Wanene Yesu Kristi?
“MUTANE da yawa da ba Kiristoci ba ne sun yarda cewa Shi babban malami ne mai hikima. Hakika shi ne mutum mafi daraja da ya taɓa rayuwa.” (The World Book Encyclopedia) Wanene “Shi”? Yesu Kristi ne, wanda ya ƙafa Kiristanci. Ka san ko shi wanene? Yana shafan rayuwarka kuwa?
An rubuta abubuwan da suka faru a hidimar Yesu a cikin Littafi Mai Tsarki a cikin littattafan tarihi guda huɗu da ake kira Linjila. Waɗannan labaran gaskiya ne kuwa? Bayan da ya bincika Linjilar, wani sanannen ɗan tarihi Will Durant ya ce: “Idan har mutane marasa ilimi sosai a wani zamani, suka yi tunani suka fito da wani labari game da wani mutum wanda yake da iko da hali mai kyau irin na Yesu kuma wannan labarin ya shafi rayuwar mutane da yawa wanda ya haɗa kan mutane, wannan shi ne babban mu’ujiza da ya fi wanda aka rubuta a Linjila.”
Ga miliyoyin mutane a Gabas da kuma wasu wurare Yesu Kristi mutum ne da babu wanda ya san shi. Za su iya gaskata cewa ya wanzu, amma ba su taɓa tunanin cewa zai iya shafan rayuwarsu ba. Waɗansu suna ganin cewa mai da hankali ga Yesu ba shi da amfani saboda abubuwan da waɗanda suke da’awar cewa su mabiyansa ne suka yi. ‘Sun jefa bam a Nagasaki,’ kamar yadda wasu a ƙasar Japan suke ce wa, ‘birnin da Kiristoci suka fi yawa a ƙasar Japan.’
Amma, za ka ɗora wa likita laifi ne idan marar lafiya ya ƙi shan maganin da likitan ya ce ya sha? A’a. Mutanen Kiristendam sun ƙi bin umurnin da Yesu ya bayar na kawar da matsaloli na yau da kullum. Maimakon ka ƙi Yesu saboda waɗanda suke da’awar cewa su Kiristoci ne, amma ba sa abin umurninsa, me ya sa ba za ka koyi wani abu game da shi ba? Ka karanta Littafi Mai Tsarki ka fahimci ko wanene ainihi Yesu da kuma yadda zai iya canja rayuwarka.
Ƙauna—Shawarar da Ya Bayar
Yesu babban malami ne da ya yi rayuwarsa a Palasɗinu kusan shekaru 2,000 da suka wuce. Ba a san tarihinsa sa’ad da yake yaro sosai ba. (Matta, sura 1 zuwa 2; Luka, sura 1 zuwa 2) Sa’ad da ya kai shekaru 30, Yesu ya soma hidimarsa na “bada shaida ga gaskiya.” (Yohanna 18:37; Luka 3:21-23) Mutane huɗu da suka rubuta tarihin rayuwar Yesu sun mai da hankali ne ga hidimar fage ta shekaru uku da rabi da ya yi a duniya.
A lokacin hidimarsa, Yesu ya ba almajiransa mabuɗin magance matsaloli dabam dabam a rayuwarsu. Menene mabuɗin? Ƙauna ce. A wata sananniyar huɗuba a tarihi da ake kira Huɗuba a Kan Dutse, Yesu ya koya wa almajiransa yadda za su nuna wa ’yan’uwansu ƙauna. Ya ce: “Dukan abu fa iyakar abin da ku ke so mutane su yi maku, ku yi musu hakanan kuma.” (Matta 7:12) Ana kiransa Ƙa’idar Ja-gora. “Mutane” da Yesu ya ambata a nan sun haɗa da abokan gaba. A wannan huɗubar, ya ce: “Ku yi ƙaunar magabtanku, kuma waɗanda su kan tsananta muku, ku yi musu addu’a.” (Matta 5:44) Irin wannan ƙaunar za ta magance yawancin matsalolin da muke fuskanta a yau. Mohandas Gandhi shugaban Indiya ya gaskata da haka. An yi ƙaulinsa yana cewa: “Idan muka yi amfani da koyarwar da Kristi ya yi a wannan Huɗuba ta kan Dutse, da mun magance matsaloli . . . na dukan duniya.” Lalle idan aka yi amfani da koyarwar da Yesu ya yi game da ƙauna za ta magance matsalolin mutane.
Ya Nuna Ƙaunarsa
Yesu ya aikata abin da yake koyarwa. Ya sa bukatun wasu gaba da na sa kuma ya nuna ƙauna. Wata rana, Yesu da almajiransa suna yi wa mutane da yawa wa’azi, ba dama da za su ko ci abinci. Yesu ya ga cewa ya kamata almajiransa su “huta kaɗan,” sai suka je inda ba kowa. Amma mutanen suka je suna jiransu. Idan kai ne Yesu me za ka yi? Yesu “ya ji juyayinsu” sai “ya fara koya masu abu dayawa.” (Markus 6:30-34) Irin wannan juyayin ya motsa shi ya taimaki mutane.
Abin da Yesu ya yi don mutane su amfana ba a kan koyarwa ta ruhaniya ba ne kawai. Ya kuma ba su taimako na zahiri. Alal misali, ya ciyar da maza 5,000 (ban da mata da yara) waɗanda suke sauraransa har zuwa yamma. A wani lokaci kuma ya ciyar da mutane 4,000. Da farko, ya yi amfani da burodi biyar da kifaye biyu daga baya kuma ya yi amfani da burodi bakwai da kifaye kaɗan. (Matta 14:14-21; 15:32-38; Markus 6:35-44; 8:1-9) Hakika, shi mai yin mu’ujiza ne.
Yesu kuma ya warƙar da marasa lafiya. Ya warƙar da makafi, guragu, kutare, da kuma kurame. Ya kuma ta da matattu! (Luka 7:22; Yohanna 11:30-45) Wani kuturu ya roƙe shi: “Idan ka yarda, kana da iko ka tsarkake ni.” Menene Yesu ya yi? “Ya miƙa hannunsa, ya taɓa shi, ya ce masa, Na yarda; ka tsarkaka.” (Markus 1:40, 41) Muradi mai ƙarfi ya motsa Yesu ya taimake su. Ta wajen wannan mu’ujizai, ya nuna ƙaunarsa ga waɗanda suke wahala.
Yana da wuya a gaskata da hakan? Amma Yesu ya yi yawancin mu’ujizan a inda mutane suke. Har ma ’yan hamayya da suke nemansa da a kowane lokaci, ba za su iya cewa bai yi mu’ujiza ba. (Yohanna 9:1-34) Saboda mu’ujizar da ya yi suna da manufa. Mu’ujizan sun taimaki mutane su fahimci cewa Allah ne ya aiko Yesu.—Yohanna 6:14.
Ta wajen yin la’akari da koyarwar Yesu da kuma rayuwarsa za su sa mu ƙaunace shi kuma su motsa mu mu yi koyi da ƙaunarsa. Duk da haka, ba ta wannan hanyar ba ce kawai Yesu zai shafi rayuwarmu ba. Shi ba babban malami ba ne wanda yake koyar da ƙauna kawai. Ya nuna cewa shi haifaffen Ɗan Allah ne kafin ya zama mutum. (Yohanna 1:14; 3:16; 8:58; 17:5; 1 Yohanna 4:9) Ya kuma zama mutum, wanda hakan ya sa ya kasance mai muhimmanci a gare mu. Littafi Mai tsarki ya nuna cewa an ta da Yesu daga matattu kuma an naɗa shi Sarki na Mulkin Allah. (Ru’ya ta Yohanna 11:15) Yesu ya ce: “Rai na har abada ke nan, su san ka, Allah makaɗaici mai-gaskiya, da shi kuma wanda ka aiko, Yesu Kristi.” (Yohanna 17:3; 20:31) Hakika, sanin Yesu Kristi zai iya kawo rayuwa marar iyaka a aljanna! Ta yaya hakan zai yiwu? Ka yi koyi da Yesu ka ga yadda “ƙaunar Kristi” ta motsa mu mu bi gurbinsa. (2 Korinthiyawa 5:14) Shaidun Jehobah za su yi farin cikin taimaka maka.—Yohanna 13:34, 35.
Sai dai ko an ba da alama, dukan ayoyin da aka yi amfani da su daga Litafi Mai Tsarki ne.