Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • my labari na 38
  • ’Yan Leƙen Asiri 12

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • ’Yan Leƙen Asiri 12
  • Littafina na Labarun Littafi Mai Tsarki
  • Makamantan Littattafai
  • ’Yan Leken Asiri
    Darussa daga Littafi Mai Tsarki
  • Joshua Ya Zama Shugaba
    Littafina na Labarun Littafi Mai Tsarki
  • Musa Ya Bugi Dutsen
    Littafina na Labarun Littafi Mai Tsarki
  • Rahab Ta Ɓoye ’Yan Leƙen Asiri
    Littafina na Labarun Littafi Mai Tsarki
Dubi Ƙari
Littafina na Labarun Littafi Mai Tsarki
my labari na 38

LABARI NA 38

’Yan Leƙen Asiri 12

DUBI ’ya’yan itatuwa da waɗannan mutane suka ɗauka. Dubi girman damin wannan inabi. Har sai mutane biyu suka ɗauka da sanda. Kuma dubi ’ya’yan ɓaure da rumanan nan. A ina aka sami waɗannan ’ya’yan itatuwa masu kyau? A ƙasar Kan’ana. Ka tuna, Kan’ana ita ce ƙasar da Ibrahim, Ishaku, da Yakubu suka taɓa zama a cikinta. Kuma domin ƙarancin abinci a nan, Yakubu da iyalinsa suka ƙaura zuwa ƙasar Masar. Amma yanzu, bayan shekaru 216, Musa yana ja-gorar Isra’ilawa zuwa Kan’ana. Suka isa wani wuri a cikin daji da ake kiran Ka’desh.

Miyagun mutane ne suke zaune a ƙasar Kan’ana. Saboda haka, Musa ya aika da mutane 12 su leƙi asiri, kuma ya gaya masu: ‘Ku je ku gani mutane nawa ne suke zaune a nan, kuma yaya ƙarfinsu. Ku duba ku gani ko ƙasar tana da kyau domin noma. Kuma ku dawo da ’ya’yan itatuwa.’

Sa’ad da ’yan leƙen asirin suka komo Ka’desh, suka gaya wa Musa: ‘Hakika ƙasa ce mai kyau.’ Kuma domin su tabbatar da haka, suka nuna wa Musa wasu cikin ’ya’yan itatuwa. Amma 10 cikin ’yan leƙen asirin suka ce: ‘Mutane da suke zaune a nan ƙattai ne masu ƙarfi. Za su kashe mu idan muka yi ƙoƙarin mu ƙwace ƙasar.’

Isra’ilawa suka tsorata da suka ji haka. ‘Da ya fi mu mutu a Masar ko kuma a nan cikin daji,’ suka ce. ‘Za a kashe mu a yaƙi, kuma a kama matanmu da ’ya’yanmu. Mu zaɓi sabon shugaba maimakon Musa, mu koma ƙasar Masar!’

Amma biyu cikin ’yan leƙen asirin suka dogara ga Jehobah, suka yi ƙoƙarin su kwantar wa mutanen hankali. Sunayensu Joshua da Kaleb. Suka ce: ‘Kada ku ji tsoro. Jehobah yana tare da mu. Ba zai yi wuya ba mu ƙwace ƙasar.’ Amma mutanen suka ƙi saurara. Har suna so su kashe Joshua da Kaleb.

Wannan ya sa Jehobah ya yi fushi sosai, ya gaya wa Musa: ‘Babu ɗaya cikin mutanen nan daga masu shekara 20 zuwa sama da za su shiga cikin ƙasar Kan’ana. Sun ga mu’ujizai da na yi a ƙasar Masar da kuma a cikin daji, amma duk da haka ba su yarda da ni ba. Saboda haka za su yi yawo a cikin daji nan na shekara 40 har sai dukansu sun mutu. Joshua da Kaleb ne kawai za su shiga ƙasar Kan’ana.’

Litafin Lissafi 13:1-33; 14:1-38.

Tambayoyi na Nazari

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba