Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • jt pp. 6-11
  • Ƙaruwarsu da Bunƙasarsu ta Zamani

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ƙaruwarsu da Bunƙasarsu ta Zamani
  • Shaidun Jehovah Su Wanene ne Su
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • SHEKARA TA 1914
  • NASARORI A KOTU
  • TSARIN KOYARWA TA MUSAMMAN
  • AN FAƊAƊA MAƊABA’A
  • MANYAN TARO A DUKAN DUNIYA
  • Hanyoyin Yin Wa’azi​—Yin Amfani da Hanyoyi Dabam-dabam Wajen Yin Wa’azi
    Mulkin Allah Yana Sarauta!
Shaidun Jehovah Su Wanene ne Su
jt pp. 6-11

Ƙaruwarsu da Bunƙasarsu ta Zamani

Tarihin zamani na Shaidun Jehovah ya soma fiye da shekaru ɗari da suka shige. A farkon shekara ta 1870 rukunin nazarin Littafi Mai Tsarki da ba a san shi ba ya fara a Allegheny, Pennsylvania, U.S.A., wadda yanzu ta zama sashen Pittsburgh. Charles Taze Russell ne ya ba da ƙwazo a rukunin. A Yuli 1879, jaridar Zion’s Watch Tower and Herald of Christ’s Presence ta farko ta bayyana. A shekara ta 1880 ikilisiyoyi da yawa sun bazu daga wannan ƙaramin rukunin nazarin Littafi Mai Tsarki zuwa jihohi na kusa. A shekara ta 1881 aka kafa Zion’s Watch Tower Tract Society, kuma a shekara ta 1884 Russell ya zama shugabanta. Daga baya aka canja sunan Society zuwa Watch Tower Bible and Tract Society. Mutane da yawa suna yin wa’azi daga gida zuwa gida suna ba da adabi na Littafi Mai Tsarki. Mutane hamsin ne suke yin wannan aiki na cikakken lokaci a shekara ta 1888—yanzu matsakaicin adadin masu aiki na cikakken lokaci a yau sun kai kusan 700,000 a dukan duniya.

A shekara ta 1909, aikin ya kai dukan duniya, kuma aka ƙaurar da hedkwatar Society zuwa wurin da take yanzu a Brooklyn, New York. Ana buga huɗuba a cikin jaridu, kuma a shekara ta 1913 ana yin haka a harsuna huɗu a cikin dubban jaridu a United States, Canada, da Turai. An rarraba littattafai, ƙasidu, da warƙoƙi wajen ɗarurruwan miliyoyi.

A shekara ta 1912 aka soma aiki a kan “Photo-Drama of Creation.” Aka shirya silima, da ta nuna farawar halitta zuwa ƙarshen Sarautar Kristi ta Shekara Dubu. An fara nunawa a shekara ta 1914, mutane 35,000 suna kallonta kullum. Rukunin mutane ne suka kawo cin gaba wajen hotuna masu motsi.

SHEKARA TA 1914

Lokaci na musamman yana matsowa kusa. A shekara ta 1876 ɗalibin Littafi Mai Tsarki Charles Taze Russell ya ba da gudummawar talifi “Lokatan Al’ummai: Yaushe Suka Ƙare?” ga Bible Examiner, da aka buga a Brooklyn, New York, wanda shafi na 27 fitar Oktoba ya ce, “lokatai bakwai za su ƙare a A.Z. 1914.” Lokatan Al’ummai lokatai ne da wani fassara na Littafi Mai Tsarki ya kira su “zamanan Al’ummai.” (Luka 21:21) Ba dukan abin da ake tsammani za su faru a shekara ta 1914 ne suka faru ba, amma ya kawo ƙarshen Lokatan Al’ummai, shekara ce ta musamman. ’Yan tarihi da ’yan sharhi da yawa sun yarda cewa shekara ta 1914 lokaci ne na musamman a tarihin ’yan Adam. Ga wasu misalai da aka ɗauko da suka kwatanta hakan:

“Shekara ta ƙarshe da take yadda ‘ta kamata’ ita ce 1913, shekarar da ta zo kafin a fara Yaƙin Duniya na I.”—Talifi a cikin Times-Herald, Washington, D.C., 13 ga Maris, 1949.

“ ’Yan tarihi sun ga shekara 75 da ya soma daga 1914 zuwa 1989, da aka yi yaƙoƙin duniya biyu da yaƙin wutar ƙaiƙayi, lokaci ne na musamman da ƙasashe da yawa suke yaƙi, wasu suna gamawa ko kuma shirin yin yaƙi.”—The New York Times, 7 ga Mayu, 1995.

“Hakika duk duniya ta halaka a Yaƙin Duniya na I kuma har ila, ba mu san abin da ya sa ba. Kafin lokacin, mutane suna tunani cewa lokacin da kome zai yi daidai ya kusa. Akwai salama da ni’ima. Sai komi ya halaka. Tun lokacin ba ma cin gaba . . . An kashe mutane a cikin wannan ƙarni fiye da duka cikin tarihi.”—Dokta Walker Percy, American Medical News, 21 ga Nuwamba, 1977.

Fiye da shekara 50 bayan shekara ta 1914, wani tauraron gwamnatin Jamus Konrad Adenauer ya rubuta: “Kwanciyar rai da salama sun ɓace daga rayuwar mutane tun a 1914.”—The West Parker, Cleveland, Ohio, 20 ga Janairu, 1966.

Shugaban Society na farko C. T. Russell ya mutu a shekara ta 1916 kuma a shekara da ta biyo baya Joseph F. Rutherford ya gaje shi. Abubuwa da yawa suka canja. Aka fara buga jarida mai bin Hasumiyar Tsaro da aka kira The Golden Age. (Yanzu ana kiranta Awake!, ana buga fiye da 20,000,000 cikin sama da harsuna 80.) Aka soma yin wa’azi na ƙofa zuwa ƙofa sosai. Domin su kasance dabam daga ɗarikar Kiristendam, a shekara ta 1931 waɗannan Kiristoci suka karɓi suna Shaidun Jehovah. Wannan sunan ya samo asali ne daga Ishaya 43:10-12.

An yi amfani da rediyo sosai a shekara ta 1920 da ta 1930. A shekara ta 1933 Society suna amfani da tashoshin rediyo 403 don su sanar da laccoci na Littafi Mai Tsarki. Daga baya, aka canja yin amfani da rediyo, Shaidu suka soma amfani da garmaho da laccoci na Littafi Mai Tsarki da ke kan faifai a ziyara ta gida zuwa gida. Sai a soma nazarin Littafi Mai Tsarki da kowa da ya nuna marmari a gaskiyar Littafi Mai Tsarki.

NASARORI A KOTU

A shekara ta 1930 da ta 1940 aka kama Shaidu da yawa domin yin wannan aiki, aka yi shari’a don a tsare ’yancin magana, maɗaba’a, taro, da kuma addini. A cikin United States, afil da aka yi a ƙananan kotuna ya sa Shaidu su ci nasara a shari’a 43 a Babban Kotun United States. Hakanan, an yi shari’a ta gaskiya a manyan kotuna a wasu ƙasashe. Game da waɗannan nasarori a kotu, Shehun Malami C. S. Braden, a cikin littafinsa These Also Believe, ya ce game da Shaidun: “Sun ba da taimako da babu irinsa ga dimokuraɗiyya ta faɗā da suka yi su tsare ’yancinsu, sun yi ƙoƙari sun tsare ’yancin kowanne ƙaramin rukuni a Amirka.”

TSARIN KOYARWA TA MUSAMMAN

J. F. Rutherford ya mutu a shekara ta 1942 kuma N. H. Knorr ya gaje shi. Tsarin koyarwa da aka haɗa hannu aka shirya ya soma. A shekara ta 1943 aka kafa makarantar koyarwa ta musamman da aka kira ta Watchtower Bible School of Gilead (Makarantar Littafi Mai Tsarki ta Gilead) don masu wa’azi a ƙasashen waje. Daga wannan lokacin, waɗanda suka sauke karatu daga wannan makarantar an aika da su zuwa ƙasashe a duka duniya. An sami sabbin ikilisiyoyi a ƙasashen da a dā babu, kuma rassa da aka kafa a duka duniya yanzu sun fi 100. A wasu lokatai, dattiɓan ikilisiya, masu aiki a rassa, waɗanda suke aikin wa’azi na cikakken lokaci (majagaba) suna samun koyarwa ta musamman a makaranta da aka kafa musu. An ba masu hidima koyarwa dabam dabam ta musamman a makarantar da ake yi a Patterson, New York.

N. H. Knorr ya mutu a shekara ta 1977. Ɗaya cikin canji na ƙarshe da ya yi kafin ya mutu shi ne ƙara waɗanda suke cikin Hukumar Mulki da ke a hedkwatar dukan duniya a Brooklyn. A shekara ta 1976 aka raba ayyuka aka ba kwamiti dabam dabam da suke Hukumar Mulkin, waɗanda sun manyanta suna aikin hidima shekaru da yawa.

AN FAƊAƊA MAƊABA’A

Tarihin Shaidun Jehovah na zamani yana cike da aukuwa na ban sha’awa. Daga ƙaramin rukunin nazarin Littafi Mai Tsarki a Pennsylvania can a shekara ta 1870, Shaidun sun ƙaru zuwa ikilisiyoyi 90,000 a dukan duniya a shekara ta 2000. Da farko ana buga duk littattafai a waje, amma a shekara ta 1920, Shaidun sun buga wasu littattafai a wasu gine-gine da suka yi hayarsu. Amma tun daga shekara ta 1927 ana buga littattafai a bene mai hawa takwas da ke Brooklyn, New York, Watchtower Bible and Tract Society of New York, Inc., ne suke da wannan. Yanzu an faɗaɗa wannan zuwa wasu gine-gine na ma’aikata da kuma ofishi mai girma. Akwai ƙarin gidaje a kusa da Brooklyn inda masu hidima da suke aiki da maɗaba’o’in za su zauna. Ƙari ga haka, ana yin aikin gona kuma ana buga littattafai kusa da Wallkill, a arewacin New York. A wurin ana buga jaridun Hasumiyar Tsaro da Awake! kuma ana noman abinci don masu aiki a wurare dabam dabam. Kowanne mai aiki yana karɓan ɗan guzuri kowane wata don ya biya bukatu na nan da nan.

MANYAN TARO A DUKAN DUNIYA

A shekara ta 1893 an yi babban taro na farko a Chicago Illinois ta U.S.A. Mutane 360 ne suka halarta, kuma an yi wa sababbi 70 baftisma. An yi babban taro na ƙarshe na dukan duniya a Birnin New York a shekara ta 1958. An yi amfani da Babban Filin Wasa na Yankee da kuma Filin Sukuwa da suke wajen a dā. Ƙolin waɗanda suka halarta 253,922 ne; sababbi 7,136 aka yi wa baftisma. Tun daga lokacin ana manyan taro na dukan duniya a ƙasashe da yawa. Duka duka, irin wannan manyan taron za su kai dubbai a ƙasashe gewaye da duniya.

[Bayanin da ke shafi na 8]

Aikin ba da kashedi ga ’yancin mutane

[Hoto a shafi na 6]

“Hasumiyar Tsaro,” daga 6,000 a yare ɗaya zuwa fiye da 22,000,000 a sama da harsuna 132

[Hoto a shafi na 7]

Lokaci na musamman a tarihin ’yan Adam

[Hoto a shafi na 10]

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba