Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • T-33 pp. 1-4
  • Wane Ne Ainihi Yake Iko Da Duniya?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Wane Ne Ainihi Yake Iko Da Duniya?
  • Wane Ne Ainihi Yake Iko Da Duniya?
  • Makamantan Littattafai
  • Mene Ne Ra’ayinka Game Da Nan Gaba?
    Mene Ne Ra’ayinka Game Da Nan Gaba?
  • Mene ne Mulkin Allah?
    Mene ne Mulkin Allah?
  • Matattu Za Su Sake Rayuwa Kuwa?
    Matattu Za Su Sake Rayuwa Kuwa?
  • Wahala Za Ta Ƙare Kuwa?
    Wahala Za Ta Ƙare Kuwa?
Dubi Ƙari
Wane Ne Ainihi Yake Iko Da Duniya?
T-33 pp. 1-4

Wane Ne Ainihi Yake Iko Da Duniya?

Kana ganin . . .

  • Allah ne?

  • ’yan Adam ne?

  • ko wani halitta dabam?

ABIN DA LITTAFI MAI TSARKI YA CE

“Duniya duka kuwa tana hannun Mugun.”—1 Yohanna 5:19, Littafi Mai Tsarki.

“Dalilin bayyanar Ɗan Allah shi ne domin ya rushe aikin Iblis.”—1 Yohanna 3:8.

ABIN DA ZA KA IYA MORA IDAN KA GASKATA DA HAKAN

Za ka sami ingantaccen bayani game da abin da ya sa munanan abubuwa suke faruwa a duniya.—Ru’ya ta Yohanna 12:12.

Tabbataccen hujja na ba da gaskiya cewa za a sami canji da zai sa mutane su ji daɗin rayuwa a duniya.—1 Yohanna 2:17.

Shaidan ne ke ja-gorancin siyasa da ake yi a duniya da sojoji da addinai da kuma mutane

ZA MU IYA GASKATA DA LITTAFI MAI TSARKI KUWA?

Hakika, aƙalla saboda waɗannan dalilai uku:

  • Za a kawo ƙarshen mulkin Shaiɗan. Tabbas, Jehobah zai kawo ƙarshen sarautar Shaiɗan bisa ’yan Adam. Jehobah ya yi alkawari cewa zai “halakar da . . . Iblis” kuma ya gyara dukan abubuwan da Shaiɗan ya ɓata.—Ibraniyawa 2:14.

  • Allah ya zaɓi Yesu Kristi ya yi mulkin duniya. Halin Yesu ya bambanta sosai da na wannan mugun, mai son zuciya da ke mulkin duniya a yanzu. Allah ya yi alkawari game da mulkin Yesu cewa: ‘Za ya nuna tausayi ga matalauci da mai-rashi, za ya kuwa cece su . . . daga zalunci da ƙwace.’—Zabura 72:13, 14.

  • Allah ba ya ƙarya. Littafi Mai Tsarki ya bayyana ɓaro-ɓaro cewa: “Ba shi yiwuwa Allah ya yi ƙarya.” (Ibraniyawa 6:18) Idan Jehobah ya yi alkawarin yin wani abu, kamar dai an gama! (Ishaya 55:10, 11) “Za a fitar da mai-mulkin wannan duniya.”—Yohanna 12:31.

KA YI TUNANI A KAN WANNAN TAMBAYAR

Mambobin iyali sun fita shakatawa

Yaya duniya za ta kasance bayan an kawar da mai mulkinta?

Littafi Mai Tsarki ya ba da amsar a ZABURA 37:10, 11 da kuma RU’YA TA YOHANNA 21:3, 4.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba