Wane Bege Ƙaunatattu da Suka Mutu Suke da Shi?
“Idan mutum ya mutu za ya sake rayuwa?” wannan ita ce tambayar da mutumin nan Ayuba ya yi da daɗewa. (Ayuba 14:14) Wataƙila, kai ma, ka yi tunani game da wannan. Yaya za ka ji idan ka san cewa sake saɗuwa da waɗanda ka ke ƙauna zai yiwu bisa wannan duniyar ƙarƙashin yanayi da ya fi kyau?
Littafi Mai-Tsarki ya yi alkawari: “Matattunka za su yi rai. . . . za su tashi.” Littafi Mai-Tsarki ya kuma ce: “Masu-adalci za su gāji ƙasan, su zauna a cikinta har abada.”—Ishaya 26:19; Zabura 37:29.
Don mu ba da gaskiya ga irin waɗannan alkawuran, muna bukatar mu amsa wasu muhimman tambayoyi: Me ya sa mutane suke mutuwa? Ina ne matattu su ke? Kuma yaya za mu tabbata cewa za su sake rayuwa?
Mutuwa, da Abin da Ke Faruwa Sa’anda Muka Mutu
Littafi Mai-Tsarki ya yi bayani sarai cewa asali ba nufin Allah ba ne mutane su mutu. Ya halicci mutane biyu na farko Adamu da Hawa’u, ya sa su a cikin aljanna a duniya da aka kira Adnin, kuma ya umurce su su haifi ’ya’ya su faɗaɗa gidansu Aljanna zuwa dukan duniya. Idan suka yi rashin biyayya ga umurnansa ne kaɗai za su mutu.—Farawa 1:28; 2:15-17.
Don rashin godiya ga alherin Allah, Adamu da Hawa’u suka yi rashin biyayya kuma aka sa su sha horon da aka kafa. “[Za] ka koma ƙasa,” Allah ya gaya wa Adamu, “gama daga cikinta aka ciro ka: gama turɓaya ne kai, ga turɓaya za ka koma.” (Farawa 3:19) Kafin a halicce shi, Adamu bai wanzu ba; turɓaya ne shi. Kuma saboda rashin biyayyarsa, ko zunubi, aka yanka wa Adamu hukunci komawa ga turɓaya, yanayin rashin wanzuwa.
Mutuwa rashin rai ke nan. Littafi Mai-Tsarki ya nuna bambancin: “Hakin zunubi mutuwa ne; amma kyautar Allah rai na har abada ce.” (Romawa 6:23, tafiyar tsutsa tamu ce.) Ya nuna cewa mutuwa yanayin rashin sanin kome ne, Littafi Mai-Tsarki ya ce: “Gama masu-rai sun san za su mutu: amma matattu ba su san komi ba.” (Mai-Wa’azi 9:5) Idan mutum ya mutu, Littafi Mai-Tsarki ya yi bayani: “Numfashinsa ya kan fita, ya kan koma turɓayarsa kuma; A cikin wannan rana shawarwarinsa su kan lalace.”—Zabura 146:3, 4.
Amma, tun da yake Adamu da Hawa’u ne kawai suka take umurni a cikin Adnin, me ya sa dukanmu muke mutuwa? Domin an haife mu duka bayan rashin biyayyar Adamu, saboda haka dukanmu mun gāji zunubi da mutuwa daga wurinsa. Kamar yadda Littafi Mai-Tsarki ya yi bayani: “Zunubi ya shigo cikin duniya ta wurin mutum ɗaya [Adamu], mutuwa kuwa ta wurin zunubi; har fa mutuwa ta bi kan dukan mutane.”—Romawa 5:12; Ayuba 14:4.
Har ila, wani yana iya tambaya: ’Yan Adam ba su da kurwa mara mutuwa da take tsira wa mutuwa ne?’ Mutane da yawa sun koyar da wannan, har ma sun ce mutuwa hanya ce ta wata rayuwa. Amma wannan ra’ayin bai zo daga Littafi Mai-Tsarki ba. Maimakon haka, Kalmar Allah ta koyar da cewa mutum kurwa ne, ya nuna cewa kai ne kurwa, da duka iyawarka na jiki da na tunani. (Farawa 2:7; Irmiya 2:34; Misalai 2:10) Kuma Littafi Mai-Tsarki ya ce: “Mai-rai da ya yi zunubi, shi za ya mutu.” (Ezekiel 18:4) Ba inda Littafi Mai-Tsarki ya koyar da cewa mutum yana da kurwa mara mutuwa da ke tsira lokacin da jiki ya mutu.
Yadda Mutane Za Su Sake Rayuwa Kuma
Bayan zunubi da mutuwa sun shigo duniya, Allah ya bayyana cewa nufinsa ne a mayar da matattu zuwa rai ta wurin tashin matattu. A wannan hanyar Littafi Mai-Tsarki ya yi bayani: “Ibrahim . . . ya aza Allah yana da iko ya tada ko daga matattu [ɗansa Ishaƙu].” (Ibraniyawa 11:17-19) Gaba gaɗin Ibrahim ba kuskure ba ne, gama Littafi Mai-Tsarki ya faɗi game da Maɗaukaki: “Shi dai ba Allah na matattu ba ne, amma na masu-rai: gama duka suna rayuwa gareshi.”—Luka 20:37, 38.
Hakika, Allah Maɗaukaki ba mai iko ba ne kawai amma yana da muradin ya tayar da mutane da ya zaɓa. Yesu Kristi da kansa ya ce: “Kada ku yi mamakin wannan; gama sa’a tana zuwa, inda dukan waɗanda suna cikin kabarbaru za su ji muryatasa, su fito.”—Yohanna 5:28, 29; Ayukan Manzanni 24:15.
Ba da daɗewa ba bayan ya faɗi haka, Yesu ya gamu da wani jerin gwano na masu jana’iza suna fitowa daga birnin Isra’ila ta Nayin. Saurayin da ya mutu ɗan tilo ne na wata gwamruwa. Da ganin tana baƙin ciki sosai, Yesu ya ji tausayi. Sai ya matso wurin gawar, ya ba da umurni: “Saurayi, ina ce maka, Ka tashi!” Sai ya tashi, Yesu kuma ya ba da shi ga uwarsa.—Luka 7:11-17.
Yadda yake ga wannan gwamruwa, an yi farin ciki ƙwarai lokacin da Yesu ya ziyarci gidan Yairus, wani mahukuncin jama’a na majami’ar Yahudawa. ’Yarsa mai shekara 12 ta rasu. Amma lokacin da Yesu ya isa gidan Yairus, ya je wajen matacciyar kuma ya ce: “Yarinya, ki tashi!” Kuma ta tashi!—Luka 8:40-56.
Bayan haka, abokin Yesu Li’azaru ya rasu. Lokacin da Yesu ya isa gidansa, Li’azaru ya riga ya mutu da kwana huɗu. Ko da yake tana baƙin ciki sosai, ’yar’uwansa Martha ta nuna bege, cewa: “Na sani za ya tashi kuma a cikin tashin matattu a kan rana ta ƙarshe.” Amma Yesu ya je kabarin, ya ba da umurni a kawar da dutsen, kuma ya yi kira: “Li’azaru, ka fito!” Ya kuwa fito!—Yohanna 11:11-44.
Yanzu ka yi tunani game da wannan: Wane yanayi ne Li’azaru yake ciki kwanaki huɗu da ya mutu? Li’azaru bai ce kome ba game da zama a sama na jin daɗi ko a wutan jahannama, wanda lallai da ya faɗa idan ya je can. A’a, Li’azaru mamaci ne bai san kome ba kuma da ya kasance haka har sai “tashin matattu a kan rana ta ƙarshe” da a ce Yesu bai mayar da shi ba zuwa rai.
Gaskiya ne waɗannan mu’ujizoji na Yesu amfaninsu na ɗan lokaci ne kawai, tun da waɗanda ya tayar da su sun sake mutuwa. Amma, ya ba da tabbaci shekara 1,900 da suka shige cewa da ikon Allah, matattu za su sake rayuwa! Ta wurin mu’ujizojin Yesu ya nuna a ƙanƙanin hanya abin da zai faru a duniya a ƙarƙashin Mulkin Allah.
Lokacin da Wanda Ka Ke Ƙauna Ya Mutu
Lokacin da magabci mutuwa ya kawo hari, baƙin cikinka yana iya yin yawa ƙwarai, ko ma ƙila ka na da begen za a tashi matattu. Ibrahim yana da bangaskiya cewa matarsa za ta sake rayuwa, duk da haka mun karanta cewa “Ibrahim kuma ya zo domin makoki saboda Saratu, ya yi kuka kuma dominta.” (Farawa 23:2) Yesu kuma fa? Lokacin da Li’azaru ya mutu, ya “ji haushi cikin ruhunsa, yana jin zafi a ransa,” kuma jim kaɗan bayan haka ya “yi kuka.” (Yohanna 11:33, 35) Saboda haka, lokacin da wanda ka ke ƙauna ya mutu, ba kumammanci ba ne ka yi kuka.
Yayin da yaro ya mutu, musamman uwar tana baƙin ciki ƙwarai. Da haka, Littafi Mai-Tsarki ya san baƙin ciki mai ɗaci da uwa ta kan yi. (2 Sarakuna 4:27) Babu shakka, uba ma yana baƙin ciki sosai. “Da ma Allah ya yarda na mutu dominka,” abin da Sarki Dauda ya faɗa ke nan lokacin da yake baƙin cikin mutuwar ɗansa Absalom.—2 Samuila 18:33.
Duk da haka, domin kana da gaba gaɗi a tashin matattu, baƙin cikinka ba zai ci gaba ba. Kamar yadda Littafi Mai-Tsarki ya ce, kada “ku yi baƙinciki, kamar sauran mutane, waɗanda ba su da bege.” (1 Tassalunikawa 4:13) Maimako haka, ka matso kusa da Allah cikin addu’a, kuma Littafi Mai-Tsarki ya yi alkawari cewa “shi kuma za ya agaje ka.”—Zabura 55:22.
Sai dai ko an nuna alama, dukan ayoyin da aka yi amfani da shi daga Litafi Mai-Tsarki ne kuma an yi amfani da harufan zamani.