Za Ka So Ka Ƙara Sanin Littafi Mai Tsarki?
Me Ya Sa Za Ka Karanta Littafi Mai Tsarki?
LITTAFI MAI TSARKI ba kamar wasu littattafai ba ne—yana ɗauke da umurni mai kyau daga Allah. (1 Tassalunikawa 2:13) Idan ka yi amfani da abin da Littafi Mai Tsarki yake koyarwa, za ka amfana ƙwarai. Za ka ƙara ƙaunar Allah kuma za ka kusaci Mai ba da “kowacce kyakkyawar baiwa da kowacce cikakkiyar kyauta.” (Yaƙub 1:17) Za ka san yadda za ka kusace shi cikin addu’a. A lokatai na wahala, Allah zai taimaka maka. Idan ka daidaita rayuwarka da mizanan da aka kafa cikin Littafi Mai Tsarki, Allah zai ba ka rai madawwami.—Romawa 6:23.
Littafi Mai Tsarki na ɗauke da gaskiyar da ke wayarwa. Waɗanda suka samu sanin Littafi Mai Tsarki sun yantu daga rashin ganewa da ke mallakar rayuwar miliyoyin mutane. Alal misali, sanin gaskiyar game da abin da ke faruwa in mun mutu yana ’yantar da mu daga tsoron cewa matattu za su yi mana lahani ko kuma danginmu da abokananmu da suka mutu suna shan azaba. (Ezekiel 18:4) Abin da Littafi Mai Tsarki ya koyar game da tashin matattu na ta’azantar da waɗanda suka yi rashin wanda suke ƙauna. (Yohanna 11:25) Sanin gaskiya game da miyagun mala’iku yana sa mu yi hattara domin haɗarin sihiri kuma yana taimaka mana mu fahimci abin da ya sa ake wahala da yawa a duniya.
Ƙa’idodin ibada cikin Littafi Mai Tsarki suna koya mana mu yi rayuwa a hanyar da zai kawo mana amfani na jiki. Alal misali, zama “mai-kāmewa” na kawo lafiyar jiki. (1 Timothawus 3:2) Ta ‘tsarkake kanmu daga dukan ƙazamtar jiki da ta ruhu,’ muna guje wa cutar da kanmu. (2 Korinthiyawa 7:1) Yin amfani da gargaɗi da ke cikin Littafi Mai Tsarki zai sa mu samu farin ciki a cikin aure kuma mu daraja kanmu.—1 Korinthiyawa 6:18.
Idan ka yi amfani da Kalmar Allah, za ka zama mutum mai farin ciki. Sanin Littafi Mai Tsarki na taimaka mana mu samu kwanciyar hankali da wadatar zuci kuma yana ba mu bege. Yana taimaka mana mu koya halaye masu kyau kamar su juyayi, ƙauna, farin ciki, salama, alheri, da bangaskiya. (Galatiyawa 5:22, 23; Afisawa 4:24, 32) Irin waɗannan halaye na taimaka mana mu zama miji ko mata, uba ko uwa, ɗa ko ’ya na kirki.
Ka taɓa tunani game da abin da ke zuwa nan gaba? Annabce-annabcen Littafi Mai Tsarki na nuna mana cewa muna zama a lokaci na ƙarshe. Waɗannan annabce-annabce ba su kwatanta yanayin duniyar yau ba kawai amma kuma sun nuna cewa jim kaɗan Allah zai juya duniya zuwa aljanna.—Ru’ya ta Yohanna 21:3, 4.
Taimako don Fahimtar Littafi Mai Tsarki
Wataƙila ka yi ƙoƙari ka karanta Littafi Mai Tsarki ka iske shi da wuyar fahimtawa. Mai yiwuwa ba ka san inda za ka duba cikin Littafi Mai Tsarki ba don ka sami amsoshin tambayoyinka. Idan haka ne, ai kuna nan da yawa. Dukanmu muna bukatar taimako mu fahimci Kalmar Allah. Shaidun Jehovah, a wasu ƙasashe 235, suna tanadin koyarwa ta Littafi Mai Tsarki kyauta ga miliyoyin mutane. Za su yi farin ciki su taimake ka kai ma.
Da ma, ya fi kyau a yi nazarin Littafi Mai Tsarki bi-da-bi, somawa da muhimman koyarwar. (Ibraniyawa 6:1) Yayin da ka ci gaba, za ka iya cin “abinci mai-ƙarfi”—wato, gaskiya masu zurfi. (Ibraniyawa 5:14) Littafi Mai Tsarki ne tushen. Littattafai na Littafi Mai Tsarki, kamar su mujallar nan Minene Allah ke Bukata Daga Garemu?, suna iya taimaka maka ka fahimci ayoyin Nassi game da batutuwa dabam dabam.
Kana Shirye Ka Ba da Lokaci Kowanne Mako don Ka Fahimci Littafi Mai Tsarki?
Za a iya shirya yin nazari a lokaci da kuma wuri da ka ke so. Mutane da yawa sun yi nazari a gidansu. Wasu ma sun yi nazari ta amfani da tarho. Nazarin ba kamar na aji ba ne da mutane da yawa, tsari ne wanda dominka ne daidai da yanayinka, daidai bisa saninka da iliminka. Ba a ba da jarrabawa, kuma ba za a ba ka kunya ba. Za a amsa tambayoyinka na Littafi Mai Tsarki, kuma za ka koyi yadda za ka kusaci Allah.
Ba ka bukatar ka biya kuɗi domin wannan nazari na Littafi Mai Tsarki. (Matta 10:8) Ana ba da shi kyauta ga mutane na dukan addinai da waɗanda ba sa yin kowanne addini amma waɗanda da gaske suna son su ƙara saninsu na Kalmar Allah.
Su waye za su iya kasancewa cikin tattaunawar? Dukan iyalinka. Abokai da ka ke son ka gayyace su za su bi ka. Ko kuma kai kaɗai, idan ka fi son hakan.
Mutane da yawa suna keɓe awa guda kowanne mako don nazarin Littafi Mai Tsarki. Idan ka ba da ƙarin lokaci ko kuma lokaci kaɗan ka ke da shi kowanne mako, Shaidun za su ba da kansu su taimake ka.
Gayyata don Koyo
Muna gayyatarka ka tuntuɓi Shaidun Jehovah. Hanya ɗaya da za ka yi wannan ita ce ta rubuta wasiƙa zuwa ga adireshi na ƙasan nan. Za a shirya wani ya yi nazarin Littafi Mai Tsarki na gida da kai kyauta.
Sai dai ko an nuna alama, dukan ayoyin da aka yi amfani da su daga Litafi Mai-Tsarki ne kuma an yi amfani da harufan zamani.