Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • cl babi na 17 pp. 169-178
  • “Ina Misalin Zurfin . . . Hikimar Allah!”

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • “Ina Misalin Zurfin . . . Hikimar Allah!”
  • Ka Kusaci Jehobah
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Mece ce Hikima ta Allah
  • Tabbacin Hikima ta Allah
  • Hikima da Ta Gabaci Duniya
  • Jehobah Ne “Kaɗai Mai Hikima”
  • Hikima Tana Kira da Babban Murya
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2022
  • “Hikima Mai-Fitowa Daga Bisa” Tana Aiki Kuwa A Rayuwarka?
    Ka Kusaci Jehobah
  • “Ga Shi, Wannan Allahnmu Ne”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2003
Ka Kusaci Jehobah
cl babi na 17 pp. 169-178
Wasu agwagi suna firewa.

BABI NA 17

“Ina Misalin Zurfin . . . Hikimar Allah!”

1, 2. Mene ne nufin Jehobah ga rana ta bakwai, kuma ta yaya aka gwada hikimar Allah a farkon rana ta bakwan?

AN HALAKA! Mutum, ɗaukaka ta rana ta shida ta halitta, farat ɗaya ya faɗo daga sama zuwa ƙasa. Jehobah ya furta cewa “dukan abin da ya yi,” har da mutane, “yana da kyau sosai.” (Farawa 1:31) Amma a farkon kwana ta bakwai, Adamu da Hauwa’u suka zaɓi su bi Shaiɗan su yi tawaye. Suka faɗa cikin zunubi, da ajizanci, da kuma mutuwa.

2 Wataƙila ya bayyana kamar dai nufin Jehobah ga rana ta bakwai ta kauce a hanya ke nan babu bege. Wannan ranar, kamar ranaku shida da suka gabace ta, za ta kasance da tsawon shekaru dubbai. Jehobah ya riga ya ce da ita tsarkakkiya, kuma a ƙarshe zai ga dukan duniya ta zama aljanna tana cike da kamiltacciyar iyalin ’yan Adam. (Farawa 1:28; 2:3) Amma bayan tawaye na bala’i, ta yaya irin wannan abu zai faru? Mene ne Allah zai yi? A nan an gwada hikimar Jehobah ƙwarai—wataƙila gwaji mafi girma.

3, 4. (a) Me ya sa martanin Jehobah ga tawaye a Adnin misali ne mai ban tsoro na hikimarsa? (b) Tawali’u zai motsa mu mu tuna da wace gaskiya sa’ad da muke nazarin hikimar Jehobah?

3 Jehobah ya mai da martani babu ɓata lokaci. Ya yanke hukunci ga ’yan tawayen na Adnin, kuma a wannan lokacin, ya ba da ɗan bayani game da wani abu mai ban mamaki: nufinsa ya gyara aibi da suka jawo. (Farawa 3:15) Nufin Jehobah mai hangar nesa ya miƙe daga Adnin cikin dukan shekaru dubbai na tarihin mutane zuwa gaba, gaba can da nisa. Ga shi mafi kyau ne ƙwarai marar wuya, duk da haka yana cike da hikima da mai karanta Littafi Mai Tsarki zai yi amfani da yawancin rayuwarsa a yin nazari da kuma yin bimbini a kansa. Bugu da ƙari, nufin Jehobah yana da cikakken tabbacin yin nasara. Zai kawo ƙarshen dukan mugunta, zunubi, da kuma mutuwa. Zai kai amintattun mutane zuwa kamilci. Dukan wannan zai faru kafin rana ta bakwan ta ƙare, saboda, duk abin da ya faru, Jehobah zai cika nufinsa ga duniya da kuma ’yan Adam a kan lokaci ɗaya rak!

4 Irin wannan hikimar tana da ban tsoro, ko ba haka ba? Manzo Bulus ya motsa ya rubuta: “Ina misalin zurfin yawan hikimar Allah!” (Romawa 11:33) Sa’ad da muke nazarin fasaloli dabam dabam na wannan hikimar Allah, ya kamata tawali’u ya motsa mu mu tuna wata muhimmiyar gaskiya—cewa, dukan ƙoƙarinmu, sama saman wannan hikima ne mai yawa na Jehobah za mu iya tonewa. (Ayuba 26:14) Da farko, bari mu ba da ma’anar wannan hali mai ban tsoro.

Mece ce Hikima ta Allah

5, 6. Wace nasaba ce take tsakanin ilimi da hikima, kuma yaya yawar ilimin Jehobah yake?

5 Hikima ba daidai take da ilimi ba. Kwamfuta ta iya riƙe ilimi mai yawa, amma zai yi wuya a ce wani ya kira wannan inji cewa mai hikima ne. Duk da haka, ilimi da hikima suna da nasaba. (Karin Magana 10:14) Alal misali, idan kana bukatar shawara mai kyau game da magance ciwo mai tsanani, za ka je ne wajen wanda ba shi da ilimi sosai game da magani? Da ƙyar! Saboda haka, ilimi wajibi ne ga hikima ta gaskiya.

6 Jehobah yana da ilimi marar iyaka. Tun da shi ne “Sarkin” zamanai, shi ne kaɗai yake raye har abada. (Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 15:3) Kuma a dukan waɗannan shekaru aru-aru, yana sane da kome. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ba wani abu a dukan halitta wanda yake a ɓoye ga Allah. Kome da kome yana nan a buɗe, a fili kuma, a gaban idonsa. Shi ne kuma wanda za mu ba shi lissafi game da rayuwarmu.” (Ibraniyawa 4:13; Karin Magana 15:3) Tun da shi ne Mahalicci, Jehobah yana da cikakken ilimin abin da ya halitta, kuma ya lura da dukan ayyukan ’yan Adam tun daga farko. Yana bincika zuciyar kowane mutum, baya ƙetare ko ɗaya. (1 Tarihi 28:9) Tun da ya halicce mu da ’yancin zaɓan abin da muke so, yana yin farin ciki sa’ad da ya ga muna zaɓan abin da yake da kyau a rayuwa. Tun da “Mai jin addu’o’i” ne, yana sauraron addu’o’i masu yawa a lokaci ɗaya! (Zabura 65:2) Ba sai an faɗa ba, Jehobah ba ya mantuwa.

7, 8. Ta yaya Jehobah ya nuna fahimta, fahimi, da kuma hikima?

7 Jehobah yana da fiye da ilimi. Yana ganin yadda gaskiya take da nasaba kuma ya gano dukan batun ta wajen bayani masu yawa. Zai bincika kuma ya hukunta, ya bambance tsakanin mai kyau da marar kyau, mai muhimmanci da marar muhimmanci. Bugu da ƙari, yana gani fiye da sama sama kawai, yana ganin cikin zuciya. (1 Sama’ila 16:7) Saboda haka, Jehobah yana da fahimta da fahimin abubuwa da suka fi ilimi. Amma duk da haka hikima ta fi su duka.

8 Hikima tana nufin yin amfani da ilimi, fahimi, da kuma fahimta domin a samu sakamakon da ake bukata. Wasu kalmomi na asali da aka fassara su “hikima” a zahiri suna nufin “ainihin aiki” ko “hikima wajen aiki.” Saboda haka, hikimar Jehobah ba maganar baki ba ce kawai. Tana aiki, kuma tana nasara. Yin amfani da zurfin iliminsa da kuma fahimtarsa, ko da yaushe Jehobah yana yanke shawara mafi kyau, yana yin su ta hanya mafi kyau da za a yi tunaninta. Wannan ita ce hikima ta gaskiya! Jehobah ya nuna gaskiyar maganar Yesu: “Ana gane hikimar Allah a ayyukanta.” (Matiyu 11:19) Ayyukansa a dukan sararin sama suna ba da shaida mai ƙarfi game da hikimarsa.

Tabbacin Hikima ta Allah

9, 10. (a) Jehobah ya nuna wace irin hikima, kuma ta yaya ya nuna wannan? (b) Ta yaya ƙwai na naman jiki ya ba da tabbacin hikima ta Jehobah?

9 Ka taɓa mamakin hikimar mai aikin hannu da ya yi wani abu mai kyau da yake aiki daidai? Irin wannan hikima ce mai ban sha’awa. (Fitowa 31:1-3) Jehobah da kansa shi ne Tushen hikima kuma shi ne Mafi Girma wajen hikima. Sarki Dauda ya ce game da Jehobah: “Ina yabonka, domin yadda ka harhaɗa ni abin tsoro da ban mamaki ne. Ayyukanka masu ban mamaki ne, na san da wannan sosai.” (Zabura 139:14) Hakika, yayin da mun koyi game da jikin mutum, hakanan za mu ga mun tsorata da hikima ta Jehobah.

10 Alal misali: Rayuwarka ta fara da ƙwaya ɗaya na ƙwai na naman jiki—ƙwan maniyyi daga mamarka, ya haɗu da na maniyyin babanka. Ba da daɗewa ba, wannan ƙwan ya fara rarrabuwa. Kai, da ka fito a ƙarshe, ƙwayaye tiriliyan 100 suka yi ka. Ƙanana ne ’yan mitsitsi. Kan allura zai ɗauki kusan 10,000 masu matsakaicin girma. Duk da haka, kai halitta ce na ban mamaki. Ƙwan ya fi dukan wani inji da mutum ya gina ko kuma masana’anta. ’Yan kimiyya sun ce ƙwan kamar birni ne mai ganuwa—mai ƙofa da mafita, tsarin sifiri, tsarin sadarwa, tushen lantarki, masana’anta, tsarin zubar da juji, ’yan tsaro, har ma da gwamnatin tarayya a cikin cibiyarsa. Bugu da ƙari, ƙwan zai iya yin wani kamarsa a cikin ’yan awoyi kaɗan!

11, 12. (a) Mene ne yake saka ƙwai daga ɗan tayi su bambanta, kuma ta yaya wannan ya jitu da Zabura 139:16? (b) A wace hanya ce ƙwaƙwalwar mutum ta nuna cewa yadda ‘aka yi mu abin mamaki ne’?

11 Hakika, ba dukan ƙwan naman jiki ba ne suke daidai da juna. Sa’ad da ƙwan ɗan-tayi ya ci gaba da rarrabuwa, suna ɗaukan matsayi dabam dabam. Wasu za su zama ƙwai masu gina jijiyoyi; wasu na ƙashi, tsoka, jini, ko kuma na ido. Dukan waɗannan bambancin an tsara su cikin “laburare” na ƙwan, wato DNA. Abin farin ciki, an hure Dauda ya ce game da Jehobah: “Idanunka sun ga gaɓoɓin jikina kafin su cika. A cikin littafinka an rubuta.”—Zabura 139:16.

12 Waɗansu gaɓoɓin jiki suna da wuyar ganewa ƙwarai. Alal misali, ka yi la’akari da ƙwaƙwalwar mutum. Wasu sun kira ta, abin da ta fi wuya da aka gano a dukan sararin sama. Tana ɗauke da ƙwayayen jijiyoyi wajen biliyan 100—da yawa suna kamar taurari a damin taurari namu. Kowanne cikin waɗannan ƙwayayen yana yin saiwa mai dubban nasaba da wasu ƙwayayen. ’Yan kimiyya sun ce ƙwaƙwalwar mutum za ta iya ɗaukan dukan bayani da suke cikin dukan laburare na duniya, suka ce wajen ajiyarta, da gaske, babu magwaji. Duk da shekaru da yawa na nazari a kan wannan abin da ‘aka yi mai ban mamaki,’ ’yan kimiyya sun yarda cewa ba za su taɓa fahimtar yadda take aiki sosai ba.

13, 14. (a) Ta yaya tururuwa da kuma wasu halittu suka nuna cewa suna da “hikima sosai,” kuma mene ne wannan ya koya mana game da Mahalicci? (b) Me ya sa za mu ce irin halitta kamar su saƙar gizo an yi su “cikin hikima”?

13 Duk da haka, mutane misali ne ɗaya kawai na hikimar Jehobah ta halitta. Zabura 104:24 ta ce: “Ya Yahweh, ina misalin yawan ayyukanka, cikin hikima ka yi su duka! Duniya cike take da halittunka.” Hikimar Jehobah tana bayyane a dukan halitta da suka kewaye mu. Alal misali, tururuwa, tana da “hikima sosai.” (Karin Magana 30:24) Hakika, maƙauratar tururuwa an tsara su ƙwarai. Wasu maƙauratar tururuwa suna gadi, wasu suna yin gida, wasu kuma suna samun abinci daga wasu ƙananan ƙwari da ke shan furanni kamar waɗannan garke ne. Wasu tururuwa suna ayyuka kamar manoma, suna shuki kuma suna girbe “iri” na naman ƙwari. Halittu da yawa an tsara su su yi abubuwa masu ban mamaki ta azancinsu. Ƙuda yana iya jujjuyawa yadda jirgin da mutum ya yi ba zai iya ba. Tsuntsaye masu ƙaura suna tafiya ta wajen bin taurari, ta wajen maganaɗiso na duniya, ko kuma ta wajen wasu irin taswira ta cikin duniya. Masana ƙwayoyin rai sun yi shekaru suna nazari a kan waɗannan halaye masu ban mamaki da aka tsara a cikin waɗannan halittun. Hakika kuwa Allah Mai Tsara waɗannan abubuwa yana da hikima!

14 ’Yan kimiyya sun koyi abubuwa da yawa daga hikimar halitta ta Jehobah. Har ma da sashen injiniyoyi da ake kira kimiyyar kwaikwayo, da take neman ta yi kwaikwayon dukan abin da suke gani a halitta. Alal misali, wataƙila za ka zuba wa saƙar gizo-gizo idanu kana mamakin kyanta. Amma injiniya yana gani abin ban mamaki ne kawai na zane-zane. Wasu zare da kamar ba su da ƙarfi sun fi ƙarfe ƙarfi, sun fi ma zaren da ake rigar kāre harsashi da shi. Yaya ƙarfinsu? Ka yi tunani an faɗaɗa saƙar gizo har sai da ta kai girman taru. Irin wannan tarun zai iya kama jirgin sama na fasinja da yake cikin gudu! Hakika, Jehobah ya yi dukan waɗannan abubuwa ‘cikin hikima.’

Hotuna: Hikimar Jehobah a halitta. 1. Gizo-gizo. 2. Cinnaku suna dauke da ganye. 3. Wasu agwagi suna firewa.

Wa ya tsara halittun duniya su kasance da “hikima”?

Hikima da Ta Gabaci Duniya

15, 16. (a) Damin taurari suna ba da wane tabbaci ne na hikimar Jehobah? (b) Ta yaya matsayin Jehobah na Kwamanda Mafi Girma bisa mala’iku babu iyaka ya ba da tabbacin hikimar wannan Mai Gudanarwa?

15 Hikimar Jehobah ta bayyana a cikin dukan ayyukansa a dukan sararin sama. Sama mai taurari da muka tattauna da ɗan dama a Babi na 5 ba kawai suna watse ba ne a sama. Godiya ta tabbata ga hikimar “ƙa’idodin sammai” na Jehobah, taurarin an tsara su dami dami, kuma damin aka tara su cikin manyan dami, kuma aka tara manyan a cikin dami mafiya girma. (Ayuba 38:33) Babu mamaki da Jehobah ya kira waɗannan halittun runduna! (Ishaya 40:26) Har yanzu da wata runduna kuma da ta bayyana hikimar Jehobah sosai.

16 Kamar yadda muka lura a Babi na 4, an kira Allah ‘Jehobah Mai Girma’ domin matsayinsa na Kwamanda Mafi Girma na rundunar miliyoyin halittu na ruhu. Wannan tabbaci ne na ikon Jehobah. Amma ta yaya wannan ya shafi hikimarsa? Ka lura: Jehobah da Yesu ba sa zaman banza. (Yohanna 5:17) Daidai ne da ya nuna cewa, mala’iku masu yi wa Mai Girma Duka hidima suna aiki kullum. Kuma ka tuna cewa sun fi mutane, sun fi mutane fahimi da kuma iko. (Ibraniyawa 1:7; 2:7) Duk da haka, Jehobah ya saka dukan waɗannan mala’iku aiki, suna aiki mai gamsarwa da farin ciki—suna “aikata nufinsa” kuma suna “biyayya da maganarsa”—na biliyoyin shekaru. (Zabura 103:20, 21) Lallai hikimar Mai Gudanar da wannan yana da ban tsoro!

Jehobah Ne “Kaɗai Mai Hikima”

17, 18. Me ya sa Littafi Mai Tsarki ya ce Jehobah ne “kaɗai mai hikima,” kuma me ya sa hikimarsa za ta tsoratar da mu?

17 Bisa ga waɗannan tabbacin, abin mamaki ne da Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa hikimar Jehobah babu na biyunta? Alal misali, ya ce Jehobah ne “kaɗai mai hikima.” (Romawa 16:27) Jehobah ne kaɗai yake da hikima a cikakkiyar ma’anarta. Shi ne Tushen dukan hikima ta gaskiya. (Karin Magana 2:6) Abin da ya sa ke nan Yesu ko da yake shi ne mafi hikima a dukan halittun Jehobah, bai dogara ga tasa hikimar ba amma ya yi magana kamar yadda Ubansa ya yi masa ja-gora.—Yohanna 12:48-50.

18 Ka lura da yadda manzo Bulus ya furta fardanci na hikimar Jehobah: “Ina misalin zurfin yawan hikimar Allah! Zurfin saninsa kuma marar iyaka ne! Hukunce-hukuncensa sun fi gaban bincike, hanyoyin al’amuransa sun wuce gaban ganewa!” (Romawa 11:33) Ta wajen fara ayar da “Ina misali,” Bulus ya nuna motsin rai sosai—a wannan batun, ɗaukaka ce ƙwarai. Kalmar Helenanci da ya zaɓa wa “zurfin” tana da nasaba ta kusa da kalmar “rami marar matuƙa.” Saboda haka, kalmominsa sun kawo hoton zuci. Sa’ad da muka yi tunani bisa hikimar Jehobah, kamar dai a ce muna leƙa wani rami ne marar iyaka marar ƙarshe, rami mai zurfi da faɗi da ba za mu iya ma fahimtar girmansa ba, balle ma a ce mu yi bayani ko kuma mu zana shi dalla-dalla. (Zabura 92:5) Wannan ba abin da zai sa mutum sauƙin kai ba?

19, 20. (a) Me ya sa gaggafa alama ce da ta dace ta hikimar Allah? (b) Ta yaya Jehobah ya nuna iyawarsa ya ga abin da zai faru a nan gaba?

19 Jehobah ne “kaɗai mai hikima” a wata hanya kuma: Shi kaɗai ne kawai zai iya ganin abin da ke zuwa a nan gaba. Ka tuna cewa, Jehobah ya yi amfani da gaggafa mai ganin nesa ya alamta hikimarsa. Babbar gaggafa wataƙila nauyin ta awu goma ne, amma idanunta sun fi na cikakken mutum girma. Idanun gaggafa suna gani na ban mamaki, suna sa tsuntsuwar ta hangi abinci daga nisan dubban ƙafafu daga sama, wataƙila ma nisan miloli! Jehobah ya taɓa cewa game da gaggafa: “Daga can yakan leƙi abincinsa, idanunsa suka hange shi tun daga nesa.” (Ayuba 39:29) Hakazalika, Jehobah yana iya hangar “nesa” game da lokaci—nan gaba!

20 Littafi Mai Tsarki yana cike da tabbaci cewa wannan gaskiya ce. Yana ɗauke da ɗarurruwan annabce-annabce, ko kuma tarihi da aka rubuta kafin abin ya auku. Sakamakon yaƙe-yaƙe, tashi da faɗuwar masu mallakar duniya, da kuma wasu dabarar yaƙi na wasu kwamandojin soja duka an faɗe su a cikin Littafi Mai Tsarki—a wasu batun, ɗarurruwan shekaru kafin su faru.—Ishaya 44:25–45:4; Daniyel 8:2-8, 20-22.

21, 22. (a) Me ya sa babu tushen cewa Jehobah ya riga ya ga dukan abin da za ka zaɓa a rayuwa? Ka ba da misali. (b) Ta yaya muka sani cewa hikimar Jehobah ba cewa, ba ta da juyayi da kuma motsin rai ba ne?

21 Wannan yana nufi ne cewa, Allah ya riga ya ga abin da za ka zaɓa a rayuwarka? Wasu da suke koyar da koyarwar ƙaddara sun nace cewa wai amsar E ce. Amma, wannan ra’ayin yana ƙasƙantar da hikimar Jehobah, domin yana nufin cewa ba zai iya ya sarrafa iyawarsa na ganin abin da yake zuwa a nan gaba ba. Alal misali: Idan kana da muryar waƙa kyakkyawa, ba ka da zaɓe ke nan, sai dai ka riƙa waƙa a koyaushe? Ra’ayin ba shi da kan gado! Hakanan, Jehobah yana iya ganin abin da zai faru a nan gaba, amma ba ya amfani da ita a kowane lokaci. Yin haka zai take mana namu son rai, kyauta mai kyau da Jehobah ba zai taɓa kwacewa ba.—Maimaitawar Shari’a 30:19, 20.

22 Mafi muni ma, tunanin ƙaddara yana nuna cewa hikimar Jehobah ba ta da juyayi, ba ta da ƙauna, ko kuma tausayi. Amma babu abin da ya wuce gaskiya! Littafi Mai Tsarki ya koyar da cewa Jehobah mai “zuciyar hikima ne.” (Ayuba 9:4) Ba wai yana da zuciya ta zahiri ba, amma Littafi Mai Tsarki sau da yawa yana amfani da wannan kalmar wajen maganar abin da ke cikin mutum, wanda ya haɗa da motsin rai da kuma yadda mutum yake ji, kamar ƙauna. Saboda haka, hikimar Jehobah, kamar wasu halayensa, ƙauna ce take mata ja-gora.—1 Yohanna 4:8.

23. Fifitar hikimar Jehobah ya kamata ta motsa mu mu yi mene ne?

23 Yadda take, hikimar Jehobah abin dogara ce cikakkiya. Domin ta ɗara hikimarmu ƙwarai shi ya sa Kalmar Allah ya aririce mu cikin ƙauna: “Dogara ga Yahweh da dukan zuciyarka, kada ka dogara ga ganewarka. A dukan hanyoyin rayuwarka ka girmama shi, shi kuwa zai daidaita hanyoyinka.” (Karin Magana 3:5, 6) Bari yanzu mu shiga binciken hikimar Jehobah saboda mu matso kusa da Allahnmu kaɗai mai hikima.

Tambayoyi don Bimbini

  • Ayuba 28:11-28 Yaya muhimmancin hikimar Allah take, kuma wane sakamako ne mai kyau zai zo daga bimbini bisa wannan batun?

  • Zabura 104:1-25 Ta yaya hikimar Jehobah ta bayyana a halitta, kuma me wannan take sa ka ji?

  • Karin Magana 3:19-26 Idan muka yi waswasi bisa hikimar Jehobah kuma muka yi amfani da ita, yaya za ta shafi rayuwarmu ta yau da kullum?

  • Daniyel 2:19-28 Me ya sa aka kira Jehobah Mai Tone Asiri, kuma yaya za mu amsa ga hikimar annabci da take cikin Kalmarsa?

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba