Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • ypq tambaya ta 5 pp. 15-17
  • Me Zan Yi Idan Aka Zolaye Ni a Makaranta?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Me Zan Yi Idan Aka Zolaye Ni a Makaranta?
  • Amsoshi ga Tambayoyi 10 da Matasa Suke Yi
  • Makamantan Littattafai
  • Me zan yi idan aka yi mini zolaya?
    Tambayoyin Matasa
  • Ta Yaya Za Ka Taimaka Wa Yaronka Idan Ana Cin Zalinsa?
    Taimako don Iyali
  • Ka Dogara ga Jehobah Saꞌad da Ake Cin Zalin Ka
    Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2023
  • Me Zan Yi Idan Ana Cin Zalina ta Intane?
    Tambayoyin Matasa
Amsoshi ga Tambayoyi 10 da Matasa Suke Yi
ypq tambaya ta 5 pp. 15-17
Wani yaro yana zolayar wani a gaban abokan makarantarsu

TAMBAYA TA 5

Me Zan Yi Idan Aka Zolaye Ni a Makaranta?

ABIN DA YA SA HAKAN YAKE DA MUHIMMANCI

Abin da ka yi zai iya sa a daina zolayarka ko kuma a ƙara zolayarka.

MENE NE ZA KA YI?

Ka yi tunanin wannan yanayin: Thomas ba ya son zuwa makaranta kuma. A cikin watanni uku da suka wuce, ya samu kansa a cikin wani irin yanayi in da abokan makarantarsu suka yaɗa jita-jitar ƙarya game da shi. Sai suka soma kiransa da wasu sunaye. A wasu lokatai, wani zai kaɗe littattafan Thomas daga hannunsa kuma su zube amma mutumin zai yi kamar ba da gangan ya yi hakan ba. Ƙari ga haka, wani zai zo daga bayansa ya ture shi, amma idan Thomas ya juya, ba zai ga wanda ya tura shi ba. Jiya abin ya wuce gona da iri sa’ad da Thomas ya sami wani saƙon barazana a kwamfutarsa cewa . . .

Mene ne za ka yi idan ka sami kanka a yanayin da Thomas yake ciki?

KA DAKATA KA YI TUNANI!

Za ka iya yin wani abu! Ka san cewa za ka iya dūkan mai zolayarka ba tare da ka yi amfani da hannunka ba? Ta yaya za ka yi hakan?

  • KA ƘYALE SU. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Wawa yakan furta dukan fushinsa; amma mai-hikima yakan danne shi ya kwaɓe shi.” (Misalai 29:11) Idan ba ka ce musu kome ba, waɗanda suke zolayarka za su daina.

  • KADA KA RAMA. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Kada ku sāka wa kowane mutum mugunta da mugunta.” (Romawa 12:17) Ramuwa za ta sa su ci gaba da zolayarka.

  • KADA KA JEFA KANKA CIKIN MATSALA. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Mutum mai-hankali yakan hangi masifa, ya ɓuya.” (Misalai 22:3) Idan zai yiwu, ka guji mutanen da za su jefa ka cikin matsala da kuma yanayin da zai sa a zolaye ka.

  • KA BA SU AMSAR DA BA SA ZATO. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Mayar da magana da taushi yakan juyar da hasala.” (Misalai 15:1) Kana iya faɗin abin ban dariya. Alal misali, idan mai zolayarka ya ce kana da ƙiba sosai, kana iya cewa, “Kar ka damu, zan rage ƙibar!”

  • KA BAR WURIN. Nora ’yar shekara 19 ta ce: “Idan ka yi shiru, hakan zai nuna cewa ka manyanta kuma ka fi wanda yake zolayarka hikima. Ƙari ga haka, yana nufin cewa kana kame kanka, halin da wanda yake zolayarka bai da shi.”—2 Timotawus 2:24.

  • KA KASANCE DA GABA GAƊI. Masu zolaya sun san waɗanda suke damuwa da abubuwan da suke musu da kuma waɗanda ba za su rama ba. Ƙari ga haka, masu zolaya za su daina yin hakan idan suka ga ba sa sa ka fushi.

  • KA GAYA WA WANI. Wani malamin makaranta a dā ya ce: “Zan shawarci wanda ake zolayarsa ya gaya wa wani. Abin da ya dace ke nan, kuma hakan zai iya hana zolayar.”

Wani saurayi ya fuskanci mai zolayarsa da gaba gadi

Kasancewa da gaba gaɗi zai ba ka ƙarfin zuciyar da mai zolayarka ba shi da shi

Shin Ka Sani?

Ban da dūkan mutum, zolaya ta ƙunshi waɗannan abubuwan:

  • Kalmomi kamar wuta suna fitowa daga bakin mai zolayar wani

    Zagi. Celine ’yar shekara 20 ta ce: “Ba zan taɓa manta da irin sunayen da suke kirana da su ba, da kuma abubuwan da suke gaya mini. Suna sa in ji kamar ni ba kome ba ne, ba wanda yake ƙaunata kuma ban da amfani. Gwamma a yi mini dūka da a zage ni.”

  • Wani matashi yana zaune shi kadai don tsararsa sun guje shi

    Ƙin yin abota da kai. Wata yarinya mai suna Haley ’yar shekara 18 ta ce: “’Yan ajinmu sun guje ni. Kuma a lokacin cin abinci ba sa so in zauna tare da su. Na yi shekara guda ina cin abinci ni kaɗai kuma ina ta kuka.”

  • Wata matashiya ta fice daga kwamfutarta bayan an zolaye ta ta hanyar sakon da aka aika mata a kwamfuta.

    Zolaya ta Intane. Wani yaro mai suna Daniel ɗan shekara 14 ya ce: “Da ɗan ƙaramin batu da aka saka a Intane, za ka iya ɓata sunan mutum ko kuma rayuwarsa. Hakan ba ƙarya ba ne, yana faruwa!”

WASA KWAKWALWA

GASKIYA KO ƘARYA

AMSOSHI

1 An daɗe ana zolayar mutane.

1 Gaskiya. Alal misali, Littafi Mai Tsarki ya ambaci Nephilim, wato mutanen da sunansu yake nufin “Waɗanda Suke Sa Wasu Su Fāɗi.”—Farawa 6:4.

2 Zolaya tsokana ce kawai da ake yi wa mutane.

2 Ƙarya. Zolaya ce ke sa matasa da yawa su kashe kansu.

3 Gwamma ka rama idan kana so a daina zolayarka.

3 Ƙarya. Sau da yawa, yawancin masu yin zolaya sun fi waɗanda suke zolaya ƙarfi, shi ya sa waɗanda ake zolaya ba sa iya ramawa.

4 Idan an zolaye ka, bai kamata ka rama ba.

4 Ƙarya. Idan ka ga ana zolayar wani kuma ka yi shiru, kana iya ɗaukan alhakin abin da ke faruwa maimakon mai magance matsalar.

5 A yawancin lokaci masu yin zolaya ba su da ƙarfi, mugun baki ne kawai gare su.

5 Gaskiya. Ko da yake wasu masu zolaya suna da girman kai, da yawa a cikinsu ba su da wani ƙarfi sai mugun baki, don su nuna sun fi wasu.

6 Masu yin zolaya za su iya dainawa.

6 Gaskiya. Tare da taimako, masu zolaya za su iya dainawa.

ABUBUWAN DA ZAN YI

  • Idan wani ya zolaye ni, abin da zan yi ko abin da zan faɗa shi ne:

ƘARIN BAYANI!

Ka Bugi Azzalumi ba Tare da Damtse Ba

Ka kalli bidiyon zanen allo mai jigo Ka Bugi Azzalumi ba Tare da Damtse Ba a www.pr418.com/ha. (Ka duba ƙarƙashin KOYARWAR LITTAFI MAI TSARKI > MATASA)

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba