Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • kr babi na 20 pp. 209-219
  • Hidimar Agaji

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Hidimar Agaji
  • Mulkin Allah Yana Sarauta!
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Abin da Ya Sa Aikin Agaji “Tsarkakkiyar Hidima” Ce
  • Abubuwan da Ake Cim Ma ta Wajen Ba da Agaji
  • Aikin Agaji Yana Kawo Albarka na Dindindin
  • Za Ka Iya Taimakawa?
  • Yadda Za Mu Taimaka Bayan Wani Balaꞌi
    Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2023
  • Kuna Ba da Agaji a Lokacin da Bala’i Ya Auku Kuwa?
    Tambayoyin da Ake Yawan Yi
  • Tallafa Wa Mulkin​—Yin Gini Domin Ibada da Kuma Ba da Agaji
    Mulkin Allah Yana Sarauta!
  • Aikinmu Na Ba da Agaji
    Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2019
Dubi Ƙari
Mulkin Allah Yana Sarauta!
kr babi na 20 pp. 209-219

BABI NA 20

Hidimar Agaji

MANUFAR WANNAN BABIN

Ƙauna tana motsa Kiristoci su ɗauki mataki a lokacin bala’i

1, 2. (a) Wane mawuyacin hali ne Kiristoci da ke Yahudiya suka sami kansu a ciki? (b) Ta yaya Kiristoci da ke Yahudiya suka san cewa ’yan’uwansu a wasu wurare suna ƙaunarsu?

A WAJEN shekara ta 46 a zamaninmu an yi yunwa mai tsanani a Yahudiya. Saboda ƙarancin abinci, Yahudawa almajiran Yesu ba su iya sayan abinci ba don ya yi tsada sosai. A sakamakon haka, sun yi fama da yunwa sosai. Amma a wannan lokacin, Jehobah ya kula da su a wata muhimmiyar hanya da ba su taɓa tsammani ba. A wace hanya ke nan?

2 Sa’ad da Kiristoci da ke zama a Antakiya da Suriya suka ga yadda Kiristoci a Urushalima da Yahudiya suke shan wahala, sai suka yi gudummawar kuɗi don taimaka wa waɗannan ’yan’uwansu masu bi. Bayan haka, sai suka zaɓi ’yan’uwa biyu da aka yarda da su, wato Barnaba da Shawulu, don su kai kayan agaji ga dattawan ikilisiyar da ke Urushalima. (Karanta Ayyukan Manzanni 11:27-30; 12:25.) Ka yi tunanin yadda ’yan’uwa mabukata da ke Yahudiya suka ji saboda ƙaunar da Kiristoci da ke Antakiya suka nuna musu. Hakika, hakan ya ƙarfafa su sosai!

3. (a) Ta yaya bayin Allah a yau suke bin gurbin Kiristoci na farko da ke Antakiya? Ka ba da misali. (Ka kuma duba akwatin nan “Gagarumin Aikin Agaji da Muka Soma Yi a Zamaninmu.”) (b) Waɗanne tambayoyi ne za mu tattauna a wannan babin?

3 A ƙarni na farko, wannan shi ne agaji na farko da Kiristoci a wata ƙasa suka aika wa ’yan’uwansu Kiristoci da ke zama a wata ƙasa dabam. A yau, muna bin gurbin ’yan’uwanmu da ke Antakiya. Muna taimakon ’yan’uwanmu da ke wani wuri idan muka ji cewa bala’i ya shafe su ko kuma sun shiga wani mawuyacin hali.a Don mu fahimci alaƙar da ke tsakanin aikin agaji da kuma sauran ayyukan ibada, bari mu tattauna tambayoyi uku game da hidimar agaji: Me ya sa muka ɗauki aikin agaji a matsayin hidima ga Allah? Mene ne ake cim ma ta aikin agaji? Ta yaya muke amfana daga hidima ta agaji?

Abin da Ya Sa Aikin Agaji “Tsarkakkiyar Hidima” Ce

4. Mene ne Bulus ya bayyana wa ’yan’uwa da ke Korinti game da hidimar Kirista?

4 A wasiƙa ta biyu da Manzo Bulus ya rubuta zuwa ga ’yan’uwa a Korinti, ya bayyana cewa hidimar da Kiristoci suke yi tana da fannoni biyu. Ko da yake ya rubuta wasiƙar ne ga shafaffun Kiristoci, amma abin da ya faɗa ya shafi “waɗansu tumaki” na Kristi. (Yoh. 10:16) Fanni ɗaya na hidimar shi ne “hidima ta sulhu,” wato wa’azi da koyarwa da muke yi. (2 Kor. 5:18-20; 1 Tim. 2:3-6) Fanni na biyu kuma shi ne hidimar agaji da muke yi wa ’yan’uwanmu masu bi. Wannan ne Bulus ya ambata sa’ad da ya yi maganar “hidima ga tsarkaka.” (2 Kor. 8:4) Wannan kalmar “hidima” da aka ambata sa’ad da aka yi maganar ‘hidima ta sulhu’ da kuma ‘hidima ga tsarkaka,’ kalma ce da aka fassara daga harshen Helenanci, wato di·a·ko·niʹa. Me ya sa aka yi amfani da wannan kalmar a waɗannan ayoyin?

5. Me ya sa Bulus ya ce aikin agaji hidima ce ga Allah?

5 Sa’ad da Bulus ya yi amfani da kalmar nan “hidima” wajen kwatanta yin wa’azi da kuma na agaji, yana nuna cewa ba da agaji fanni ɗaya ne na hidimar da muke yi a cikin ikilisiyar Kirista. Kafin ya ambaci hakan, ya ce: ‘Akwai hidimomi kuma iri iri, Ubangiji kuwa ɗaya ne. Akwai kuma aike aike iri iri, . . . Amma dukan waɗannan shi wannan ruhu ɗaya ya ke aikata su.’ (1 Kor. 12:4-6, 11) Hakika, Bulus ya kwatanta hidimomi dabam-dabam da ake yi a cikin ikilisiya da ‘bauta’ ko kuma tsarkakkiyar hidima.b (Rom. 12:1, 6-8) Shi ya sa ya ga cewa ya dace ya yi amfani da lokacinsa don ‘yi wa tsarkakku hidima!’—Rom. 15:25, 26.

6. (a) Me ya sa Bulus ya ce aikin agaji sashe ne na ibadarmu ga Allah? (b) Ka bayyana yadda muke gudanar da aikin agaji a faɗin duniya a yau. (Ka duba akwatin nan “Sa’ad da Bala’i Ya Auku!” a shafi na 214.)

6 Bulus ya taimaka wa Korintiyawa su fahimci cewa ba da agaji hidima ce kuma ibada ce ga Jehobah. Yana nufin Kiristoci da suke ba da agaji suna yin hakan ne don suna ‘biyayya . . . ga bisharar Kristi.’ (2 Kor. 9:13) Wato, Kiristoci suna taimaka wa ’yan’uwansu masu bi ne don suna bin koyarwar Kristi. Bulus ya ce waɗannan ayyukan alheri da suke yi a madadin ’yan’uwansu yana bayyana “mafificin alherin Allah.” (2 Kor. 9:14; 1 Bit. 4:10) Saboda da haka, sa’ad da Hasumiyar Tsaro ta 1 ga Disamba, 1975, ta yi magana game da taimaka wa ’yan’uwanmu, ta ce: “Kada mu yi tunanin cewa Jehobah Allah da Ɗansa Yesu ba sa ɗaukan irin wannan hidimar da muhimmanci.” Babu shakka, ba da agaji fanni ne da ke da muhimmanci a bautarmu ga Jehobah.—Rom. 12:1, 7; 2 Kor. 8:7; Ibran. 13:16.

Abubuwan da Ake Cim Ma ta Wajen Ba da Agaji

7, 8. Mene ne abu na farko da ake cim ma a aikin agaji? Ka bayyana.

7 Waɗanne abubuwa ne ake cim ma a ba da agaji? Bulus ya ba da amsar wannan tambayar a cikin wasiƙarsa ta biyu zuwa ga Korintiyawa. (Karanta 2 Korintiyawa 9:11-15.) A cikin waɗannan ayoyin, Bulus ya ambaci abubuwa uku da ake cim ma idan muka saka hannu a “aikin nan na alheri,” wato ba da agaji. Bari mu tattauna su ɗaya bayan ɗaya.

8 Na farko, ba da agaji da muke yi yana ɗaukaka Jehobah. Ka lura da yadda Bulus ya taimaka wa ’yan’uwansa su girmama Jehobah Allah a littafin 2 Korintiyawa 9:11-15 da aka ambata a baya. Manzon ya ce su riƙa yin “godiya ga Allah” kuma su “yawaita godiya ga Allah.” (Ayoyi 11 da 12) Ya ce ba da agaji yana sa Kiristoci su “ɗaukaka Allah” kuma su ɗaukaka “alherin Allah marar misaltuwa.” (Ayoyi 13 da 14) Bulus ya ambaci “godiya ga Allah” kafin ya kammala maganarsa game da hidimar agaji.—Aya ta 15; 1 Bit. 4:11.

9. Ta yaya aikin agaji zai sa mutane su daina kasancewa da mummunan ra’ayi? Ka ba da misali.

9 Ga bayin Allah a yau, ba da agaji hanya ce ta ɗaukaka Jehobah da kuma nuna cewa suna bin koyarwarsa. (1 Kor. 10:31; Tit. 2:10) Hakika, ba da agaji muhimmiyar hanya ce ta taimaka wa mutane su daina kasancewa da mummunan ra’ayi game da Jehobah Allah da kuma Shaidunsa. Alal misali: A wani yanki, wata mata ta saka wata alama a ƙofar gidanta da ke cewa: “Shaidun Jehobah, Kada Ku Zo Wa’azi a Nan.” Sa’ad da bala’i ya addabi yankin, sai matar ta lura da wasu masu aikin agaji da suke gyara gidan wani da bala’in ya shafa kusa da gidanta. Ta yi kwanaki tana lura da yadda masu aikin suke fara’a, sai ta je wurin don ta san ko su wane ne waɗannan mutanen. Sa’ad da ta gane cewa masu aikin agajin Shaidun Jehobah ne, abin ya burge ta kuma ta ce, “Na yi muku bahaguwar fahimta.” Mene ne sakamakon haka? Matar nan ta cire wannan alamar daga ƙofarta.

10, 11. (a) Waɗanne misalai ne suka nuna cewa muna cim ma maƙasudi na biyu a aikin agaji? (b) Wace ƙasida ce ta taimaka wa masu aikin agaji? (Ka duba akwatin nan “Sabuwar Ƙasida Don Masu Aikin Agaji.”)

10 Na biyu, muna ‘biyan bukatun’ ’yan’uwanmu masu bi. (2 Kor. 9:12a) Muna marmarin taimaka wa ’yan’uwanmu da kuma sauƙaƙa musu wahala idan bukata ta kama. Me ya sa? Don dukan waɗanda ke cikin ƙungiyar Jehobah suna nan kamar ‘jiki ɗaya’ ne, kuma “idan gaɓa ɗaya kuwa ya sha raɗaɗi, dukan gaɓaɓuwa suna shan raɗaɗi tare da shi.” (1 Kor. 12:20, 26) Saboda haka, ƙauna da tausayi suna motsa ’yan’uwa maza da mata a yau su bar aikinsu nan take kuma su tattara kayan aiki zuwa inda aka yi bala’i don taimaka wa ’yan’uwansu. (Yaƙ. 2:15, 16) Alal misali, bayan tsunami ya addabi Japan a shekara ta 2011, ofishin reshe na Amirka ya aika wasiƙa zuwa ga Kwamitocin Gine-gine na Yanki da ke Amirka. Wasiƙar ta ce ana bukatar “’yan’uwa kaɗan da suka cancanta” don su taimaka da sake gina Majami’un Mulki a Japan. “Mutane nawa ne suka amsa wannan kira? Cikin makonni, kusan ’yan’uwa 600 ne suka ba da sunansu cewa za su taimaka, kuma sun amince su biya kuɗin jirgi daga aljihunsu zuwa Japan! Ofishin reshe na Amirka ya ce: “Yawan mutanen da suka amsa wannan kira ya ba mu mamaki sosai.” Sa’ad da wani ɗan’uwa ya tambayi wani mai taimako da ya zo daga wata ƙasa dalilin da ya sa ya ba da kai don ya taimaka, amsar da aka ba shi ita ce: “’Yan’uwanmu da ke Japan suna kamar gaɓar ‘jikinmu’ ne. Muna jin wahalar da suke sha.” Masu aikin agaji suna sadaukar da kai don su taimaka wa ’yan’uwansu, wani lokaci ma sukan sa ransu cikin haɗari don suna ƙaunar ’yan’uwansu.c—1 Yoh. 3:16.

Wata Mashaidiyar Jehobah tana shirya kayan agaji don ’yan’uwan da ke Siwizalan a shekara ta 1946

Shekara ta 1946, Siwizalan

GAGARUMIN AIKIN AGAJI DA MUKA SOMA YI A ZAMANINMU

A SATUMBA na shekara ta 1945, ’yan watanni bayan Yaƙin Duniya na Biyu a Turai, Ɗan’uwa Knorr ya yi sanarwa game da wani gagarumin kamfen na aika “kayan agaji wa ’yan’uwa mabukata da ke tsakiyar Turai.”

Cikin ’yan makonni bayan wannan sanarwar, Shaidu da ke Kanada da Amirka da wasu ƙasashe suka soma karɓan tufafi da kuma abinci. Daga watan Janairu 1946, aka aika kaya zuwa ga ’yan’uwa da ke Austria da Belgium da Bulgaria da Caina da Czechoslovakia da Denmark da Ingila da Finland da Faransa da Jamus da Girka da Hungary da Italiya da Netherlands da Norway da Filifin da Poland da kuma Romaniya.

Wannan aikin agajin ba na gajeren lokaci ba ne. An yi shekaru biyu da rabi ana aika kayan agaji! A wannan lokacin, ’yan’uwa wajen 85,000 ne suka aika abinci mai yawan kilo wajen 300,000 da tufafi mai nauyin wajen kilo 450,000 da takalma da suka wuce yawan 124,000 ga ’yan’uwansu da ke ƙasashe da yaƙi ya addaba. A Agusta na shekara ta 1948 ne aka kammala wannan aikin agajin. A shekara ta 1949, Hasumiyar Tsaro ta ambata cewa: “Hakika, wannan hanyar nuna ƙauna ce ga juna. Mun san cewa duka ’yan’uwa sun yi hakan ne don girmama Ubangiji, da yake sun san cewa wannan taimakon agaji zai ba wa ’yan’uwansu damar ci gaba da ibada ta gaskiya; saboda da haka, yi wa ’yan’uwansu hidima ta wannan hanyar babban gata ne a gare su.” Wannan aikin agaji ya ɗaukaka Jehobah kuma ya sa ’yan’uwa a faɗin duniya sun ƙara kasancewa da haɗin kai.

11 Ƙari ga haka, mutanen da ba Shaidun Jehobah ba suna godiya don aikin agajin da muke yi. Alal misali, bayan wani bala’i ya addabi jihar Arkansas, a Amirka, a shekara ta 2013, wata jarida ta ba da rahoto game da yadda Shaidun Jehobah suke saurin zuwa inda aka yi bala’i don su taimaka. Jaridar ta ce: “Shaidun Jehobah sun ƙware sosai wajen tsara aikin agaji don suna zuwa inda bala’i ya auku ba tare da ɓata lokaci ba.” Hakika, muna ‘biyan bukatun’ ’yan’uwanmu da kyau kamar yadda manzo Bulus ya faɗa.

12-14. (a) Me ya sa yake da muhimmanci mu cim ma maƙasudi na uku na aikin agaji? (b) Waɗanne kalamai ne suka nuna cewa ci gaba da ayyuka na ibada yana da muhimmanci?

12 Na uku, muna taimaka wa waɗanda bala’i ya shafa su sake ci gaba da ayyukansu na ibada. Me ya sa hakan yake da muhimmanci? Bulus ya ambata cewa agajin da ’yan’uwa suka karɓa zai motsa su su miƙa “godiya mai-yawa zuwa ga Allah.” (2 Kor. 9:12b) Babu shakka, hanya mafi muhimmanci da waɗannan za su nuna godiyarsu ga Allah ita ce ta sake ci gaba da ayyukansu na ibada ba tare da ɓata lokaci ba. (Filib. 1:10) A shekara ta 1945, an ambata a cikin Hasumiyar Tsaro cewa: “Bulus ya ce a yi . . . gudummawa don tana taimaka wa . . . Kiristoci mabukata su sami abin biyan bukata da damar yin wa’azi da ƙwazo.” Hakazalika, abin da aikin agaji yake cim ma ke nan a yau. Idan ’yan’uwa suka sake ci gaba da wa’azi, suna ƙarfafa maƙwabtansu da ke baƙin ciki kuma ta hakan, suna ƙarfafa kansu.—Karanta 2 Korintiyawa 1:3, 4.

13 Wasu da suka ci gaba da hidima bayan sun sami agaji sun ce sun sami ƙarfafa sa’ad da suka fita wa’azi. Bari mu yi la’akari da abin da suka faɗa. Wani ɗan’uwa ya ce: “Mun amfana sosai sa’ad da muka fita wa’azi. Yayin da muke ƙoƙarin ƙarfafa wasu, mun sami kwanciyar hankali don mun ɗan manta da damuwarmu.” Wata ’yar’uwa ta bayyana cewa: “Mai da hankali ga ayyukan ibada ya sa na manta da bala’in da ya faru. Ya sa hankalina ya kwanta.” Wata ’yar’uwa ta ƙara da cewa: “Ko da yake ba za mu iya sarrafa wasu abubuwa da ke faruwa ba, fita wa’azi ya sa iyalinmu ta kasance da bege. Yi wa wasu magana game da alkawarin sabuwar duniya ya sa mun ƙara kasancewa da tabbaci cewa Jehobah zai sake mai da kome sabo.”

14 Wani aiki na ibada kuma da muke taimaka wa ’yan’uwanmu da bala’i ya shafa su sake ci gaba da yi ba tare da ɓata lokaci ba shi ne halartan taro. Ka yi la’akari da abin da ya faru da wata ’yar’uwa mai suna Kiyoko da ta ba shekaru hamsin da biyar baya. Wani tsunami ya addabe su sakamakon haka, ta yi asarar dukan mallakarta. Abin da suka rage kawai su ne tufafi da takalma da take sanye da su. Hakan ya sa ta damu sosai kuma ta rasa abin za ta yi. Sai wani dattijo ya gaya mata cewa za su riƙa yin taron Kirista a cikin motarsa. Kiyoko ta ce: “Wani dattijo da matarsa da ni da wata ’yar’uwa ne muka zauna a cikin motar. An gudanar da taron a sawwaƙe, amma wani abin mamaki ya faru, na manta gaba ɗaya cewa tsunami ya faru. Na sami kwanciyar rai. A wannan taron, na fahimci cewa tarayya da ’yan’uwa Kirista yana da amfani sosai.” Wata ’yar’uwa ta yi kalami game da taron da ta halarta bayan da wani bala’i ya addabe su, ta ce: “Waɗannan taron sun taimaka min in jure!”—Rom. 1:11, 12; 12:12.

Aikin Agaji Yana Kawo Albarka na Dindindin

15, 16. (a) Wace albarka ce ’yan’uwa da ke Korinti da kuma wasu wurare za su samu ta wajen yin aikin agaji? (b) Ta yaya muke amfana daga aikin agaji a yau?

15 Sa’ad da manzo Bulus yake tattauna batun hidimar agaji, ya bayyana wa Korintiyawa da wasu Kiristoci albarka da irin wannan aikin yake kawowa. Da yake magana a madadin Kiristoci da ke Urushalima da suka karɓi agaji, ya ce: ‘Su kuwa da kansu, yayinda suna roko dominku, suna begenku saboda mafificin alherin Allah da ke cikinku.’ (2 Kor. 9:14) Hakika, karimci da Korintiyawa suka yi zai sa Kiristoci Yahudawa su yi addu’a a madadinsu da kuma waɗanda suka fito daga al’ummai, kuma hakan zai sa ’yan’uwa Yahudawa su ƙara ƙaunar su.

16 Ta yaya za mu amfana daga abin da Bulus ya faɗa game da albarkar da ake samu don aikin agaji? Hasumiyar Tsaro ta 1 ga Disamba, 1945, ta bayyana cewa: “Sa’ad da bayin Allah suka yi gudummawa don biyan bukatun ’yan’uwansu da ke zama a wani ɓangare dabam, hakan yana ƙara haɗa kanmu!” Abin da masu aikin agaji suke mora ke nan. Wani dattijo da ya taimaka a wani aikin agaji sa’ad da ambaliyar ruwa ta addabi wani yanki, ya ce: “Saka hannu a aikin agaji ya sa na yi kusa da ’yan’uwana sosai.” Wata ’yar’uwa da ta amfana daga aikin agaji ta ce: “’Yan’uwantaka da muke mora a ƙungiyar Jehobah ce kawai za mu ɗan kwatanta Aljanna a duniya da shi.”—Karanta Misalai 17:17.

17. (a) Ta yaya kalmomin da ke Ishaya 41:13 ya ke cika a aikin agaji? (b) Ka ba da wasu misalai da ke nuna yadda aikin agaji yake ɗaukaka Jehobah da kuma ƙara haɗa kanmu. (Ka duba akwatin nan “’Yan’uwa a Faɗin Duniya Sun Taimaka da Aikin Agaji.”)

17 Sa’ad da masu aikin agaji suka isa inda bala’i ya auku, ’yan’uwanmu da abin ya shafa sukan ga cikar wannan alkawarin da Allah ya yi sa’ad da ya ce: “Ni Ubangiji Allahnka zan riƙe hannun damanka, . . . Kada ka ji tsoro, ni taimake ka.” (Isha. 41:13) Wata ’yar’uwa da ta tsira daga wani bala’i ta ce: “Sa’ad da na ga abin da ya faru, na karaya, amma Jehobah ya taimake ni. Ba zan iya kwatanta taimakon da ’yan’uwa suka yi mini ba.” Bayan wani bala’i ya addabi yankinsu, wasu dattawa guda biyu sun rubuta wasiƙa a madadin ikilisiyoyinsu, sun ce: “Girgizar ƙasar ta sa mu baƙin ciki sosai amma mun amfana daga taimakon da Jehobah yake tanadarwa ta wurin ’yan’uwanmu. A dā muna karanta yadda ake yin aikin agaji ne kawai, amma yanzu mun ga yadda ake gudanarwa da idanunmu.”

Peter Johnson working on a theocratic building project

AIKIN AGAJI YA YI TASIRI A RAYUWARSA

TA YAYA yin aikin agaji zai iya shafan rayuwar matasa? Ka yi la’akari da abin da ya faru da Peter Johnson, wanda ya yi hakan sa’ad da yake ɗan shekara 18. Ya ce: “Godiya da ’yan’uwa suke yi da kuma farin ciki da bayarwa ke kawowa sun taɓa ni ƙwarai. Hakan ya sa na ƙara kasancewa da sha’awar bauta wa Jehobah da ƙwazo sosai.” Bayan haka, sai ya soma hidimar majagaba. Da shigewar lokaci, ya yi hidima a Bethel kuma daga baya ya soma hidima a matsayin memban Kwamitin Gini na Yanki. Peter ya ƙara da cewa: “Yin aikin agaji da na soma yi a shekara ta 1974, ya yi tasiri a rayuwata.” Kai matashi ne? Shin za ka iya bin gurbin Peter? Kai ma wataƙila aikin agaji zai yi tasiri a rayuwarka yayin da kake bauta wa Jehobah!

Za Ka Iya Taimakawa?

18. Mene ne za ka iya yi ɗaukawa idan kana so ka yi aikin agaji? (Ka duba akwatin nan “Aikin Agaji Ya Yi Tasiri a Rayuwarsa.”)

18 Za ka so ka mori farin cikin da ke tattare da aikin agaji? Idan kana so, ka tuna cewa ana zaɓan masu aikin agaji ne daga masu aikin gine-gine na Majami’ar Mulki. Saboda haka, ka gaya wa dattawa da ke ikilisiyarku cewa kana so ka cika afilkeshan ɗin. Wani dattijo da ya daɗe yana aikin agaji, ya ba da wata shawara cewa: “Kada ka je inda bala’i ya auku idan ba ka sami wasiƙa daga Kwamitin Aikin Agaji ba.” Idan muka bi shawarar nan, aikin agajin da muke yi zai kasance da tsari.

19. Ta yaya masu aikin agaji suke sa a san cewa mu almajiran Yesu ne da gaske?

19 Aikin agaji muhimmiyar hanya ce ta yin biyayya ga umurnin da Yesu ya bayar cewa mu kasance da ‘ƙauna ga junanmu.’ (Yoh. 13:34, 35) Hakika, kasancewa da masu aikin agaji da son rai da ke ɗaukaka Jehobah yayin da suke tanadar da agaji wa waɗanda ke wa’azin Mulkin Allah ba ƙaramar albarka ba ce!

a Wannan babin ya tattauna aikin agaji da ake yi don taimaka wa ’yan’uwa masu bi. Amma, a yawancin lokaci, aikin agaji da muke yi yana amfanar waɗanda ba Shaidun Jehobah ba.—Gal. 6:10.

b Bulus ya yi amfani da jam’in kalmar nan di·aʹko·nos (mai hidima) sa’ad da yake kwatanta “dikon.”—1 Tim. 3:12.

c Ka duba talifin nan “Aiding Our Family of Believers in Bosnia,” da ke shafuffuka na 23-27 na Hasumiyar Tsaro ta 1 ga Nuwamba, 1994, a Turanci.

Ka Gaskata da Mulkin Kuwa?

  • Ta yaya muka san cewa aikin agaji sashe ne na ibadar ga Allah?

  • Waɗanne abubuwa uku na ake cim ma a aikin agaji?

  • Wace albarka na dindindin ce ke tattare da aikin agaji?

  • Mece ce alaƙar da ke tsakanin aikin agaji da umurnin da Yesu ya ba da a Yohanna 13:34?

’YAN’UWA A FAƊIN DUNIYA SUN TAIMAKA DA AIKIN AGAJI

AFIRKA TA TSAKIYA DA KUMA TA YAMMA

A shekara ta 1994, an kashe mutane fiye da 800,000 a kisan ƙare-dangi da aka yi a ƙasar Ruwanda. Bayan kashe-kashen, an sami tashin hankali a wasu ƙasashe da ke Afirka ta Tsakiya. A sakamakon haka, mutane sun yi cunkoso a sansanin gudun hijira. Don su taimaki ’yan’uwansu, Shaidun Jehobah da ke Belgium da Faransa da kuma Siwizalan suka aika da tan 300 na tufafi da magunguna da wajen shimfiɗa da abinci da kuma wasu abubuwa. A cikin makonni, ’yan’uwan da ke neman taimako sun sami kayan agajin.

A Afirka, likitoci da su nas nas guda goma waɗanda Shaidun Jehobah ne daga Faransa sun yi wa ’yan’uwa jinya don su sauƙaƙa musu wahalar da suke fuskanta saboda yaƙin basasa da yunwa da kuma cuta. Cikin shekaru biyu da suka shige kawai, sun yi jinya fiye da sau 10,000. Aikin da suka yi ya girmama Jehobah da kuma ƙungiyarsa. Wata nas daga cikin su ta ce: “Sa’ad da muka isa yankin don mu taimaka wa ’yan’uwanmu, mutane suka soma cewa: ‘Waɗannan Shaidun Jehobah ne. Sun zo ne don su taimaka wa ’yan’uwansu.’” Sa’ad da wata nas ta yi wa wata Mashaidiya jinya, sai Mashaidiyar ta ce: “Na gode miki ’yar’uwata. Na gode maka Jehobah!”

A wasu lokatai, akan bukaci aikin agaji sa’ad da aka yi haɗari mai tsanani. A shekara ta 2012, an yi wani mummunan haɗari a ƙasar Nijeriya. Shaidun Jehobah 13 suka rasa rayukansu kuma 54 suka ji rauni sosai. Dukan Shaidun daga ikilisiya ɗaya ne. Wani kwamitin agaji ya shirya yadda za a kula da kowannensu dare da rana. Wata mata da take kwance a asibitin ta lura da yadda aka kula da ’yan’uwan nan, sai ta yi wa fastonsu waya, ta ce: “Babu wani a cocinmu da ya zo ya ziyarce ni. Ka zo asibiti ka ga yadda Shaidun Jehobah suke ƙaunar ’yan’uwansu!”

Duk da cewa ba ƙaramin rashi ba ne ’yan’uwanmu da ke wannan ikilisiya suka yi, sun sami ƙarfafa sosai saboda ƙaunar da ’yan’uwa masu bi suka nuna musu. Ƙari ga haka, saboda irin ƙaunar da masu aikin agaji suka nuna wa ’yan’uwan nan da haɗarin ya shafa, wasu a cikin ikilisiyar sun daɗa ƙwazo a wa’azi. Kafin haɗarin, ikilisiyar tana da masu shela 35. Amma a cikin shekara ɗaya, adadin masu shelan ya ƙaru zuwa 60.

OSTARELIYA

A shekara ta 2013, ambaliyar ruwa ta addabi wasu sassan gaɓar teku kusa da Queensland. A sakamakon haka, Shaidun Jehobah guda 70 suka rasa gidajensu. Mark da Rhonda, wasu ma’aurata da kuma ’yarsu sun gudu daga gidansu zuwa inda jirage masu saukar ungulu suke kwashe mutane. An cika wurin maƙil. Rhonda ta ce: “Mun kasa zama don babu wurin zama.” Ƙarar jiragen da ke sauka da kuma tashi ta sa yanayin wurin ya daɗa kasancewa da muni. Rhonda ta damu kuma ta tambayi mijinta, “Mene ne za mu yi?” Sai mijinta Mark, ya yi addu’a ga Jehobah don ya taimake su. Rhonda ta ce: “Wajen minti 30 bayan haka, sai wata mota ta zo wurin kuma wasu ’yan’uwa uku suka fito daga cikin motar, suka ce: ‘Mun zo ne mu ɗauke ku. Za ku zauna a gidan wani ɗan’uwa.’ Ba za mu iya kwatanta yadda muka ji a lokacin ba domin irin kulawar da ƙungiyar Jehobah ta nuna mana.”

Masu aikin agaji 250 ne suka je inda bala’in ya auku don su taimaka wa ’yan’uwansu. Wani ɗan’uwa da ya manyanta ya ce: “Wasu Shaidun Jehobah sun yi aiki tuƙuru don su share gidana. Ni da matata ba za mu taɓa mance yadda suka taimake mu ba”

BRAZIL

A shekara ta 2008, ambaliyar laka da ta addabi jihar Santa Catarina ta sa mutane wajen 80,000 sun gudu sun bar gidajensu. Wannan ambaliyar kamar “tsunami ne na taɓo da laka haɗe da bishiyoyi,” in ji wani mazaunan wurin. Wasu ’yan’uwa sun sami mafaka a wani Majami’ar Taro. Wani ɗan’uwa mai suna Márcio shi ne yake kula da Majami’ar, kuma ya ce: “Sun tsira ne da tufafin da suka saka kawai, kuma sun kwaɓu da laka.” Wata ’yar’uwa ta ce: “Gidanmu ya rushe. Ganin yadda gidan ya lalace cikin ’yan mintoci ya sa ni baƙin ciki ƙwarai, amma ba zan taɓa mance yadda ’yan’uwanmu maza da mata suka ƙarfafa mu ba. ’Yan’uwanmu sun kula da mu sosai! Wannan abin da ya faru ya koya mini cewa hikima ce mu riƙa ɗaukan abubuwan da suka shafi dangantakarmu da Jehobah da muhimmanci.”

Shaidun Jehobah suna shirya kayan agaji don ’yan’uwan da ke Brazil

A shekara ta 2009, an yi amfani da Majami’ar Taro na Santa Catarina a ƙasar Brazil don ba da agaji kuma wurin ya cika da kayayyakin agaji

Ambaliyar lakar ta yi ɓarna sosai a unguwoyi da suke gefen tsaunukan da ke kusa da birnin Rio de Janeiro. Don su iya tanadar da taimako a kan kari sa’ad da bala’i ya auku, ’yan’uwa sun kafa Kwamitin Agaji na dindindin kuma idan aka ga alama cewa za a yi ambaliyar laka, masu faɗakarwa (wasu ’yan’uwa da aka zaɓa a yankin) suna faɗakar da kwamitin. Nan da nan bayan haka, masu aikin ceto za su zo a cikin manyan motoci masu ɗauke da alamar nan “Jehovah’s Witnesses—Humanitarian Aid,” (Shaidun Jehobah Masu Ba da Agaji). Ana gaya wa kowane mai aikin ceto abin da zai yi tun da wuri. Masu aikin sukan saka riguna da ke nuna cewa su Shaidun Jehobah ne. Suna aiki tare da Kwamitin Hulɗa da Asibitoci don su yi wa ’yan’uwan da suka ji rauni jinya. Masu aikin agaji suna zuwa da abinci da ruwa da magunguna da tufafi da kuma kayan share-share. Wanke laka daga gidaje ba ƙaramin aiki ba ne. Bayan wata ambaliyar laka, masu taimako guda 60 sun kwashe laka da ya cika manyan motoci huɗu daga gida guda kawai!

YIN SHIRI DON BALA’I

Hukumar da Ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah ta umurci dukan ofisoshin reshe a faɗin duniya su gaya wa dattawan ikilisiyoyi da masu kula masu ziyara yadda za su yi shiri don bala’i da kuma matakan da za su ɗauka sa’ad da bala’i ya auku. Alal misali, kafin bala’i ya auku, ya kamata dattawa su kasance da lambobin waya da kowane mai shela a cikin ikilisiya yake amfani da shi da kuma adireshinsu.

SA’AD DA BALA’I YA AUKU!

  1. Wata ’yar’uwa ta ziyarta wata iyali

    Dattawan ikilisiya suna ƙoƙari su nemi dukan masu shela

  2. Dattawan za su ba da rahoto ga mai tsara ayyukan rukunin dattawa

  3. Yadda masu tsara ayyukan dattawan ikilisiya da masu kula masu ziyara da wasu ’yan’uwa da kuma ofisoshinmu suke sadawa da juna

    Masu tsara ayyukan rukunin dattawa za su miƙa rahoton ga masu kula masu ziyara da kuma wasu ’yan’uwa da suke da hakkin tuntuɓar ofishin reshe a kowane lokaci

  4. Tanadin abinci da ruwa

    Ana tanadar da abinci da ruwa da wurin kwana da magunguna da kuma ƙarfafawa daga Littafi Mai Tsarki da makamancinsu, kuma ana yin hakan ba tare da ɓata lokaci ba

  5. Ana bincika rahoto game da masu bukatar agaji

    Ofishin reshe zai aika rahoto ga Kwamitin Masu Tsara Ayyuka na Hukumar da Ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah a kan yanayin da ake ciki da kuma abubuwan da ake bukata

  6. Ana ba da kayan agaji

    Kwamitin Agaji yana tsara yadda za a ba da agaji kuma yana taimaka wa ’yan’uwa maza da mata su farfaɗo

  7. Wani jirgin sama

    Kwamitin Masu Tsara Ayyuka zai bincika yanayin kuma idan da bukata, zai ba da izini don masu aikin agaji daga wasu ƙasashe su zo su taimaka

SABUWAR ƘASIDA DON MASU AIKIN AGAJI

Bangon kasidar nan Jehovah’s Witnesses and Disaster Relief

A WATAN Yuni ta 2013, an tanadar da ƙasidar nan, Jehovah’s Witnesses and Disaster Relief. An wallafa ta ne don ma’aikatan gwamnati da ke kula da ayyukan gaggawa a ƙasar Amirka. Wannan ƙasidar ta bayyana wasu ayyukan agaji da muka yi daga shekara ta 1944. Ƙari ga haka, tana ɗauke da taswira da ke nuna yawan wuraren da muka yi aikin agaji a faɗin duniya. Wani dattijo da ke cikin waɗanda suke shirya aikin agaji ya ce: “Mambobin Kwamitocin Agaji suna amfani da wannan ƙasidar wajen sada da manyan ma’aikatan gwamnati a wuraren da bala’i yake yawan aukuwa kuma suna yin hakan da wuri kafin wani bala’i ya auku.” Ya daɗa da cewa: “Yana yi mana sauƙi mu sami izinin shiga wuraren da bala’i ya auku idan waɗannan ma’aikatan gwamnati sun san yadda muke gudanar da ayyukan agaji.”

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba