Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • ll kashi 8 pp. 18-19
  • Mece Ce Ma’anar Mutuwar Yesu a Gare Ka?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Mece Ce Ma’anar Mutuwar Yesu a Gare Ka?
  • Ka Saurari Allah Don Ka Rayu Har Abada
  • Makamantan Littattafai
  • Sashe na 8
    Ka Saurari Allah
  • Mene ne Mulkin Allah?
    Me Za Mu Koya Daga Littafi Mai Tsarki?
  • Menene Mulkin Allah?
    Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?
  • Game da Mulkin Allah
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
Dubi Ƙari
Ka Saurari Allah Don Ka Rayu Har Abada
ll kashi 8 pp. 18-19

SASHE NA 8

Mece Ce Ma’anar Mutuwar Yesu a Gare Ka?

Yesu ya mutu domin mu rayu. Yohanna 3:16

Wasu mata suna leka wurin da aka sa gawar Yesu

Kwanaki uku bayan mutuwar Yesu, wasu mata sun ziyarci kabarinsa kuma suka tarar da cewa babu kome a cikinsa. Jehobah ya riga ya ta da Yesu daga matattu.

Yesu ya bayyana a gaban manzanninsa, daga baya ya koma sama

Daga baya, Yesu ya bayyana ga manzanninsa.

Hakika, Jehobah ya ta da Yesu a matsayin ruhu mai iko, marar mutuwa. Almajiran Yesu sun gan shi sa’ad da yake komawa sama.

  • Mene ne sakamakon zunubi?—Romawa 6:23.

  • Yesu ya buɗe hanyar samun rai madawammi.—Romawa 5:21.

Allah ya ta da Yesu daga matattu kuma ya naɗa shi Sarkin Mulkin Allah. Daniyel 7:13, 14

Yesu yana mulki bisa mutanen da suke aljanna a kan kursiyinsa

Yesu ya ba da ransa don ya fanshi ’yan Adam. (Matta 20:28) Ta hanyar fansar nan, Allah ya buɗe mana hanyar yin rayuwa har abada.

Jehobah ya naɗa Yesu ya zama Sarki don ya yi mulki bisa duniya. Mutane 144,000 masu aminci da aka ta da daga matattu a duniya ne za su kasance tare da shi a sama. Yesu da mutane 144,000 ne za su zama sarakuna a wannan gwamnati mai adalci na samaniya, wato Mulkin Allah.—Ru’ya ta Yohanna 14:1-3.

Mulkin Allah zai mai da duniya aljanna. Yaƙi, laifi, talauci, da yunwa za su zama labari. Mutane za su kasance da farin ciki sosai.—Zabura 145:16.

  • Waɗanne albarka ne Mulkin zai kawo?—Zabura 72.

  • Muna bukatar mu yi addu’a Mulkin Allah ya zo.—Matta 6:10.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba