Ruhohi Basu Taɓa Rayuwa Kuma Mutu a Duniya Ba
Ruhohi sun wanzu! A cikin lardi na ruhu, da akwai nagargaru da kuma miyagun ruhohi. Ashe mutane ne da suka rayu kuma mutu a duniya?
A’a, ba su ba. Yayinda mutum ya mutu, shi ko ita ba ya wuce zuwa lardi na ruhu, kamar yadda mutane dayawa suke tunaninsa. Ta yaya muka san da haka? Don Littafi Mai-tsarki ya faɗi haka. Littafi Mai-tsarki littafi ne na gaskiya da ya zo daga wurin Allah na gaskiya kaɗai, wanda sunansa Jehovah ne. Jehovah ya hallici yan-Adam; ya san kuma abinda yake faruwa masu yayinda suka mutu.—Zabura 83:18; 2 Timothawus 3:16.
Littafi Mai-tsarki ya ce Allah ya yi mutum na farko, Adamu, “daga turɓayan ƙasa.” (Farawa 2:7) Allah ya ajiye shi cikin Aljanna, gonar Adnin. Da fa Adamu ya yi biyyaya da dokar Jehovah, da baza ya mutu ba; da har wa yau yana nan da rai. Amma yayinda Adamu ya taka dokar Allah da ganganci, Allah ya ce masa: “Kuma ka koma ƙasa gama daga cikinta aka ciro ka, gama turɓaya ne kai, ga turɓaya zaka koma.”—Farawa 3:19.
Minene wannan ke nufi? To dai, ina ne Adamu yake kafin Jehovah ya hallice shi daga turɓayan ƙasa? Ba shi ko’ina. Shi ba wani halittan ruhu ne cikin sama ba. Ba ya wanzu ba daɗai. Saboda haka fa yayinda Jehovah ya ce Adamu zaya “koma ƙasa,” yana nufin cewa Adamu zaya mutu ne. Baya haye zuwa cikin lardin ruhu ba. Adamu ya zama babu rai kuma, baya wanzuwa. Mutuwa rashin rai ne.
Amma minene ya faru ko ga wasu waɗanda suka mutu? Ashe basu wanzu su ma? Littafi Mai-tsarki ya amsa haka:
“Duk [yan-Adam da dabbobi] wuri ɗaya za su; duk na turɓaya ne, turɓaya kuma zasu koma.”—Mai-Wa’azi 3:20.
“Matattu basu san komi ba.”—Mai-Wa’azi 9:5.
“Ƙaunarsu duk da kiyayyassu, da kishinsu, yanzu sun ƙare.”—Mai-Wa’azi 9:6.
“Babu wani aiki, ko dabara, ko ilimi, ko hikima, cikin kabari [Sheol] inda zaka.”—Mai-Wa’azi 9:10.
“[Mutum] yakan koma turɓayansa kuma; a cikin wannan rana shawarwarinsa sukan lalace.”—Zabura 146:4.
Ashe waɗannan nassosi suna da wuyan yarda gareka ne? Idan haka ne, yi tunani game da wannan: A cikin iyalai dayawa, maji ne yake neman kuɗi don ci da iyalinsa. Yayinda mutumen ya mutu, iyalinsa sukan sha wahala. A wasu lokutta matar ma da yaransa ba zasu samu isasshen kuɗi don sayan abinci ba. Mai-yiwuwa magaɓtan mutumen ma su a wulakantar da su. To yanzu ka tambaye kanka: ‘Idan wannan mutum yana da rai cikin lardi na ruhu, don me baya ci gaba da tanadar da abinci ga iyalinsa ba? Me ya sa baya iya tsare iyalinsa daga miyagun mutane?’ Haka domin nassosin daidai suke. Wannan mutumen ba shi da rai, baya iya yin kome.—Zabura 115:17.
Ashe wannan yana nufin cewa matattu ba zasu komo zuwa rai kuma ba? A’a, ba haka ba ne. Zamu yi zance game da tashiwar matattu nan gaba. Amma ashe yana nufin cewa matattun mutane basu san abinda ka ke yi ba ke nan. Ba su a iya ganin ka, jin ka, ko kuwa yin magana da kai ba. Ba ka bukatan jin tsoronsu. Ba zasu iya taimakon ka ba, kuma ba zasu iya maka ɓarna ba.—Mai-Wa’azi 9:4; Ishaya 26:14.
[Hoto a shafi na 4]
Adamu daga turɓayan ƙasa ne, kuma ya koma zuwa turbayan ƙasa
[Hotuna a shafi na 5]
Masu rai ne kaɗai zasu iya yin waɗannan abubuwa
[Hotuna a shafi na 6]
Matattu ba su a taimake masu yunwa ko kuwa tsare waɗanda ake zaluntawa