Sashe 21
An Ta da Yesu Daga Matattu!
Yesu ya bayyana ga mabiyansa don ya ba su umurni kuma ya ƙarfafa su
ARANA ta uku bayan mutuwar Yesu, wasu mata waɗanda mabiyansa ne sun ga cewa an kawar da dutsen da aka rufe bakin kabarin da shi. Ban da haka, babu komi a cikin kabarin!
Sai mala’iku biyu suka bayyana. “Kuna neman Yesu, Ba-nazarat,” in ji guda a cikinsu. “Ya tashi.” (Markus 16:6) Ba tare da ɓata lokaci ba, matan suka ruga don su gaya wa manzannin. A kan hanyarsu, sun haɗu da Yesu. “Kada ku ji tsoro,” in ji shi. “Ku tafi, ku faɗa wa ’yan’uwana su tafi zuwa cikin Galili, can kuwa za su gan ni.”—Matta 28:10.
A wannan ranar, mabiyansa su biyu suna tafiya daga Urushalima zuwa ƙauyen Imwasu. Wani baƙo ya haɗu da su kuma ya tambaye su abin da suke tattaunawa. Amma, mutumin Yesu ne da aka ta da daga matattu, wanda ya bayyana a fasalin da ba su gane ba da farko. Da fuskar da ke cike da baƙin ciki sun mai da martani cewa suna tattaunawa ne game da Yesu. Baƙon ya soma bayyana batutuwa game da Almasihu a cikin dukan Nassosi. Hakika, Yesu ya cika dukan annabce-annabcen da aka yi game da Almasihu daga farko har ƙarshe.a Sa’ad da almajiran suka fahimci cewa Yesu ne baƙon, wanda aka ta da daga matattu a matsayin ruhu, sai ya ɓace.
Nan da nan almajiran biyu suka koma Urushalima. A nan suka tarar da manzannin sun taru a cikin wani ɗakin da aka rufe ƙofofin. Yayin da su biyun suke faɗin abin da suka gani, sai Yesu ya bayyana. Abin ya ba mabiyansa mamaki sosai! “Don menene kuwa zacezace suna tashi a cikin zuciyarku?” Yesu ya tambaye su. “Hakanan aka rubuta, Kristi za ya sha wahala, za ya tashi daga matattu kuma kan rana ta uku.”—Luka 24:38, 46.
A cikin kwanaki 40 bayan an ta da shi daga matattu, Yesu ya bayyana ga almajiransa a lokatai dabam-dabam. Akwai lokacin da ya bayyana ga mutane fiye da 500! Wataƙila a wannan lokacin ne ya ba su wannan aikin mai girma: “Ku tafi . . . ku almajirtarda dukan al’ummai, . . . kuna koya musu su kiyaye dukan iyakar abin da na umurce ku: ga shi kuwa ina tare da ku kullayaumi har matuƙar zamani.”—Matta 28:19, 20.
A taronsa na ƙarshe da manzanninsa 11 masu aminci, Yesu ya yi alkawari: “Za ku karɓi iko lokacin da Ruhu Mai-tsarki ya zo bisanku; za ku zama shaiduna . . . har kuma iyakan duniya.” (Ayukan Manzanni 1:8) Bayan haka aka yi sama da Yesu, kuma gajimare ya hana su ganinsa yayin da yake yin sama.
—An ɗauko daga Matta sura ta 28; Markus sura ta 16; Luka sura ta 24; Yohanna surori na 20 da 21; 1 Korintiyawa 15:5, 6.
[Hasiya]
a Don samun misalan annabce-annabce game da Almasihu da suka cika a kan Yesu, ka duba shafuffuka na 17-19 na wannan mujallar da kuma shafuffuka na 199-201 na littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?
◼ Ta yaya ne almajiran Yesu suka san cewa Allah ya ta da shi daga matattu?
◼ Menene Yesu ya bayyana wa almajirai biyu da ya haɗu da su a kan hanyar zuwa Imwasu?
◼ Waɗanne umurni ne Yesu ya ba almajiransa kafin ya koma sama?
[Akwati a shafi na 24]
RUHU MAI TSARKI
Ruhu mai tsarki na Allah shi ne iko mafi ƙarfi a sararin samaniya. Jehobah ya yi amfani da ruhunsa, ko ƙarfin iko, ya halicci sama da duniya kuma ya ja-goranci rubuta Littafi Mai Tsarki. Wannan ruhun shi ne ikon da ake yin amfani da shi a dukan mu’ujizan da muka karanta game da su, har da mafi girma a cikin su, wato, ta da Yesu Kristi daga matattu zuwa rai a matsayin ruhu mai iko sosai.—Farawa 1:2; 2 Samuila 23:2; Ayukan Manzanni 10:38; 1 Bitrus 3:18.
[Taswira a shafi na 24]
Farawa
Fitowa
Levitikus
Littafin Lissafi
Kubawar Shari’a
Joshua
Alƙalawa
Ruth
1 Sama’ila
2 Sama’ila
1 Sarakuna
2 Sarakuna
1 Labarbaru
2 Labarbaru
Ezra
Nehemiya
Esther
Ayuba
Zabura
Misalai
Mai-Wa’azi
Waƙar Waƙoƙi
Ishaya
Irmiya
Makoki
Ezekiel
Daniyel
Hosiya
Joel
Amos
Obadiya
Yunana
Mikah
Nahum
Habakkuk
Zafaniya
Haggai
Zakariya
Malakai
● Matta
● Markus
● Luka
● Yohanna
Ayyukan Manzanni
Romawa
1 Korintiyawa
2 Korintiyawa
Galatiyawa
Afisawa
Filibiyawa
Kolosiyawa
1 Tasalonikawa
2 Tasalonikawa
1 Timotawus