Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • lv babi na 13 pp. 144-159
  • Bukukuwan da Allah ba ya So

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Bukukuwan da Allah ba ya So
  • “Ku Tsare Kanku Cikin Ƙaunar Allah”
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • KIRSIMATI YA SAMI ASALI NE DAGA BAUTAR RANA
  • ABIN DA LITTAFI MAI TSARKI YA CE GAME DA RANAKUN HAIHUWA
  • ISTA BAUTAR RANAR HAIHUWA NE A ƁOYE
  • TUSHEN BIKIN HALLOWEEN
  • BARI AURENKA YA KASANCE MAI TSABTA
  • ƊAGA KOFI KUMA A KARA SHI DA NA WANI, YA DACE NE?
  • “YA KU MASU-ƘAUNAR UBANGIJI, SAI KU ƘI MUGUNTA”
  • KA ƊAUKAKA ALLAH A KALAMINKA DA HALINKA
  • Dukan Bukukuwa Ne Allah Yake So?
    Ku Ci Gaba da Kaunar Allah
  • Ka Yanke Shawarar Bauta wa Allah
    Me Za Mu Koya Daga Littafi Mai Tsarki?
  • Ka Dage Domin Bauta ta Gaskiya
    Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?
  • Dukan Bukukuwa Ne Allah Yake Amincewa da Su?
    Ka Ji Dadin Rayuwa Har Abada!​—Don Nazarin Littafi Mai Tsarki
Dubi Ƙari
“Ku Tsare Kanku Cikin Ƙaunar Allah”
lv babi na 13 pp. 144-159
Wani yaro yana bude kyautar da iyayensa suka ba shi

BABI NA 13

Bukukuwan da Allah ba ya So

“Kuna gwada abin da ke na yarda ga Ubangiji.”—AFISAWA 5:10.

1. Waɗanne irin mutane ne Jehobah yake jawowa kusa da shi, kuma me ya sa suke bukatar su kasance a faɗake a ruhaniya?

YESU ya ce: “Masu-yin sujjada da gaskiya, za su yi ma Uba sujjada a cikin Ruhu da cikin gaskiya kuma; gama irin waɗannan Uban ya ke nema, su zama masu-yi masa sujjada.” (Yohanna 4:23) Sa’ad da Jehobah ya sami irin waɗannan mutanen, kamar yadda ya same ka, yana jawo su kusa da shi da kuma Ɗansa. (Yohanna 6:44) Wannan gata ne mai girma! Waɗanda suke ƙaunar gaskiyar da ke cikin Littafi Mai Tsarki, dole ne su ci gaba da “gwada abin da ke na yarda ga Ubangiji,” domin Shaiɗan uban ruɗi ne.—Afisawa 5:10; Ru’ya ta Yohanna 12:9.

2. Ka bayyana yadda Jehobah yake ɗaukan waɗanda suke neman su haɗa bauta ta gaskiya da ta ƙarya.

2 Ka yi la’akari da abin da ya faru a kusa da Dutsen Sinai sa’ad da Isra’ilawa suka gaya wa Haruna ya ƙera musu allah. Haruna ya amince ba da son ransa ba kuma ya yi musu ɗan maraƙi na zinari kuma ya ce maraƙin yana wakiltar Jehobah. “Gobe za a yi idi ga Ubangiji,” in ji shi. Jehobah ya tsaya yana kallonsu ne kawai sa’ad da suka haɗa addini na gaskiya da na ƙarya? A’a. Ya sa an kashe mutane kusan dubu uku da suka bauta wa gunkin. (Fitowa 32:1-6, 10, 28) Menene darassin? Idan muna son mu tsare kanmu a cikin ƙaunar Allah, ba za mu “taɓa wani abu mai-ƙazamta” ba kuma Jehobah kaɗai ne za mu bauta wa.—Ishaya 52:11; Ezekiel 44:23; Galatiyawa 5:9.

3, 4. Me ya sa muke bukatar mu mai da hankali sosai ga mizanan Littafi Mai Tsarki sa’ad da muke bincika sanannun al’adu da bukukuwa?

3 Abin baƙin ciki, bayan mutuwar manzannin da suka hana ridda, waɗanda suke da’awar cewa su Kiristoci ne amma ba sa ƙaunar gaskiya sun soma bin al’adun arna, bukukuwansu, da kuma ranakunsu “mai tsarki,” kuma suka ce ya dace da Kiristanci. (2 Tassalunikawa 2:7, 10) Sa’ad da kake la’akari da waɗannan bukukuwan, ka lura da yadda suke nuna ruhun duniya, ba ta Allah ba. Gabaki ɗaya, bukukuwa na duniya suna da manufa ɗaya: Suna jawo sha’awoyi na jiki, kuma suna ɗaukaka imani na addinin ƙarya da sihiri, abubuwan da su ne ainihin alamar “Babila babba.”a (Ru’ya ta Yohanna 18:2-4, 23) Ka tuna cewa, Jehobah da kansa yana kallon mugayen abubuwan da addinan arna suke yi waɗanda su ne tushen al’adu masu yawa a yau. Babu shakka, waɗannan bukukuwan suna ɓata masa rai a yau. Bai kamata ba ne ra’ayinsa ya kasance abu mafi muhimmanci a gare mu ba?—2 Yohanna 6, 7.

4 Mu Kiristoci na gaskiya, mun san cewa akwai bukukuwan da Jehobah ba ya so. Amma muna bukatar mu ƙudurta a zuciyarmu cewa ba za mu taɓa yin su ba. Sake tattauna dalilin da ya sa Jehobah ba ya son waɗannan bukukuwan zai ƙarfafa ƙudurinmu na guje wa duk wani abin da zai hana mu tsare kanmu cikin ƙaunar Allah.

KIRSIMATI YA SAMI ASALI NE DAGA BAUTAR RANA

5. Me ya sa muka tabbata cewa ba a ranar 25 ga Disamba ba ce aka haifi Yesu?

5 Littafi Mai Tsarki bai ce a yi bikin tuna ranar haihuwar Yesu ba. Gaskiyar ita ce, ba a san ainihin ranar haihuwarsa ba. Mun tabbata cewa ba a haife shi ba a ranar 25 ga Disamba a lokacin sanyi a wannan ɓangaren duniyar.b Dalili ɗaya shi ne, Luka ya rubuta cewa sa’ad da aka haifi Yesu, “makiyaya suna kwana a filin Allah” suna kula da tumakinsu. (Luka 2:8-11) Da a ce kullum ne suke “kwana a filin Allah,” da hakan ba zai kasance da muhimmanci ba. Amma, domin ana ruwa da ƙanƙara a Bai’talami a lokacin sanyi, ana kiwon tumaki ne a cikin gida kuma makiyaya ba za su iya “kwana a filin Allah” ba. Bugu da ƙari, Yusufu da Maryamu sun je Bai’talami ne domin Kaisar Augustus ya ba da umurni a yi ƙirge. (Luka 2:1-7) Da wuya a ce Kaisar ya umurci mutanen da suka ƙi jinin sarautar Romawa su koma biranen da aka haife su ana bala’in sanyi ba.

6, 7. (a) A ina ne za a iya samun tushen al’adu masu yawa na Kirsimati? (b) Wane bambanci ne ke tsakanin kyautar da ake bayarwa a ranar Kirsimati da wadda Kiristoci suke bayarwa?

6 Tushen Kirsimati ba ya cikin Nassosi, ya fito ne daga bukukuwan arna na dā, kamar su bikin Saturnalia na Romawa, bikin da aka keɓe wa Saturn, allahn noma. Bisa ga lissafin da suka yi, masu bauta wa allahn nan mai suna Mithra suna “bikin fitowar rana,” a ranar 25 ga Disamba, in ji littafin nan New Catholic Encyclopedia. “Kirsimati ya samo asali ne a lokacin da bautar rana ta yi ƙarfi sosai a Roma,” kusan ƙarnuka uku bayan mutuwar Kristi.

Kiristoci na gaskiya suna ba da kyauta saboda ƙauna

7 A lokacin bukukuwansu, arna suna yi wa junansu kyauta kuma suna cin abinci sosai, abubuwan da har yanzu ana yi a lokacin Kirsimati. Kamar yadda yake a yau, yawancin kyautar da ake bayarwa a lokacin Kirsimati bai jitu da abin da ke 2 Korintiyawa 9:7, wadda ta ce: “Kowane mutum shi aika bisa yadda ya annita a zuciyarsa; ba da cicijewa ba, ba kuwa kamar ta dole ba: gama Allah yana son mai-bayarwa da daɗin rai.” Kiristoci na gaskiya suna ba da kyauta saboda ƙauna, ba su keɓe wata takamaiman rana na ba da kyauta ba, kuma ba sa sa ran cewa wani zai saka musu kyautar da suka bayar. (Luka 14:12-14; karanta Ayukan Manzanni 20:35) Bugu da ƙari, suna godiya sosai domin ’yantar da su da aka yi daga gajiyar da ke tattare da Kirsimati da kuma nauyin bashin da mutane da yawa suke ci a wannan lokacin.—Matta 11:28-30; Yohanna 8:32.

8. Masana taurari sun ba Yesu kyauta a ranar haihuwarsa ne? Ka ba da bayani.

8 Amma, wasu za su iya cewa, ai masanan taurari sun ba Yesu kyauta a ranar haihuwarsa. Kyautar da suka bayar hanya ce kawai ta daraja babban mutum, kuma hakan sananniyar al’ada ce da ake yi a zamanin da aka rubuta Littafi Mai Tsarki. (1 Sarakuna 10:1, 2, 10, 13; Matta 2:2, 11) Kuma ba a daren da aka haifi Yesu ba ne suka zo ba. A lokacin da suka zo, Yesu ba jariri ba ne da ke kwance a cikin sakarkari, an riga an yi watanni da haihuwarsa kuma yana zaune ne a cikin gida.

YA KAMATA NA YI BIKIN NE?

Wata ’yar’uwa ta ki ta karba furen tuna da ranar bukukuwa a wurin aikinta

Mizani: “Ku fito daga cikinsu, ku ware, in ji Ubangiji, Kada ku taɓa kowane abu marar-tsarki; Ni ma in karɓe ku.” —2 Korinthiyawa 6:17.

Wasu tambayoyi da za ka yi wa kanka game da sanannen biki ko al’ada

  • Ya samo tushe ne daga ayyuka ko koyarwar addinin ƙarya, har da sihiri?—Ishaya 52:11; 1 Korinthiyawa 4:6; 2 Korintiyawa 6:14-18; Ru’ya ta Yohanna 18:4.

  • Yana kawo ɗaukakar da bai kamata ba ne ga mutane, ƙungiya, ko ƙasa?—Irmiya 17:5-7; Ayukan Manzanni 10:25, 26; 1 Yohanna 5:21.

  • Yana ɗaukaka wata ƙasa ko yare fiye da wata?—Ayukan Manzanni 10:34, 35; 17:26.

  • Yana nuna “ruhun duniya,” wanda yake hamayya da ruhu mai tsarki na Allah?—1 Korintiyawa 2:12; Afisawa 2:2.

  • Yin sa zai iya sa wasu tuntuɓe ne?—Romawa 14:21.

  • Idan na zaɓi cewa ba zan saka hannu ba, ta yaya zan iya bayyana dalilan yin hakan ga wasu cikin daraja?—Romawa 12:1, 2; Kolossiyawa 4:6.

Nassosi na gaba za su iya ƙara ba da haske a kan tambayoyi na sanannun bukukuwa:

  • “[Isra’ilawa marasa aminci] suka cuɗaya da al’umman, Suka koya ayukansu.”—Zabura 106:35.

  • “Wanda ya ke da aminci cikin ƙanƙanin abu mai-aminci ne cikin mai yawa: kuma wanda ba shi da gaskiya cikin ƙanƙanin abu ba, mara-gaskiya ne cikin mai-yawa.”—Luka 16:10.

  • “Ku ba na duniya ba ne.”—Yohanna 15:19.

  • “Ba ku da iko ku tara ci daga [teburi] na Ubangiji, da na aljanu.”—1 Korintiyawa 10:21.

  • “Kwanakin da sun wuce ya isa bin guri na Al’ummai, da tafiya cikin lalata, da sha’awoyi, da maye, da haukan wasa, da shan giya, da ƙazantaciyar bautar gumaka.”—1 Bitrus 4:3.

ABIN DA LITTAFI MAI TSARKI YA CE GAME DA RANAKUN HAIHUWA

9. Menene ya yi fice game da bikin tuna ranar haihuwa da aka ambata a cikin Littafi Mai Tsarki?

9 Ko da yake haihuwa na jawo farin ciki sosai, Littafi Mai Tsarki bai taɓa ambata wani bawan Allah da ya taɓa yin bikin tuna ranar haihuwa ba. (Zabura 127:3) Wannan mantuwa ce? A’a, domin an ambata bukukuwan tuna ranar haihuwa guda biyu, na Fir’auna na ƙasar Masar da na Hirudus Antibas. (Karanta Farawa 40:20-22; Markus 6:21-29) Mugayen abubuwa sun auku a waɗannan bukukuwan biyu, musamman na Hirudus inda aka yanke kan Yohanna Mai Baftisma.

10, 11. Yaya ne Kiristoci na farko suka ɗauki bikin tuna ranar haihuwa, kuma me ya sa?

10 “Kiristoci na farko,” in ji littafin nan The World Book Encyclopedia, “sun ɗauki bikin ranar haihuwar mutum a matsayin al’adar arna.” Alal misali, Helenawa na dā sun gaskata cewa kowanne mutum yana da ruhun da ke kāre shi wanda ya halarci ranar haihuwarsa kuma bayan haka zai ci gaba da kula da shi. Wannan ruhun “yana da dangantaka da allahn da a ranar haihuwarsa aka haifi mutumin,” in ji littafin nan The Lore of Birthdays. Bikin ranar haihuwa yana da dangantaka na kud da kud tun da daɗewa da ilimin taurari da kuma tauraron ranar haihuwa.

“RANAKU ‘MASU TSARKI’ DA SHAIƊANCI”

Ya kamata a lura cewa rana mafi muhimmanci a addini mai suna Shaiɗanci ita ce ranar haihuwar mutum. Me ya sa? Domin mabiyan addinin Shaiɗan sun gaskata cewa kowane mutum allah ne idan ya zaɓi mai da kansa hakan. Da haka, yin bikin tuna ranar haihuwar yana nufin yin bikin haihuwar allah. Ko da yake yawancin mutane ba su da irin wannan ra’ayin da ya wuce kima. Duk da haka, littafin nan The Lore of Birthdays ya ce: “Sauran ranaku masu tsarki suna faranta zuciya, amma ranar haihuwa tana sa fahariya.”

Wasu ranaku mafi “tsarki” a kalandar mabiyan addinin Shaiɗan su ne Daren Walpurgis da Halloween. Merriam-Webster’s Collegiate Dictionary ya ce Daren Walpurgis shi ne “rana kafin ranan Mayu, ranar da aka gaskata cewa mayu suna taruwa a wani zaɓaɓɓen wurin taro.”

11 Ban da guje wa al’adun bikin ranar haihuwa domin ya samo tushe ne daga arna da sihiri, bayin Allah na dā sun ƙi su ne domin mizanansu. Me ya sa? Domin su maza da mata ne masu tawali’u, waɗanda ba su ɗauki haihuwarsu da wani muhimmanci ba sosai har da za su tuna ranar.c (Mikah 6:8; Luka 9:48) Maimakon haka, suna yaba wa Jehobah kuma suna yi masa godiya domin kyautar rai mai tamani.d—Zabura 8:3, 4; 36:9; Ru’ya ta Yohanna 4:11.

12. Ta yaya ne ranar mutuwarmu ta fi ranar haihuwarmu?

12 Idan suka mutu, Allah zai tuna dukan mutane masu aminci, kuma zai ta da su daga matattu. (Ayuba 14:14, 15) Mai-Wa’azi 7:1 ya ce: “Nagarin suna ya fi mai mai-tamani; kuma ranar mutuwa ta fi ranar haifuwa.” ‘Sunanmu’ shi ne sakamako mai kyau da muka samu daga Allah domin hidimar da muka yi da aminci. Saboda haka, tunawa kawai da aka umurci Kiristoci su dinga yi shi ne tuna mutuwar Yesu ba haihuwarsa ba, wanda ‘sunansa’ ne kawai zai iya sa mu sami ceto.—Luka 22:17-20; Ibraniyawa 1:3, 4.

ISTA BAUTAR RANAR HAIHUWA NE A ƁOYE

13, 14. Menene tushen al’adun Ista?

13 Ko da yake ana cewa bikin tashin Kristi daga matattu ne, Ista ya samo asalinsa ne daga addinin ƙarya. An haɗa sunan nan Ista da Eostre, ko Ostara, wato allahniya ta haske da damina ta ƙasar Anglo-Saxon. Kuma ta yaya aka haɗa zomaye da ƙwai da Ista? Ƙwai “alamu ne na sabon rai da tashi daga matattu,” in ji littafin nan Encyclopædia Britannica, tun da daɗewa zomo alama ce ta haihuwa. Saboda haka, Ista biki ne na haihuwa da ake yi da sunan bikin tashin Kristi daga matattu.e

14 Jehobah zai amince ne a yi amfani da bikin haihuwa da ke cike da ƙazanta don a tuna da tashin Ɗansa daga matattu? Hakan ba zai taɓa yiwu ba! (2 Korintiyawa 6:17, 18) Balle ma, Nassosi ba su taɓa ba da umurni ko ikon tuna tashin Yesu daga matattu ba. Yin hakan da sunan Ista, rashin aminci ne mai tsanani.

TUSHEN BIKIN HALLOWEEN

15. Menene tushen bikin Halloween, kuma menene ya yi fice game da ranar da aka zaɓa don yin wannan bikin?

15 Bikin Halloween wanda ake yi a ranar 31 ga Oktoba, ya yi fice wajen yin shigar mayu, da wasu irin shiga masu ban tsoro, wanda kuma ake kira Daren Hallows ko kuwa Ranar Dukan Waliyai, ya samo asali ne daga Seltikawan dā na Britaniya da kuma ƙasar Ireland. Sa’ad da wata ta cika sha huɗu a gab da 1 ga Nuwamba, suna yin biki mai suna Samhain, wanda ke nufin “Ƙarshen Rani.” Sun gaskata cewa a lokacin Samhain, ana cire abin da ya raba mutane da duniyar halittun da suka fi ’yan adam ƙarfi, kuma ruhohi masu kyau da mugaye suna yawo a duniya. Sun gaskata cewa kurwar matattu suna komawa gidajensu, kuma iyalai suna ajiye abinci da abin sha wa fatalwar da za ta ziyarce su don su lallashe ta. Saboda haka, sa’ad da yara a yau suka yi shiga irin ta fatalwa ko mayu, suna bi gida-gida suna yi wa mutane barazanar cewa za su cutar da su idan ba a ba su kyauta ba, cikin rashin sani suna yin bukukuwan Samhain ne.

BARI AURENKA YA KASANCE MAI TSABTA

16, 17. (a) Me ya sa Kiristocin da suke shirin aure suke bukatar su bincika al’adun aure na inda suke da zama ta wajen yin la’akari da mizanan Littafi Mai Tsarki? (b) Game da al’adun nan kamar su jefa shinkafa da wasu abubuwa, menene ya kamata Kiristoci su yi la’akari da shi?

16 Nan ba da daɗewa ba, “da muryar ango da muryar amarya kuma ba za a ƙara jinsu ba daɗai a cikin [Babila Babba].” (Ru’ya ta Yohanna 18:23) Me ya sa? Dalili guda shi ne ayyukanta na sihiri zai iya ƙazanta da aure tun daga ranar da aka yi shi.—Markus 10:6-9.

17 Al’adu sun bambanta a kowace ƙasa. Wasu al’adun da ake ganin cewa ba su da lahani, wataƙila sun samo asali ne daga Babila wanda ake ganin cewa za su iya kawo “sa’a” ga ma’auratan ko baƙinsu. (Ishaya 65:11, Littafi Mai Tsarki) Ɗaya daga wannan al’adar ya ƙunshi jefa shinkafa ko wasu abubuwa. Wataƙila wannan ya samo asali ne daga imanin da aka yi cewa abinci yana lallashin mugayen ruhohi kuma yana hana su cutar da amarya da angon. Bugu da ƙari, tun da daɗewa shinkafa tana da dangantaka da haihuwa, farin ciki, da tsawon rai. Babu shakka, dukan waɗanda suke son su ci gaba da tsare kansu a cikin ƙaunar Allah za su yi watsi da irin waɗannan ƙazaman al’adun.—Karanta 2 Korintiyawa 6:14-18.

18. Waɗanne mizanai na Littafi Mai Tsarki ne ya kamata ya yi wa waɗanda suke shirin aure da waɗanda aka gayyata ja-gora?

18 Hakazalika, bayin Jehobah suna guje wa halayen duniya da za su iya lalata darajar aure da liyafar aure na Kirista ko kuwa waɗanda za su iya shafan lamirin wasu. Alal misali, suna ƙin maganganu masu ban haushi ko batsa kuma suna guje wa wasannin banza ko kalaman da za su kunyatar da ma’auratan da wasu. (Misalai 26:18, 19; Luka 6:31; 10:27) Suna kuma guje wa liyafar aure mai girma, wadda ba ta nuna filako, sai “darajar rai ta wofi.” (1 Yohanna 2:16) Idan kana shirin aure, kada ka manta cewa Jehobah yana son ranarka ta musamman ta zama abin da za ka riƙa tunawa da farin ciki, ba yin da na sani ba.f

ƊAGA KOFI KUMA A KARA SHI DA NA WANI, YA DACE NE?

19, 20. Menene wani littafi ya ce game da tushen kara kofi da kofi, kuma me ya sa wannan al’adar ba ta dace da Kiristoci ba?

19 Wani abin da ake yawan yi a wajen bikin aure da liyafa shi ne kara kofi da kofin wani. Littafin nan International Handbook on Alcohol and Culture na shekara ta 1995 ya ce: “Kara kofi da kofi . . . wataƙila al’ada ce ta hadaya a zamanin dā inda ake gabatar da ruwa mai tsarki ga alloli . . . don yin fata, a taƙaitacciyar addu’ar da ake cewa ‘tsawon rai!’ ko ‘ƙarin lafiya a gare ka!’”

20 Hakika, wataƙila yawancin mutane ba sa ɗaukan kara kofi da kofi a matsayin wani abu da ya shafi addini ko camfi ba. Duk da haka, ana iya ɗaukan al’adar ɗaga kofi sama a matsayin roƙon “sama,” wato, aljanu, don samun albarka a hanyar da ba ta jitu da abin da aka faɗa ba a cikin Nassosi.—Yohanna 14:6; 16:23.g

“YA KU MASU-ƘAUNAR UBANGIJI, SAI KU ƘI MUGUNTA”

21. Duk da cewa ba su da tushe na addini, waɗanne sanannun bukukuwa ne Kiristoci za su guje wa, kuma me ya sa?

21 Ta wajen nuna mizanan wannan duniyar da take taɓarɓarewa, wato, halayen da Babila Babba take ɗaukakawa kai tsaye ko a ɓoye, wasu ƙasashe suna yin bukukuwa na shekara shekara, bukukuwan da ake yin rawan da ke cike da batsa, kuma ana iya yin bikin salon rayuwar ’yan luwaɗi da ’yan maɗigo. Zai dace mai ‘ƙaunar Jehobah’ ya halarci ko kuma ya kalli irin wannan wasan? Yin hakan zai nuna cewa yana ƙin mugun abu da gaske? (Zabura 1:1, 2; 97:10) Zai dace a yi koyi da halin mai zabura wanda ya yi addu’a cewa: “Ka kawasda idanuna ga barin duban abin banza.”—Zabura 119:37.

22. A wane lokaci ne Kirista zai iya yanke shawara bisa ga lamirinsa game da ko zai saka hannu a wani biki ko ba zai saka ba?

22 A ranakun da mutanen duniya suke yin bukukuwansu, ya kamata Kirista ya mai da hankali sosai don kada halinsa ya sa wasu su yi zaton cewa shi ma yana yin bikin. Bulus ya rubuta: “Ko kuna ci fa, ko kuna sha, ko kuwa iyakar abin da ku ke yi, a yi duka domin a girmama Allah.” (1 Korintiyawa 10:31; ka duba akwatin nan “Yanke Shawarwarin da Suka Dace,” a shafi na 158-159.) A wani ɓangaren kuma, idan al’ada ko biki bai da wani dangantaka da addinan ƙarya, bai shafi siyasa ko son ƙasa ba, kuma bai saɓa wa mizanan Littafi Mai Tsarki ba, to, kowanne Kirista ne zai yanke shawara da kansa ko zai saka hannu a ciki. Hakazalika, ya kamata ya yi la’akari da yadda wasu za su ji don kada ya sa su tuntuɓe.

KA ƊAUKAKA ALLAH A KALAMINKA DA HALINKA

23, 24. Ta yaya za mu iya ba da shaida mai kyau game da mizanai masu adalci na Jehobah?

23 Yawancin mutane suna ɗaukan ranakun wasu sanannun bukukuwa a matsayin lokacin kasancewa tare da iyali da abokai. Saboda haka, idan wani ya yi zaton cewa matsayin da muka ɗauka da ke bisa Nassi ba ya nuna ƙauna ko kuma ya wuce kima, muna iya bayyana masa cewa Shaidun Jehobah suna ɗaukan yin nishaɗi mai kyau tare da iyalinsu da kuma abokansu da tamani. (Misalai 11:25; Mai-Wa’azi 3:12, 13; 2 Korintiyawa 9:7) Muna more tarayya da ƙaunatattunmu a kowane lokaci, amma domin ƙaunar da muke yi wa Allah da kuma mizanansa na adalci, ba ma son mu ɓata waɗannan lokacin na farin ciki da al’adun da ba ya so.—Duba akwatin nan “Bauta ta Gaskiya Tana Kawo Farin Ciki Mafi Girma,” a shafi na 156.

BAUTA TA GASKIYA TANA KAWO FARIN CIKI MAFI GIRMA

Jehobah shi ne “Allah mai farin ciki,” kuma yana son bayinsa su kasance masu farin ciki. (1 Timothawus 1:11, NW.) Wannan gaskiyar ta bayyana a nassosi na gaba:

  • “Mai-farin zuciya yana da buki tuttur.”—Misalai 15:15.

  • “Na sani babu abin da ya fi masu, kamar su yi murna, su kāma aika nagarta dukan kwanakin ransu. Kowane mutum kuma shi ci, shi sha, shi ji daɗi cikin dukan aikinsa; wannan kyautar Allah ne.”—Mai-Wa’azi 3:12, 13.

  • “Amma mutumin kirki yana furtadda al’amura na kirki: a cikin al’amura na kirki kuma za ya dawama.”—Ishaya 32:8.

  • “Ku zo gareni, dukanku da ku ke wahala, masu-nauyin kaya kuma, ni [Yesu] kuwa in ba ku hutawa. . . . Gama karkiyata mai-sauƙi ce, kayana kuma mara-nauyi.”—Matta 11:28, 30.

  • “Ku a san gaskiya kuma, gaskiya kuwa za ta yantadda ku.”—Yohanna 8:32.

  • “Kowane mutum shi [bayar] bisa yadda ya annita a zuciyarsa; ba da cicijewa ba, ba kuwa kamar ta dole ba: gama Allah yana son mai-bayarwa da daɗin rai.”—2 Korintiyawa 9:7.

  • “Ɗiyan Ruhu ƙauna ne, farinciki, salama, . . . nagarta, aminci.”—Galatiyawa 5:22.

  • “Amfanin haske yana cikin dukan nagarta da adalci da gaskiya.”—Afisawa 5:9.

24 Wasu Shaidu sun yi nasara sosai wajen tattaunawa da mutanen da suke son su san gaskiyar batutuwan da ke babi na 16 na littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?h Amma ka tuna cewa muradinmu shi ne mu jawo mutane zuwa gaskiya, ba yin gardama da su ba. Saboda haka, ka daraja mutane, ka kasance mai haƙuri, kuma ka ‘bari zancenka kullum ya kasance tare da alheri, gyartace da gishiri.’—Kolossiyawa 4:6.

25, 26. Ta yaya iyaye za su iya taimaka wa yaransu su ƙarfafa bangaskiyarsu da ƙaunarsu ga Jehobah?

25 A matsayinmu na bayin Jehobah, muna da fahimi sosai. Mun san dalilin da ya sa muke yin wasu abubuwa da kuma dalilin da ya sa muke guje wa wasu. (Ibraniyawa 5:14) Saboda haka, iyaye ku koya wa yaranku su dinga yin bimbini a kan mizanan Littafi Mai Tsarki. Idan kuka yi hakan, za ku ƙarfafa bangaskiyarsu, za ku taimaka musu su ba da amsoshi da ke bisa Nassi ga mutanen da suka tuhumi imaninsu, kuma za ku tabbatar da su cewa Jehobah yana ƙaunarsu.—Ishaya 48:17, 18; 1 Bitrus 3:15.

26 Dukan waɗanda suke bauta wa Allah “cikin Ruhu da cikin gaskiya” suna guje wa bukukuwan da suka saɓa wa nassi kuma suna iya ƙoƙarinsu su kasance masu gaskiya a dukan fasalolin rayuwarsu ta yau da kullum. A yau, yawancin mutane suna ganin cewa kasancewa mai gaskiya bai dace ba. Amma kamar yadda za mu gani a babi na gaba, hanyoyin Allah su ne mafi kyau.

a Ka duba akwatin nan “Ya Kamata Na Yi Bikin Ne?” da ke shafuffuka na 148-149. An lissafa sunayen ranaku “masu tsarki” da kuma bukukuwa a cikin Watch Tower Publications Index, Shaidun Jehobah ne suka wallafa.

b Bisa ga lissafin da ke cikin Littafi Mai Tsarki da kuma littattafan tarihi, kamar dai an haifi Yesu ne a shekara ta 2 K.Z., a watan Ethanim na Yahudawa, wanda ya yi daidai da Satumba ko Oktoba a kalandarmu ta zamani. —Ka duba Insight on the Scriptures, Na 2, shafuffuka na 56-57, Shaidun Jehobah ne suka wallafa.

c Duba akwatin nan “Ranaku ‘Masu Tsarki’ da Shaiɗanci,” a shafi na 150.

d Doka ta alkawari ta ce idan mace ta haihu, ta miƙa hadaya ta zunubi ga Allah. (Leviticus 12:1-8) Wannan tunasarwa ce cewa yara suna gadon zunubi daga iyayensu, kuma wannan dokar ta taimaka wa Isra’ilawa su kasance da daidaitaccen ra’ayi game da haihuwa, kuma wataƙila hakan ya hana su saka hannu a al’adun arna na bikin ranar haihuwa.—Zabura 51:5.

e An kuma haɗa Ista da bautar allahniyar haihuwa mai suna Astarte, wadda alamunta su ne ƙwai da zomo. Siffofin Astarte a yawancin lokaci ya nuna cewa tana da manyan al’aura ko kuwa zomo a gefenta da kuma ƙwai a hannunta.

f Ka duba talifofi guda uku a kan aure da taron liyafa da ke Hasumiyar Tsaro ta 1 ga Nuwamba, 2006, shafi na 6-15, da kuma Hasumiyar Tsaro ta 15 ga Oktoba, 2006 shafi na 28 na Turanci.

g Dubi Hasumiyar Tsaro ta 15 ga Fabrairu, 2007, shafi na 30-31 na Turanci.

h Shaidun Jehobah ne suka wallafa.

YANKE SHAWARWARIN DA SUKA DACE

A wasu lokatai, wasu abubuwa suna iya tasowa da za su gwada ƙaunarmu ga Jehobah da kuma fahiminmu na yadda za mu yi amfani da mizanan Littafi Mai Tsarki. Alal misali, mata ko mijin Kirista da ba mai bi ba ne yana iya gayyatar mai bin ya ko ta zo su je su ci abinci tare da danginsu a ranar hutun da mutanen duniya suke yi. Wasu Kiristoci da lamiri mai kyau suna iya zuwa; wasu kuwa suna iya ƙin zuwa. Idan Kirista ta karɓi irin wannan gayyar, ya kamata halinta ya nuna dalla-dalla cewa ba ta kiyaye wannan ranar hutun, kuma ta ziyarci wurin ne kawai don ta more abinci tare danginta.

Yana da kyau Kirista ta yi magana cikin daraja da mijinta tun da wuri, ta wurin bayyana irin kunyar da zai iya ji idan dangin suka soma yin ayyukan da suka shafi hutun kuma ta ƙi saka hannu. Mijin wanda ba mai bi ba ne yana iya yanke shawarar kai ziyarar a wani lokaci.—1 Bitrus 3:15.

Bayan ya saurari bayanin da matarsa ta yi, idan mijin ya nace cewa sai ta bi shi fa? Tana iya yanke shawara cewa a matsayinsa na maigida, shi ke da hakkin yi wa iyalinsa tanadin abinci. (Kolossiyawa 3:18) A wannan yanayin, abincin yana gidan danginsa. Tana ma iya ba da shaida mai kyau sa’ad da suke hutawa. Abincin bai ƙazantu ba don kawai za a ci shi a ranan biki na mutanen duniya. (1 Korintiyawa 8:8) Kiristar tana iya ɗaukan hakan a matsayin cin abinci kawai kuma ba za ta yi gaishe-gaishe, waƙoƙi, kara kofi da kofi da sauransu da ake yi a wannan ranar hutu da ake kira mai tsarki ba.

Wani abu kuma da ya kamata a yi la’akari da shi shi ne yadda cin irin wannan abincin zai iya shafan wasu. Mata Kirista ta tuna cewa wasu da suka ji cewa ta ziyarci danginta da ba masu bi ba ne a wannan ranar suna iya yin tuntuɓe.—1 Korintiyawa 8:9; 10:23, 24.

Bugu da ƙari, iyalin za ta iya matsa wa Kiristar ta bijire kuwa? Son guje wa duk wani abin da zai iya kunyatar da mutum zai iya sa shi ya bijire! Saboda haka, yana da muhimmanci ta yi tunani a kan batun sosai tun da wuri, ta yi la’akari da waɗannan abubuwan duka, har da lamirinta na Kirista.—Ayukan Manzanni 24:16.

Ya Kamata in Karɓi Bonas na Kirsimati Ne?

A lokacin Kirsimati, wanda ya ɗauki Kirista aiki yana iya ba shi kyauta ko bonas. Ya kamata Kirista ya ƙi irin wannan kyautar ne? Ba dole ba ne. Wataƙila shugaban aikin ba zai yi tunanin cewa wanda ya karɓi kyautar yana yin Kirsimati ba. Wataƙila shugaban aikin yana yi wa dukan ma’aikatansa kyauta ne kawai cikin ribar da suka samu. Wataƙila ya yi hakan ne don nuna godiyarsa ga ayyukan da suka yi a wannan shekarar ya kuma ƙarfafa su su ci gaba da yin aiki mai kyau. Shugaban aikin yana iya ba dukan ma’aikatansa kyauta, har da Yahudawa, Musulmai, da sauransu, ko suna Kirsimati ko ba sa yi. Saboda haka, lokacin da ake ba da kyautar ko kuwa sunan da aka ba kyautar ba ya nufin cewa Shaidun Jehobah ba za su iya karɓa ba.

Ko da an ba da kyautar domin hutu na addini, hakan ba ya nufin cewa wanda ya karɓi kyautar yana da irin wannan ra’ayi na addini. Abokin aiki ko dangi yana iya gaya wa Mashaidi, “Na san cewa ba ka kiyaye wannan rana mai tsarki, duk da haka ina son in ba ka wannan kyautar.” Idan lamirin Kiristan ba zai dame shi ba, yana iya karɓan kyautar kuma ya yi godiya ba tare da ya yi kalami game da hutun ba. (Ayukan Manzanni 23:1) Wataƙila a lokacin da yake ganin cewa yin hakan ba zai jawo fushi ba sosai, Kiristan yana iya bayyana imaninsa cikin basira.

Amma, idan wanda ke ba da kyautar yana son ya nuna ne cewa Kiristan bai riƙe bangaskiyarsa ba sosai ko kuwa zai bijire don abin duniya fa? Zai dace a ƙi kyautar. Babu shakka, muna son mu bauta wa Jehobah Allah shi kaɗai.—Matta 4:8-10.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba