Sashe 18
Yesu Ya Yi Mu’ujizai
Ta hanyar mu’ujizansa Yesu ya nuna yadda zai yi amfani da ikonsa a matsayin Sarki
ALLAH ya ƙarfafa Yesu ya yi abubuwan da mutane ba za su iya yi ba. Yesu ya yi manyan mu’ujizai sosai, yawanci a gaban mutane. Waɗannan mu’ujizan sun nuna cewa Yesu yana da iko bisa maƙiya da ƙalubalen da mutane ajizai suka kasa magancewa. Yi la’akari da wasu misalai.
Yunwa. Mu’ujiza ta farko da Yesu ya yi ita ce mai da ruwa zuwa ruwan inabi. Sau biyu, ya ciyar dubban mutane da suke jin yunwa da kifi da burodi ɗan kaɗan. A waɗannan lokatan biyu, kowa ya samu isashen abinci, har ma ya rage.
Rashin lafiya. Yesu ya warkar da mutanen da ke da “kowace irin cuta da kowane irin rashin lafiya.” (Matta 4:23) Yesu ya warkar da makafi, kurame, da masu farfaɗiya. Ya warkar da guragu, da naƙasassu. Babu wani irin rashin lafiya da ya kasa warkarwa.
Yanayi mai haɗari. Sa’ad da Yesu da almajiransa suke cikin kwalekwale a Tekun Galili, sai aka soma mugun iska. Tsoro ya kama almajiran. Yesu ya kalli iskar da ke kaɗa tekun kuma ya ce: “Ka natsu, ka yi shuru.” Sai komi ya yi shiru. (Markus 4:37-39) A wani lokaci kuma, ya yi tafiya a kan ruwa sa’ad da ake wata iska mai ban tsoro.—Matta 14:24-33.
Mugayen ruhohi. Mugayen ruhohi sun fi mutane ƙarfi sosai. Mutane da yawa sun kasa ’yanta kansu daga mugayen maƙiyan Allah. A kai a kai, sa’ad da Yesu ya umurce su su fita, ya ’yanta mutanen daga hannun ruhohin. Bai ji tsoron waɗannan ruhohin ba. Akasin haka, sun san ikonsa kuma suna jin tsoronsa.
Mutuwa. Wadda ake kira “maƙiyi na ƙarshe,” abokin gaba ne da babu mutumin da zai iya yin nasara a kai. (1 Korintiyawa 15:26) Duk da haka, Yesu ya ta da matattu, ya ta da wani saurayi kuma ya miƙa shi ga uwarsa wadda gwauruwa ce kuma ya ta da ƙaramar yarinya kuma ya miƙa ta ga iyayenta da ke baƙin ciki. A wani lokaci mai ban mamaki, Yesu ya ta da abokinsa Li’azaru daga matattu a gaban mutanen da ke kuka, duk da cewa mutumin ya yi kwana huɗu da mutuwa! Mugayen maƙiyan Yesu sun faɗi cewa ya yi wannan mu’ujizar.—Yohanna 11:38-48; 12:9-11.
Me ya sa Yesu ya yi dukan waɗannan mu’ujizan? Daga baya, ai mutuwa ta kashe dukan waɗanda ya taimaka wa. Ƙwarai kuwa, amma mu’ujizan da Yesu ya yi suna da amfani na dindindin. Sun tabbatar da cewa dukan annabce-annabce masu ban al’ajabi da aka yi game da sarautar Sarki Almasihu duk gaskiya ne. Ba a bukatan a yi shakkar cewa Sarkin da Allah ya naɗa zai kawar da yunwa, rashin lafiya, yanayi mai haɗari, mugayen ruhohi, ko mutuwa. Ya riga ya nuna cewa Allah ya ba shi ikon yin dukan waɗannan abubuwan.
—An ɗauko daga littattafan Matta, Markus, Luka, da Yohanna.
◼ Ta yaya ne Yesu ya nuna ƙarfinsa a kan yunwa? rashin lafiya? yanayi mai haɗari? mugayen ruhohi? mutuwa?
◼ Menene mu’ujizan da Yesu ya yi suka nuna game da sarautar da zai yi bisa duniya a nan gaba?
[Taswira a shafi na 21]
Farawa
Fitowa
Levitikus
Littafin Lissafi
Kubawar Shari’a
Joshua
Alƙalawa
Ruth
Yunana
Mikah
Nahum
Habakkuk
Zafaniya
Haggai
Zakariya
Malakai
Matta ●
Markus ●
Luka ●
Yohanna ●
Ayyukan Manzanni
Romawa
1 Korintiyawa
2 Korintiyawa
Galatiyawa
Afisawa
Filibiyawa
Kolosiyawa
1 Tasalonikawa
2 Tasalonikawa
1 Timotawus
2 Timotawus
Titus
Filimon
Ibraniyawa
Yaƙub
1 Bitrus
2 Bitrus
1 Yohanna
2 Yohanna
3 Yohanna
Wasiƙa ta Yahuda
Ru’ya ta Yohanna