Gaba Mai-ban Al’ajibi
Shaitan da aljannunsa ba zasu ruɗas da ya jima mutane kuma ba. Jehovah ya jefas da su ko daga sama. (Ru’ya ta Yohanna 12:9) Anan gaba kurkusa fa, Allah zai sake aika gāba da Shaitan da aljannunsa. Cikin wata ru’ya daga Allah, manzo Yohanna ya ce: “Na ga wani mala’ika kuma yana saukowa daga sama, yana riƙe da maƙublin rami mara matuƙa, yana kuwa da babbar sarƙa a hannunsa. Sai ya ɗauki dragon, tsofon maciji, shine Ibelis da Shaitan, ya ɗaure shi har zuwa shekara dubu, ya jefasda shi cikin rami mara matuƙa, ya rufe bakin, ya sa masa hatimi a bisansa, domin kada shi ƙara ruɗin al’ummai, har shekara dubu su cika.” (Ru’ya ta Yohanna 20:1-3) Bayan haka, za a hallakas da Ibelis da dukan aljannunsa har abada.—Ru’ya ta Yohanna 20:10.
Za a kawas da miyagun mutane duka daga duniya kuma.—Zabura 37:9, 10; Luka 13:5.
Matattu Zasu Rayu Kuma!
Bayan an kawas da Shaitan da aljannunsa ko, Jehovah zaya kawo albarkatai dayawa ga mutane. Ai ka tuna da cewa matattun basu da rai, ba su wanzuwa. Yesu ya kamabta mutuwa da barci—barci mai-zurfi da babu yin mafalkai. (Yohanna 11:11-14) Ya yi haka domin ya san da cewa lokaci zata zo da za a tashe waɗanda suke barci cikin mutuwa zuwa rai. Ya ce: “Gama sa’a tana zuwa, inda dukan waɗanda suna cikin kabarbaru[n tuni] zasu . . . fito kuma.”—Yohanna 5:28, 29; gwada da Ayukan Manzanni 24:15.
Za a kodo da su zuwa rai a nan bisa duniya. Maimakon shelar cewa mutane sun mutu fa, za a samu rahotanni masu daɗi game da waɗanda aka komo da su zuwa rai! Dubi farincikinsa a marabci ƙaunatattu daga kabari!
[Hoto a shafi na 28]
Bada jimawa ba za a hana Shaitan da aljannu aiki
[Hoto a shafi na 29]
Matattu zasu dawo zuwa rai a duniya