da take cikin zuciyarmu, kuma za ta zauna da mu har abada. 3 Alheri, da jinƙai, da salama daga wurin Allah Uba da Yesu Almasihu, Ɗan Uban za su tabbata a gare mu cikin gaskiya da ƙauna. 4 Na yi farin ciki sosai sa’ad da na ga cewa waɗansu a cikin ’ya’yanku suna bin gaskiyar nan, kamar yadda Allah Ubanmu ya umarce mu. 5 Yanzu kuma ina roƙonki, uwargida, mu ƙaunaci juna. Wannan ba wani sabon umarni ba ne, umarnin da muke da shi ne tun daga farko. 6 Ainihin ƙauna ita ce, mu bi umarnan Allah. Umarnin nan kuma da kuka ji tun daga farko shi ne, ku yi zaman ƙauna. 7 Na ce haka gama mutane da yawa masu ruɗin mutane sun fito, sun bazu ko’ina cikin duniya. Ba su yarda cewa Yesu Almasihu ya zo wannan duniya da jikin mutum ba. Irin mutanen nan masu ruɗu ne kuma masu gāba da Almasihu. 8 Saboda haka ku lura, domin kada dukan abin da kuka yi ya zama banza, a maimako ku sami cikakken ladanku. 9 Duk mutumin da bai tsaya a kan koyarwar Almasihu ba, amma ya yi ƙari a kanta, mutumin nan ba shi da Allah. Amma wanda ya tsaya a kan koyarwar Almasihu, yana da Uban da kuma Ɗan. 10 Idan wani ya zo yana koyar da wani abu dabam da wannan koyarwa, kada ku karɓe shi, kada ma ku gaishe shi. 11 Gama idan wani ya gai da irin wannan mutum, yana haɗa kai da mutumin cikin mugun aikinsa ke nan. 12 Ina da abubuwa da yawa waɗanda nake so in rubuta muku, amma ba na so in rubuta su a wasiƙar nan. A maimakon haka, ina fata zan sami dama in zo wurinku domin mu tattauna fuska da fuska, domin farin cikinmu ya zama cikakke. 13 ’Ya’yan ’yar’uwarki wadda Allah ya zaɓa, suna gaishe ki.
18-24 GA NUWAMBA
DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH | RU’UYAR DA AKA YI WA YOHANNA 1-3
“Na San Ayyukanku”
(Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 1:20) Ga ma’anar asirin taurari bakwai waɗanda ka gani a hannun damana, da kuma ma’anar asirin sandunan zinariya guda bakwai masu riƙe fitilu. Taurari bakwai nan, mala’iku bakwai na jama’ar masu bi ne, kuma sandunan zinariya guda bakwai masu riƙe fitilun nan ma, jama’ar masu bi guda bakwai nan ne.
(Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 2:1, 2) “Rubuta wa mala’ikan jama’ar masu bi a Afisa cewa, ‘Ga saƙo daga wannan wanda yake riƙe da taurarin nan bakwai a hannun damansa, wanda kuma yake tafiya cikin sandunan zinariya guda bakwai masu riƙe fitilu. 2 Na san ayyukanka. Na san famar da ka yi cikin aikin bi da kuma haƙurin jimrewarka. Na san ba za ka iya yin haƙuri da mugayen mutane ba. Ka kuma gwada waɗanda suke ce da kansu manzannin, amma ba haka suke ba, kuma sai ka tarar cewa su manzannin ƙarya ne.
Neman Abubuwa Masu Tamani
(Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 1:7) Ga shi, zai zo a cikin girgije, kowa kuwa zai gan shi, har da waɗanda suka soke shi. Dukan ƙabilun duniya kuma za su yi kuka a kansa. Hakika! Wannan haka yake, Amin.
(Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 2:7) “Duk mai kunnen ji, bari ya ji abin da ruhu yake ce wa dukan jama’ar masu bi! Dukan wanda ya ci nasara, zan ba shi damar cin ’ya’yan itace mai ba da rai wanda yake cikin gonar Allah.”
Karatun Littafi Mai Tsarki
(Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 1:1-11) Ru’uyar Yesu Almasihu wanda Allah ya ba shi domin ya nuna wa bayinsa abin da zai faru ba da daɗewa ba. Yesu ya bayyana ru’uyar ta wurin aika mala’ikansa zuwa wurin bawansa Yohanna, 2 wanda ya shaida kalmar Allah, ya kuma shaida Yesu Almasihu ne, har ma da dukan abin da ya gani. 3 Mai albarka ne mutumin da yake karanta wannan kalmomin annabci, da waɗanda suke jin wannan kalmomin annabci, suke kuma kiyaye abin da aka rubuta a cikin littafin, gama lokacin da waɗannan abubuwa za su faru ya yi kusa. 4 Ni, Yohanna, ina rubuta zuwa ga jama’ar masu bi a wurare bakwai da suke a yankin ƙasar Asiya. Alheri da salama su kasance tare da ku daga Allah wanda yake a yanzu, shi ne a dā, shi ne kuma mai zuwa, da kuma daga ruhohin nan bakwai waɗanda suke a gaban kujerar mulkin Allah, 5 daga kuma Yesu Almasihu, wanda shi ne amintacce mai shaida, na farko cikin masu tashi daga matattu, mai mulkin sarakunan duniya. 6 shi ne ya mai da mu mu zama masu mulki da firistoci masu hidimar Allah Ubansa. Saboda haka bari Yesu Almasihu ya karɓi ɗaukaka da mulki har abada abadin. Amin. 7 Ga shi, zai zo a cikin girgije, kowa kuwa zai gan shi, har da waɗanda suka soke shi. Dukan kabilun duniya kuma za su yi kuka a kansa. Hakika! Wannan haka yake, Amin. 8 “Ni ne Farko, Ni ne Ƙarshe,” in ji Ubangiji Allah, wanda yake a yanzu, shi ne a dā, shi ne kuma mai zuwa, shi ne Mai Iko Duka. 9 Ni Yohanna ɗan’uwanku da kuma abokin tarayyarku ne cikin azaba da mulki da haƙurin jimrewa waɗanda suke namu cikin Yesu. An . . . ɗauke ni ƙarfi da yaji zuwa tsibirin Batmos saboda na yi wa’azin kalmar Allah da shaidar Yesu. 10 A ranar Ubangiji, sa’ad da Ruhu ya sauko a kaina, sai na ji wata babbar murya mai ƙara a bayana kamar ta ƙaho. 11 Muryar ta ce, “Rubuta abin da ka gani a littafi, ka aika wa jama’ar masu bi a wurare bakwai, wato a Afisa, da a Simirna, da a Birgamum, da a Tiyatira, da a Sardis, da a Filadelfiya, da kuma a Lawudikiya.”
25 GA NUWAMBA–1 GA DISAMBA
DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH | RU’UYAR DA AKA YI WA YOHANNA 4-6
“Fitowar Mahaya Huɗu”
(Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 6:2) Da na duba sai ga wani farin doki. Mai hawansa yana riƙe da baka, aka kuma ba shi hular mulki. Ya kuma fita kamar mai nasara domin ya ƙara cin nasara.
(Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 6:4-6) Sai wani doki ya fito ja wur. Aka ba mai hawansa iko ya kawar da salama daga duniya, domin mutane su kashe juna. Aka kuma ba shi babban takobi. 5 Da Ɗan Ragon ya ɓalle hatimi na uku, sai na ji halitta ta uku daga cikin halittun masu rai ta ce, “Zo!” Da na duba, sai ga wani ɓakin doki. Mai hawansa yana riƙe da ma’auni a hannunsa. 6 Sai na ji wani abu mai kama da murya tana fitowa da cikin tsakiyar halittu masu rai guda haɗun nan tana cewa, “Mudun hatsin alkama na yawan kuɗin da lebura zai samu na aiki yini ɗaya, mudu uku na hatsin bale na yawan kuɗin da lebura zai sami na aiki yini ɗaya, amma fa kada ka lalatar da man zaitun da kuma ruwan inabi.”
(Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 6:8) Da na duba, sai ga wani doki wanda kalarsa ta koɗe. Sunan mai hawansa kuwa Mutuwa ce, Wurin Zaman Matattu kuma yana biye da shi. Aka ba su iko a kan kashi ɗaya bisa huɗu na mazaunan duniya, domin su kashe su ta wurin takobi, da yunwa, da bala’i da kuma namomin daji.
Neman Abubuwa Masu Tamani
(Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 4:4) Kewaye da kujerar mulkin kuwa akwai waɗansu kujerun mulki ashirin da huɗu, waɗanda dattawa ashirin da huɗu suka zauna a kai. Suna sanye da farare riguna tare da hulunan mulki na zinariya a kan kowannensu.
(Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 4:6) A gaban kujerar mulkin kuma akwai wani abu kamar tafkin gilas, yana ƙyalli kamar madubi a rana. Kuma kewaye da kujerar mulkin a ta kowane gefe kuwa, akwai halittu masu rai guda huɗu cike da idanu gaba da baya.
re-E 76-77 sakin layi na 8
Ɗaukakar Kursiyin Jehobah
Yohanna ya san cewa ana naɗa firistoci domin su riƙa yin hidima a mazauni. Don haka, ya yi mamakin ganin wahayin nan da ke gaba, ya ce ya ga: “Kewaye da kujerar mulkin kuwa akwai waɗansu kujerun mulki ashirin da huɗu, waɗanda dattawa ashirin da huɗu suka zauna a kai. Suna sanye da farare riguna tare da hulunan mulki na zinariya a kan kowannensu.” (Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 4:4) A maimakon ya ga firistoci, ya ga dattawa ashirin da huɗu da suka yi ado kamar sarakuna. Su waye ne dattawan nan? Su ne shafaffu na ikilisiyar Kirista da aka ta da su zuwa sama kuma suna hidima kamar yadda Jehobah ya musu alkawari. Ta yaya muka san da hakan?
re-E 80 sakin layi na 19
Ɗaukakar Kursiyin Jehobah
Me waɗannan halittu suke wakilta? Wahayin da wani annabi mai suna Ezekiyel ya gani ya ba da amsar. Ezekiyel ya ga kursiyin Jehobah a kan wata karusa mai haske tare da wasu halittu masu kama da halittun da Yohanna ya gani a wahayi. (Ezekiyel 1:5-11, 22-28) Bayan haka, Ezekiyel ya sake ganin wannan karusar tare da halittun nan, amma a wannan karon ya kira halittun cherubim. (Ezekiyel 10:9-15) Don haka, halittu guda huɗun da Yohanna ya gani a wahayi suna wakiltar cherubim da yawa na Allah, wato mala’iku masu babban matsayi. Yohanna bai yi mamakin ganin cherubim kusa da Jehobah ba domin a cikin mazauni na zamanin dā, akwai cherubim guda biyu na zinariya da aka saka a kan akwatin alkawari da yake wakiltar kursiyin Jehobah. Kuma daga tsakanin waɗannan cherubim ne ake jin muryar Jehobah idan yana so ya ba wa al’umar dokoki ko umurni.—Fitowa 25:22; Zabura 80:1.
(Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 5:5) Sai ɗaya daga cikin dattawan nan ya ce mini, “Kada ka yi kuka! Ga shi! Zakin nan daga zuriyar Yahuda, tushen Dawuda ya riga ya ci nasara, yana da iko ya ɓalle hatiman nan bakwai ya kuma buɗe littafin.”
cf-E 36 sakin layi na 5-6
“Ga shi! Zakin nan daga zuriyar Yahuda”
Akan kwatanta zaki da ƙarfin zuciya. Shin ka taɓa ganin zaki ido-da-ido? Idan ka taɓa ganin sa, to wataƙila akwai wata katanga da ta raba ka da shi a gidan da ake ajiye dabbobi. Duk da haka, ka ji tsoro sosai sa’ad da ka haɗa ido da shi. A lokacin da ka kalli wannan zaki shi ma ya kalle ka, babu shakka, ka san cewa ba wani abu da zai iya tsoratar da shi. Littafi Mai Tsarki ya yi magana game da wani “zakin da ya fi dukan dabbobi ƙarfi, ba ya ba wani hanya.” (Karin Magana 30:30) Irin wannan ƙarfin zuciyar ne Kristi yake da shi.
Bari mu tattauna yadda Yesu ya nuna irin ƙarfin zuciyar da zaki yake da shi a hanyoyi uku: yadda ya goyi bayan gaskiya da adalci, da kuma yadda ya yi ƙarfin zuciya sa’ad da yake fuskantar tsanani. Za mu sake ganin yadda dukanmu za mu nuna ƙarfin zuciya kamar yadda Yesu ya yi.
Karatun Littafi Mai Tsarki
(Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 4:1-11) Bayan wannan, na duba sai na ga wata ƙofa a buɗe a sama. Muryar nan wadda na ji da farko mai ƙara kamar ƙaho, ta ce, “Hauro nan, zan nuna maka abin da lallai zai faru bayan wannan.” 2 Nan da nan sai Ruhu ya sauko a kaina, na kuma ga a can cikin sama wata kujerar mulki wadda wani yake zama a kai. 3 Mai zama a kujerar mulkin kuwa yana ƙyalli kamar duwatsu masu daraja, wato yasfa da karneliyan. Kewaye da kujerar mulkin kuma akwai wani bakan gizo mai ƙyalli kamar dutsen zumurrudu. 4 Kewaye da kujerar mulkin kuwa akwai waɗansu kujerun mulki ashirin da huɗu, waɗanda dattawa ashirin da huɗu suka zauna a kai. Suna sanye da farare riguna tare da hulunan mulki na zinariya a kan kowannensu. 5 Sai walƙiya take ƙararraki da kuma tsawa. A gaban kujerar mulkin kuwa akwai fitilu bakwai suna ci, waɗanda suke ruhohin nan bakwai na Allah. 6 A gaban kujerar mulkin kuma akwai wani abu kamar tafkin gilas, yana ƙyalli kamar madubi a rana. kuma kewaye da kujerar mulkin a ta kowane gefe kuwa, akwai halittu masu rai guda huɗu cike da idanu gaba da baya. 7 Halitta ta farkon nan mai rai kama da zaki take, na biyun kama da bijimi, na ukun kama da mutum, na huɗun kama da gaggafa mai tafiya a sama. 8 Kowace halitta daga cikin halittu huɗun nan masu rai suna da fikafikai shida, akwai idanu kewaye da su duka har da ƙarƙashin fikafikansu. Dare da rana ba sa daina waƙa cewa, “Mai Tsarki, Mai Tsarki, Mai Tsarki, Ubangiji Allah Mai Iko Duka! Shi ne a dā, shi ne a yanzu, shi ne kuma mai zuwa.” 9 Halittun nan huɗu masu rai, suka rera waƙoƙin ɗaukaka, da na girma, da na godiya ga wannan da yake zama a kujerar mulkin, yake kuma raye har abada abadin. Duk lokacin da suke yin haka, 10 dattawa ashirin da haɗun nan sukan faɗi a gaban wannan da yake zama a kujerar mulkin, sukan yi masa sujada, shi wanda yake raye har abada abadin. Sukan ajiye hulunan mulkinsu a ƙasa a gaban kujerar mulkin, suna cewa, 11 “Ya Ubangiji Allahnmu, ka cancanci ka karɓi ɗaukaka, da girma, da iko. Gama ka halicci kome da kome, kuma ta wurin nufinka suka kasance aka kuma halicce su.”