Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • rk sashe na 4 pp. 10-11
  • Wane ne Allah?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Wane ne Allah?
  • Cikakken Imani Zai Sa Ka Yi Farin Ciki a Rayuwa
  • Makamantan Littattafai
  • Mala’iku ‘Ruhohi Ne Masu-hidima’
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
  • Su Waye ne ko Kuma Mene ne Ake Nufi da Mala’iku?
    Amsoshin Tambayoyi Daga Littafi Mai Tsarki
  • Akwai Wanda Ya Taba Ganin Allah Kuwa?
    Amsoshin Tambayoyi Daga Littafi Mai Tsarki
  • Su Waye Suke Zama a Duniya ta Ruhu?
    Hanyar Rai Madawwami​—Ka Same ta Kuwa?
Dubi Ƙari
Cikakken Imani Zai Sa Ka Yi Farin Ciki a Rayuwa
rk sashe na 4 pp. 10-11

SASHE NA 4

Wane ne Allah?

MUTANE suna bauta wa alloli masu yawa. Amma Nassosi Masu Tsarki sun koyar da cewa Allah na gaskiya guda ɗaya ne tak. Ba shi da makamanci, shi ne maɗaukaki, kuma madawwami. Shi ne ya halicci komi a sama da ƙasa, kuma ya ba mu rai. Saboda haka, shi kaɗai ne ya cancanci mu bauta ma wa.

Musa yana rike da allon dutse na Dokoki Goma

An ba da Dokar ta hanyar annabi Musa ne a matsayin “maganan wanda aka faɗi ta bakin mala’iku”

Allah yana da suna. Kuma sunan shi ne JEHOBAH. Allah ya gaya wa Musa: “Hakanan za ka ce ma ’ya’yan Isra’ila, Yahweh, [“Jehobah” NW] Allah na ubanninku, Allah na Ibrahim, Allah na Ishaƙu, Allah na Yaƙub, ya aike ni gareku: wannan shi ne sunana har abada, shi ne kuma inda za a tuna da ni har tsararaki duka.” (Fitowa 3:15) Sunan nan Jehobah ya bayyana sau 7,000 a cikin Nassosi Masu Tsarki. Kamar yadda Zabura 83:18 ta ce game da Allah, ‘kai, wanda sunanka Jehobah ne, kai kaɗai ne Maɗaukaki bisa dukan duniya.’

Wani nassi a Takardan Tekun Gishiri da ke dauke da sunan Allah

Rubutaccen nassi na Dead Sea Scroll na dā da ke ɗauke da sunan Allah

Babu ɗan Adam ɗin da ya taɓa ganin Allah. Allah ya gaya wa Musa: “Ba ka da iko ka ga fuskata: gama mutum ba shi ganina shi rayu.” (Fitowa 33:20) Allah yana zaune ne a sama kuma ’yan Adam ba za su iya ganinsa ba. Zunubi ne a ƙera ko kuma a yi addu’a ga gunki, hoto ko kuwa siffar Allah. Jehobah Allah ya ba da doka ta hanyar annabi Musa: “Ba za ka misalta wata ƙira, ko surar abin da ke cikin sama daga bisa, ko abin da ke cikin duniya daga ƙasa, ko kuwa abin da ke cikin ruwa daga ƙarƙashin ƙasa: ba za ka yi sujada garesu ba, ba kuwa za ka bauta musu ba: gama ni Ubangiji Allahnka Allah mai-kishi ne.” (Fitowa 20:2-5) Bayan haka, ta bakin annabi Ishaya, Allah ya ce: “Ni ne Ubangiji [“Jehobah” NW]; wannan ne sunana: ba ni kuwa bada ɗaukakata ga wani, yabona kuma ga sifofi sassaƙaƙu.”—Ishaya 42:8.

Wasu sun yi imani da Allah amma suna iya ɗaukansa a matsayin wanda ba za a iya sani ba balle a kusace shi, wanda za a ji tsoronsa maimakon a ƙaunace shi. Mene ne ra’ayinka? Allah ya damu da kai kuwa? Za ka iya saninsa kuwa da gaske, har ma ka kusace shi? Bari mu ga abin da Nassosi suka ce game da ainihin halayen Allah.

Yaya Za Ka Amsa?

  • Me ya sa za mu bauta wa Allah?

  • Mene ne sunan Allah?

  • Me ya sa bai dace mu yi amfani da gumaka ko siffofi a bautarmu ga Allah ba?

  • Ta yaya Allah yake amfani da ruhunsa mai tsarki da kuma mala’ikunsa wajen cika nufinsa?

Ruhu Mai Tsarki da Mala’ikun Allah

Ta yaya Allah yake cim ma nufinsa? Hanya ɗaya ita ce ta aiko da ruhunsa mai tsarki. Ruhun Allah ba mutum ba ne ko mala’ika, amma iko ne marar iyaka da ba za mu iya gani ba wanda Allah yake amfani da shi don cim ma duk abin da yake so. Allah ya yi amfani da wannan ikon wajen halittar sama da duniya. “Da maganar Ubangiji aka yi sammai; rundunansu duka kuma da lumfashin bakinsa [wato ruhunsa mai tsarki].” (Zabura 33:6) Farawa 1:2 ta bayyana cewa sa’ad da duniya take cike da ruwa kuma Allah ya shirya duniya don ’yan Adam su zauna a cikinta, “ruhun Allah kuwa yana motsi a bisa ruwaye.” Allah ya yi amfani da ruhunsa mai tsarki don ya halicci dukan rai da ke cikin duniya.

Allah yana kuma yin amfani da mala’iku don ya cika nufinsa. Allah ya halicce su ne don su kasance a sama tare da shi. Mala’iku suna da ƙarfi sosai. Suna idar da saƙo daga Allah kuma suna yin ayyuka masu muhimmanci. Alal misali, Nassosi sun kira Dokar da aka ba Musa “magana wanda aka faɗi ta bakin mala’iku.” Mala’ikun Allah suna kuma taimaka wa bayinsa a duniya. Hakika, Nassosi sun kira mala’ikun Allah “ruhohi masu-hidima ne, aikakku domin su yi hidima sabili da waɗanda za su gaji ceto.”—Ibraniyawa 1:14; 2:2.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba