Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • wp25 Na 1 pp. 4-5
  • Yadda Yaki da Tashin Hankali Suke Shafan Dukanmu

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Yadda Yaki da Tashin Hankali Suke Shafan Dukanmu
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Wa’azi)—2025
  • Makamantan Littattafai
  • Yadda Za A Kawo Ƙarshen Yaƙi da Tashin Hankali
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Wa’azi)—2025
  • An Shiga Shekara Ta Biyu a Yakin Yukiren​—Wane Bege ne Ke Littafi Mai Tsarki?
    Karin Batutuwa
  • Me Ya Sa Ba A Daina Yaƙi da Tashin Hankali Ba?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Wa’azi)—2025
  • Gabatarwa
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Wa’azi)—2025
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Wa’azi)—2025
wp25 Na 1 pp. 4-5
Hotuna: 1. Wani soja yana takawa a wani fili kuma ga tankin yaƙi yana bin sa a baya. 2. Wasu mazaje, da mata, da yara daga ƙasashe dabam-dabam waɗanda yaƙi ya shafa.

Yadda Yaƙi da Tashin Hankali Suke Shafan Dukanmu

“Tashin hankali yana ta ƙaruwa a faɗin duniya tun lokacin da aka yi Yaƙin Duniya na Biyu. Kuma mutane biliyan 2, wato mutum ɗaya cikin huɗu na mutanen da ke duniya ne suke zama a wuraren da ake tashin hankalin.”

Mataimakiyar Babban Sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya, Amina J. Mohammed, 26 ga Janairu, 2023.

Yaƙi da tashin hankali za su iya ɓarkewa ba zato ba tsammani a wuraren da ake zaman lafiya. Ko mutanen da ba sa zama a wuraren da ake yaƙi ko tashin hankali ma, hakan zai iya shafan su. Bayan yaƙin, mummunan sakamakon za su iya shafan mutane na dogon lokaci. Ga wasu misalai:

  • Zanen hannaye biyu da suke riƙe da kwano da babu kome a ciki.

    Yaƙi yana jawo ƙarancin abinci. Hukumar Samar da Abinci ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce, “tashin hankali ne babban abin da ke jawo yunwa, domin kashi 70 na mutanen da suke fama da yunwa a faɗin duniya suna zama a wuraren da ake yaƙi da tashin hankali.”

  • Zanen wata mata da take baƙin ciki kuma ta rufe fuskarta da hannayenta.

    Yaƙi yana jawo raunuka da matsalar ƙwaƙwalwa. Idan akwai alama za a yi yaƙi a wani wuri, mutane a yankin sukan ji tsoro sosai kuma sukan yi fama da tsananin damuwa. Mutanen da suke zama a wuraren da ake tashin hankali za su iya jin rauni. Ban da haka ma, za su iya fama da matsalar ƙwaƙwalwa. Abin baƙin ciki shi ne, a yawancin lokaci, ba sa samun kulawar likitoci yadda suke bukata.

  • Zanen iyalin da suke ɗauke da manyan jakunkuna cike da kayansu.

    Yaƙi yana sa mutane su yi gudun hijira. Hukumar Kula da ꞌYan Gudun Hijira ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce zuwa Satumba 2023, mutane fiye da miliyan 114 a faɗin duniya ne aka tilasta musu su gudu su bar gidajensu. Kuma abubuwan da suka fi jawo hakan su ne yaƙi da tashin hankali.

  •  Zanen iyalin da suke tsaye a gaban gidansu.

    Yaƙi yana jawo matsalar tattalin arziki. A yawancin lokaci, yaƙi yana jawo matsalolin tattalin arziki. Alal misali, abubuwa sukan yi tsada sosai fiye da yadda aka saba. Mutane za su iya shan wahala sosai domin gwamnati tana kashe kuɗaɗe da yawa a kan sojoji da sayan makamai, waɗanda ya kamata ta kashe a kan kiwon lafiya da ilimi. Kuma bayan yaƙin, sake gina wuraren da yaƙi ya lalatar yana cin kuɗaɗe da yawa.

  • Zanen māi yana zubowa daga bututu.

    Yaƙi yana ɓata mahalli. Mutane sukan sha wahala sosai saꞌad da aka ɓata mahallinsu. Gurɓataccen ruwa, da iska, da kuma ƙasa za su iya jawo rashin lafiya na dogon lokaci. Ko bayan yaƙin ma, nakiyoyin da aka binne a ƙasa za su iya ji wa mutane rauni ko su kashe su.

Babu shakka, yaƙi yana da muni sosai kuma yana sa mutane su sha wahala ba kaɗan ba.

Abin da Littafi Mai Tsarki Ya Annabta Game da Yaƙi

Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa yaƙi da tashin hankali suna cikin alamar “ƙarshen zamani.” (Matiyu 24:3) Yesu Kristi ya ce:

  • “Za ku ji ana yaƙe-yaƙe da kuma labaran yaƙe-yaƙe. . . . Alꞌumma za ta yaƙi alꞌumma, mulki kuma ya yaƙi mulki.”—Matiyu 24:​6, 7.

  • “Kada ma ku ji tsoro in kun ji labarin yaƙe-yaƙe da tashin hankali.”—Luka 21:9.

    “Tashin hankali” yana nufin abubuwa kamar zanga-zanga, da faɗa tsakanin mutane saboda siyasa, da kuma tawaye ga gwamnati.

Don samun ƙarin bayani, ka karanta talifin nan “Mene ne Alamar ‘Kwanakin Ƙarshe’?” a dandalin jw.org/ha.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba