Darasi na 12
Nuna Daraja ga Rai da Jini
Ina yadda zamu dubi rai? (1) zub da ciki? (1)
Ina yadda Kiristoci zasu nuna cewa sun damu game da lafiya? (2)
Shin ba daidai ba ne a kashe dabbobi? (3)
Ina waɗansu ayuka da basu nuna ladabi ga rai? (4) Minene dokar Allah game da jini? (5)
Ashe wannan ya haɗa da haye jini ma? (6)
1. Jehovah shi ne Tushen rai. Ran dukan abubuwa masu-rai daga wurin Allah ne. (Zabura 36:9) Rai abu mai-tsarki ne ga Allah. Ko ran yaron da ba a haifa ba ko wanda ke cikin uwarsa na da tamani ga Jehovah. Kashe jaririn nan da ganga laifi ne a gaban Allah.—Fitowa 21:22, 23; Zabura 127:3.
2. Kiristoci na gaskiya suna damuwa game da lafiya. Suna tabbata cewa motocinsu da gidajensu basu da abin haɗari. (Kubawar Shari’a 22:8) Bayin Allah ba sua wasa da ransu don ɗan jin daɗi ko tashin rai ba. Saboda haka ba sua rabo cikin wasannin nuna ƙarfi don su ji ma wasu mutane rauni da ganga. Suna guje ma nishaɗi da ke jawo nuna ƙarfi.—Zabura 11:5; Yohanna 13:35.
3. Ran dabba ma abu mai-tsarki ne ga Mahaliccin. Kirista zai iya kashe dabbobi domin tanadar da abinci da tufa ko kuma ya tsare jikinsa daga ciwo da haɗari. (Farawa 3:21; 9:3; Fitowa 21:28) Amma laifi ne a wulakantar da dabbobi ko kashe su don wasanni ko kuwa nishaɗi.—Misalai 12:10.
4. Shan tāba, betel nut, da shan ƙwaya don jin daɗi ba ga Kirista ba ne. Waɗannan ayukan basu da kyau domin (1) suna maida mu bayinsu, (2) suna ɓata jikunanmu, kuma (3) basu da tsabta. (Romawa 6:19; 12:1; 2 Korinthiyawa 7:1) Yana da wuya ƙwarai a denna waɗannan halayen. Amma tilas mu yi haka domin mu gamsad da Jehovah.
5. Jini ma abu mai-tsarki ne a idanun Allah. Allah ya ce kurwa, ko rai, yana cikin jini. Saboda haka cin jini laifi ne. Laifi ne ma cin naman dabba da ba a yanka ba. Idan an shaƙe dabba ko kuwa ya mutu cikin tarko, ba za a ci shi ba. Idan an harɓa shi ne, sai a yanka shi da sauri idan za a ci shi.—Farawa 9:3, 4; Leviticus 17:13, 14; Ayukan Manzanni 15:28, 29.
6. Laifi ne a haye jini? Tuna fa, Jehovah yana bukatar mu hanu daga jini. Wannan yana nufin cewa ba zamu karɓi jinin wasu mutane ko kuwa jinin kanmu da aka yi ajiyansa da ko ƙaƙa. (Ayukan Manzanni 21:25) Saboda haka Kiristoci na gaskiya ba zasu iya yarda da haye jini ba. Zasu iya karɓan wasu irin jinya na asibiti, kamar haye wasu magungunan da ba jini ba a cikin jiki. Suna son su kasance da rai, amma ba zasu yi ƙoƙarin cetas da ransu ta wurin taka dokokin Allah ba.—Matta 16:25.
[Hotuna a shafi na 25]
Don mu gamsad da Allah, tilas ne mu guje ma haye jini, ƙazantattun ayuka, da kuma ɗaukan kasada na babu dalili